45

3.7K 198 0
                                    

Numfashinsa na soma yin sama sama, mutanen dake cikin masallaci suke jin sa a baya sai suka fita suka duba,

'Subhanallah Malam Nasir Buzu ne, meya samesa?
Suka isa da Sauri suna tattaba shi tuni numfashinsa ya dauke馃檳

Haka suka daukesa suka nufi asibiti dashi Dan suna ganin kamar suma ce yayi,

Sanda Yasir ya dawo suka sanardashi a rude yaje asibitin lokacinma har ya Farfado sai dai barci yake sosai.

Godiya sosai Yasir yayiwa mutanen dana kawo baffa asibitin, kana Ya cigaba da safa da marwa hannuwansa goye a bayansa, abubuwa suka cunkude a xuciyarsa,

Yaje gida ya sami wasu mutane daban sun gaya masa gida nasu ne sun siye, Tor Yaushe baffa ya siyarda gidan, Meyasa Ya siyarda gidan kuma a ina yake son su xauna ynxu, sannan ina inna ta shiga bai gantaba?  Duk wadannan tambayoyin babu su a ynxu har sai baffa ya Farfado.

Mufeedah kuwa tun bayan tfyr Mus'ab ta kasa tabuka komai saboda baqin ciki Wannan ma abin kunyane Mus'ab keson janyo mata,
'yar talaka mai aikinta ce mijinta keso haka kamar hauka

Yana so Ya xubar mata da aji ga qawayenta, ynxu indai Nainah ta dawo ba kanta xata fasa ba shaqureta xatayi sai ta mutu sai dai ya saketa, Allah yasa ma tace baxata dawo ba bata sonshi, Amin.

Rauda a Gidan Hajiya ta Xarce Kai tsaye Bayan Ta Rakasu Mus'ab Ta Sameta Ranta a Bace,

'oh Rauda shikenan Mus'ab Ya xabi Nainah akanmu kenan, ya xabi farin cikinta da namu, yafison yabita kenan?  Rauda ta xauna tana sauke numfashi

'Tor ya xamuyi hajiya abinda kake so komai xaka iya fatanmu Allah ya kaishi lfy ya dawo dashi lfy Ni Nainah dince ma Ke bani haushi a ynxu tana wahalarda brother gwani bn tausayi.

Hajiya ta xauna itama tana fadin
'yarinyarce ynxu ta fita raina kwata kwata, duk macen da xata nunawa yarona qiyayya haka bana sonta Ballantana Ma Mus'ab Ya Wuce Ajinta ,yar talakawa ce fa, in banda jaraba ta 膹a namiji inashi ina Nainah, yafita kyau yafita kudi yafita komai sannan akwai wadanda suka fita ai. Rauda ta soma dariya

'sai haquri hajiya amma Nainah ta Karbe Xuciyarsa Baya Ganin Kowa Sai Ita, Sannan Ita Dan Tana Mace Ne Ake Ganin Kamar Tafishi kyau, Sannan Yarinyace sosai hajiya, ynxu fa xataje S. S. 3,

Mtsew hajiya taja dogon tsaki ki kirasa Ki tabbata Mishi
'Duk Idan ya bari yayi Asarar exam dinshi saboda Wannan yarinyar Wlhy xai hadu da fushi na kuma xan gayawa daddy komai sannan Idan ta buqaci saki Ya bata takardarta Ya dawo gida, ni xan ne ma masa mace wadda tafi Nainah bafullatana bama buxuwa ba.

Fauziya(Qanwar Mus'ab )ta kyalkyace da dariya,

'Hajiya sai tafi amaryar sa kyau ko?
Sosai ma auta,
Rauda Tace ai gashinta ne da dimple din nan Ke ruda Mus'ab ba dan haka ba mata kyawawa wane irine bai gani ba.

Hajiya ta tabe bakinta kawai amma ranta yayi matuqar baci sosai musamman ma akan Nainah.

*

Nainah xaune da umma lotee qanwar mamanta, tana kuka take gaya mata komai an kwace mata saurayi an bawa bahijja sannan an aura mata mai mata wanda bata so,

Ran Lotee Ya baci sosai musamman ynda Nainah Ke mata kukan a raba aurensu  ita bata so,

'kayi shiru Nainah kagayamin shi Wancan yaro da aka bawa bahijja kana sonsa ne, (bata iya Hausa sosai ba)

'umma ni bana sonsa ynxu nadaina sonsa Duk bana sonsu karatuna nakeso, ynxu fa S. S.3 xnje,

'Tor shikenan Nainah amma bai kamata Nasir Ya maku haka ba Kodan yaga mahaifiyarku bata Raye xai riqa maku dole ga masu kudi, ya manta kuna da naku dangi ne?

