Page 61

3.3K 287 32
                                    

Hydar na zaune yana lallaba Kausar akan ta taso suje su dawo da Binta amma taki, ba yanda beyi da ita ba ta kiya, wanyanshi ne ya fara ringing ya dauko yaga Ummi ce ke kira ya dauka tareda karawa a kunnenshi ya mata sallama ta amsa sannan tace "in kun samu lokaci kazo kaida Kausar inason ganinku", "toh gamu nan zuwa", ya amsa mata dashi sannan ya kashe wayan ya kalli Kausar yace "toh kinji, Ummi wai muzo", badan taso ba ta tashi ta shirya Nawaf itama ta shirya sannan suka fito. Hydar da kanshi ya jasu a mota ko kadan Kausar bataso zuwa ba dan bataji dadin abinda Binta ta mata ba, ace duk zaman da sukayi akan maganan da be kai ya kawo ba rana daya ta tattara ta tafi ai bata kyauta mata ba.

A compound din gidan Ummi sukayi parking suka fito Hydar ya karbi Nawaf suka karasa ciki, da sallama suka shiga Binta dake kallo a parlor ba karamin bugawa zuciyarta tayi ba jin sallamansu, da kyar ta iya amsawa tareda gaishesu amma Hydar kadai ne ya amsa dan Kausar koh kallon inda Binta take batayi ba, Binta tasan Kausar na fushi da ita amma ya ta iya, batada yanda ta iya, dolece ta sata barin gidan dan bataga zata iya zaman ba bayan antynta na neman ta hadata aure da mijinta.

"Ina Ummi?", Hydar ya katse musu shirun da tambayan Binta, "tana daki", take bashi amsa ya kalleta yace "meyasa kika bar gida ba da izinin mu ba", shiru tayi yace "ke yanzu abinda kikayi kin kyauta kenan", tace "a'a", yace "good, idan zamu koma tareda ke zamu koma, kuma banson makamancin abinda ya faru yau ya sake faruwa", shiru tayi dan ita harga Allah batajin zata iya komawa tinda Kausar taki ta sake mata fuska. Ummi ce ta sauko daga sama tace "ashe kunzo", Hydar yace "eh Ummi", sannan  Kausar ta sauka har kasa ta gaishe da Ummi ta amsa mata fuska a sake tareda daukan Nawaf daketa wasanshi inda yake kwance kan kujera wanda tin dazu Binta keson daukanshi amma ta kasa tashi dan ji take kaman ruwa ya cinye ta.


Zama Ummi tayi tace "Kausar me ya hadaku da Binta?", kan Kausar kasa tace "ba komai", Ummi tayi murmushi tace "tacemin wai kinzo kince mata ta auri Hydar", "anyi haka Ummi", cewar Kausar da har yanzu kanta ke kasa Ummi ta kuma cewa "meyasa?", shiru Kausar tayi na en dakiku sannan tace "saboda a ganina shi zefi kula da ita tinda 'yar uwarshi ce kuma shi ai yana sonta", Ummi murmushin su na manya tayi sannan tace "itama Binta tana sonshi ne", Kausar ta girgiza kai alaman a'a, Ummi ta sake cewa "kuma bakya kishin mijinki ne", shiru tayi dan idan tace bata kishinsa tayi karya amma indai akan Binta ne ai zata iya danne kishinta, "Kausar", Ummi ta kirata, a hankali tace "ina kishinsa", Ummi tayi murmushi tace "toh shikenan magana ta kare, idan basu ne suka sasanta kansu ba karki shiga maganan saboda gaba, kai kuma Hydar bance ka matsawa 'yar mutane ba, ku barta ta zabi wanda takeso, tayi auren soyayya itama kaman yadda kuma kukayi ba tareda wani ya hadaku ba, sannan daga yanzu Binta ta dawo wurina kenan sedai ta dinga zuwa gaishe ku", Kausar batace komai ba Hydar ne yayi karfin halin cewa "Ummi ki bari ta dawo gidanmu, Insha Allah bazamu kara takurata akan abinda bataso ba.


