39

3.8K 241 3
                                    

Nainah baxata xauna da mijina ba, zaman Nainah a gidana Ya qare idanma arxiki kukeyi mawa kun Sam...... Tayi shiru sakamakon Marin da hajiya Ta dauketa dashi,

"ashe bakida mutunci mufeedah, bakida ragowa Kodan idon mu mahaifan mijinki....., ta fashe da kuka mai tsanani ta ajiye sulaimi qasa ta fice da Sauri tana kuka, Fahad Ya tashi Yabi bayanta,

"oh mufeedah Meyasa kikayi haka Wannan tsakaninki ne da mijinki bai kamata Kibari iyayenku Susan bakya girmamasa ba,

Cikin kuka take mgn
"kagayamin abinda akamin anmin adalci kenan, daga taimako sai Idan dama can an qulla Wannan abinne Dan aci Xarafina, Meyasa sai Nainah yakeso Meyasa yakeson toxartani a gun abokaina yar aikina mijina Ke aure馃槶

"is not bad mufeedah Allah bai haramtaba kuma bana so kibi xugar qawaye kiyi haquri da mijinki da Nainah, ki gode Allah Nainah mai haquri ce bata da fitina...

Taja dogon tsaki ta shiga motar tana fadin
"baxan xauna da ita ba, koni ko Nainah dole xai xabi daya, driverya Jata Fahad yabita da kallo yana tabe bakinsa,
"kin gama haukarki Ki bari Mus'ab baxai bar *haskensa* saboda ke ba kina sonsa haka kike wulaqantashi,

Baffa yayi gyaran murya,
"ynxu na fahimci majeed kuma na gode Allah da har ynxu yana son jinina, halaccin majeed gareni baxan manta inmasa butulciba, Ya dauki Nainah matsayin qanwarsa saboda bahijja har yake kula da ita sannan a yau ina shaida maku na bawa majeed bahijja ita kuma Nainah ta haqura ta xauna dakin mijinta Allah Ya albarkaci aurenku,

Nainah ta riqo baffa
"baffa Meyasa xakamin haka, Kafi kowa sanin xuciyata, ban taba son kowa bayan majeed ba shi Kadai nakeso baffa Dan Allah ka Barni dashi,

Bahijja ta tashi Tana kuka sosai ta fice majeed ma Ya tashi Yabi bayanta,

Inna ta rangada guda
"uba Ya sayarda yar'sa saboda kudi, andaiji Kunya,
Mohd Kaita ya juya yana kallon ta Wannan ko tana haukane, Ya duba agogon hannunsa jirginsa Ya kusa tashi, ya dubi baffa ya masu Godiya ya fice tare da hajiya bayan ta dauki sulaimi,

Baffa ya riqo fuskarta yana kallon ta
Kiyi biyayya Nainah ,ina gayamiki ba son majeed kike ba sabon da kukayi dashine, Ki riqe mijinki kiyi biyayya garesa, Watarana xakiji dadi, ki share min hawaye na ko Dan inna kuma kada Ki qullaci bahijja yayarkice ba laifinta bane,

Tayi shiru tana cigaba da kuka,

Ya Kalli Mus'ab dake kallonsu
'xoka tafi da matarka Allah Ya sanya albarka,

Rauda ta tashi ta dauki trolley din da Nainah ta shigo da ita ta fita, Mus'ab kuwa Ya riqo hannun Nainah suka fice,

Fahad dake tsaye bakin motarsa ya dubi Rauda yana nuna mata Mus'ab da Nainah dake fitowa
"sister kinga perfect match sun dace da junansu,
Rauda ta dubesu kafin ta juya Tana sanya trolley a mota
"sun dace ni kaina yau na fara ganin Nainah amma Naji ina sonta yarinyar akwai kwarjini sosai amma bnsan Meyasa ta tsani brother ba,

"xata so sa kibarta xafin son saurayinta ne, Kinsan mata da aji balle ma mutum irin abokina da matan Skul Ke kururuwa akansa,

Sukayi dariya alokaci  daya dai dai da qarasowarsu, Nainah ta zame hannuwanta daga nasa ta bude motar fuskarta ba Walwala ta shiga,

Mus'ab Ya shiga motar Fahad, ita kuma Rauda suka tafi tare da Nainah,

Sanda suka iso gidan Rauda tayi qoqarin fahimtarda Nainah sosai musamman akan Mus'ab, jinta kawai take amma ita hr a xuciyarta bata sonsa,

Sanda Rauda xata tafi Nainah taje rakiyarta mufeedah ta kamata da duka ta ko ina dai dai lokacin Mus'ab Ke shigowa tare da Fahad, qarasowarsa wurin yayi Daidai da bugawa Nainah kwalbar dake hannunta,
Goshinta kuwa Ya fashe ta saki qara.....numfashinta na dauke Luuuuu tayi ta fadi ragwaf a jikin Mus'ab, manyan idanuwansa akan mufeedah yake rungume da Nainah.

NAINAHWhere stories live. Discover now