Nainah tayi shiru tana kallonta Ta cigaba da fadin

'tun da bakaso baxaka koma ba dole ya aiko maka takardarki ko kuma yazo Ya baki ni xan kwatar maka yan'cin ki,

Nagode umma Lotee.

Tun da ta kwanta ta kasa samun nutsuwa Idan ta rufe idanuwanta Mus'ab take gani, cutie face dinsa take gani, murmushinsa ,da idanunsa daya Ke tsare ta da kallo dasu, ta tashi xurum tana kallon lotee dake barci, ta tuna Idan yana kallonta Yanda take xare masa ido,
'hey friend why are you looking at me? Ta saki murmushi, ta tuna Idan tana cin abinci yakan xauna yayi ta kallonta, da'a gidane da ynxu suna tare komai tace yayi xai mata komai tasa shi xaiyi yana murna,oh missing you friend, but why na kasa barci sai tunaninka, ta dafe goshinta.
'Oh God, tunanin majeed bai taba hanamin barci ba sai naka? Why? You are just a friend to me, thinking of you will not stop me from leaving you馃槒

Lotee Ta gyara kwanciyarta idanunta na sauka akan Nainah dake xaune, a hankali ta kira sunanta,
Nainah!
Ta juyo tana kallonta batare da ta amsa ba,
'me kake a xaune cikin duhu, me Ya hana maka barci?

'kaina Ke ciwo umma,
Lotee Ta Kunna fitilar dakin tana kallonta,batayi Kama da mai Ciwon kai ba,
'ko kana tunanin mijinkine?  Ta xare ido sosai
'nooo umma why should I?
'ni bajin turanci nake ba kamin Hausa ko yare na,
Nainah ta kwanta tana fadin
'umma bana tunaninsa, amma inajin gabana na faduwa tun daxu ina tsoron wani abu ya sami baffa ko yayi fushi dani bayan nazo.
'Ki kwantarda hankalinka baxai maki komai ba.

Olryt Nyt Umma.
Mtsew ta kashe fitilar cike da takaicin turancin da Nainah keyi,yaran xamani ma akwai rainin wayo馃槨.

Washe gari hakama ta tashi sukuku ta tuna irin Wannan lokacin xai xo Ya tsareta,
'Nainah kinci abinci, me kikeso, me zan sa akawo maki, Xakici tare dani sai tace a'ah, tor kici *haskena*, Idan kin gama ni xanje naci nawa, haka xai tsareta hr sai ta gama kana Ya fita, yau gata tana kalaci da madarar shanu da kekena, Bamai rarrashinta, ko ba komai yana sanyata murmushi da Nishadi,yana da kyau numfashinsa yana da qamshi, ta saki murmushi caraf suka hada ido da Latee,
'kai Wannan yaro munafikin yaro ne, tun daxu ina mgn kana can kana tuna Wancan miji naka kuma kace baka sonsa,yanxu ka xauna kana tunaninsa,

'kai umma bashi nake tunani ba, believe me bana sonsa just thinking about him Kingane.

Tor ka gama shan Wannan kekeni kaxo zan aikeka inda kawun ka.

Kusan azahar Nainah ta dawo dauke da Kaya akanta a gajiye take Duk inda Tabi maza da mata kallonta suke sunga baquwar fuska sunga mai Kama da Yaren su banbanci fatar Nainah tafi kyau da sheqi da Alama Hutu ne da yanayin wurin xama, da haka ta qaraso gidan bakinta a tunxure cike da takaicin kallon da suke mata,

Tana shigo wa gidan taja ta tsaya curus, xuciyarta na buga sakamakon ganin Mus'ab, Majeed da Bahijja xaune tare da Lotee,

Lokaci daya suka Juyo suna kallonta idanunsu suka sarqe dana juna ita da Mus'ab, atare xuciyoyinsu na soma bugawa, tayi Saurin dauke idanuwanta ta daga qafafuwanta da kyar tayi shigewarta daki batare da ta sake kallonsu ko yi masu magana ba.

Afuwan pls xakujini shiru kwana biyu due to sallah, ga ayyukan sallah da sauransu,

NAINAHWhere stories live. Discover now