Shiru Ummi tayi sannan ta kalli Kausar, ganin yanayin Kausar yasa Ummi cewa "shikenan, ku tafi da ita amma banson ta kara kawomin korafinku", "Insha Allah", cewar Hydar a yayinda yake murza hannun Kausar dan ko ba'a fada mishi ba yasan ranta a bace yake. Se yamma lis suka bar gidan tin a mota har suka kai gida Kausar bata yarda tawa Binta magana ba, sosai rashin yi mata maganan ke damun Binta amma ya ta iya tinda ita ta jawo, koda suka shiga gida kowa dakinshi yayi. Tana zaune kan gado Anwar ya kirata ta dauka suka gaisa har take bashi lbrn ta dawo gida, ranshi beso ba amma se yayi addu'an Allah yasa hakan shi yafi alkhairi, sosai sukasha hira yake fada mata yama mahaifinshi magana tace "Allah ya tabbatar da alkhairi",


Washegari ya kama Sunday kaman yanda Dad yama Anwar alkawari haka koh akayi, sun shirya shida Uncle Hamza sukaje sukaga Abba kuma alhmdllh Abba ya amince dukda besan Anwar din ba amma tinda ance sun sasanta da Binta toh shima ya amince, sosai su Dad sukaji dadin  karamci irin na Abba, a nan take suka biya sadakin Anwar kaman yadda sukayi na Khaleel, wannan karon ma seda Abba ya rage yace yayi yawa ya karba 50k. Sanda Anwar yaji lbrn ji yayi kaman ya zuba ruwa a kasa yasha dan murna, bayan su Dad sun wuce Abba ya dau waya ya kira Hydar yace yanason ganinsu gabadaya, da toh Hydar ya amsa mishi sannan ya kashe wayan, kallon Kausar dake sawa Nawaf pampers yayi yace "Abba na neman mu, ki fadawa Binta", ya fada yana mikawa dan ya canza kaya, "ka fada mata da kanka ai tana daki", se a lokacin ya tuna ashe har yanzu Kausar batawa Binta magana dan koh data gaishe ta da safe ciki ciki ta amsa mata, girgiza kai yayi a zuciyarshi yace "mata kenan", sannan ya sauka ya fadawa Binta da kanshi sannan ya koma sama.



Koda sukaje gidan anty Maryam tazo ziyara da yaranta tinda weekend ne, seda duk suka gaggaisa sannan suka wuce parlorn Abba inda yake zaune suka zazzauna Abba ya kalli Binta yace "kiramin mamanku", tashi tayi ta fita ba jimawa ta dawo tareda Ummi duk suka zazzauna Abba ya dauko kudin da su Dad suka bayar yace "ga sadakin Binta nan an kawo", ba Hydar ba har Kausar seda taji wani iri amma tayi shiru a yayinda Binta taji dadi ya ziyarce ta dan ko ba'a fada mata ba tasan Anwar ne, Hydar ne yayi karfin halin cewa "waye ya fito", kallonshi Abba yayi yace "wai sunanshi Anwar kanin Khaleel abokin ka, mijin Zeena" shiru Hydar yayi dan yasan waye Anwar da rashin jinshi kap lbrn Anwar ba wanda Khaleel baya fada mishi har zuwanshi India da dawowan shi duka Hydar ya sani amma baya ganin ze iya hana Anwar Binta kodan abokantakan dake tsakanin iyayensu da wanda ke tsakanin shi da Khaleel amma kuma yasan idan yayi hakan toh beyi ma Binta adalci ba tinda kila ita batasan haka halin Anwar din yake ba, 'toh yanzu me abinyi?' ya tambayi kanshi amma ba amsa.

Dagowa yayi ya kalli Abba yace "Abba ita tana sonshi ne", kallonta Abba yayi yace "iyayenshi sunce wai yace musu kun sasanta kanku haka ne, kina sonshi?", cike da jin kunya tace "eh hakane Abba, ina sonshi", runtse ido Khaleel yayi yayinda Abba yace "toh kaji", kada kai yayi yace "Allah yasa hakan shi yafi alkhairi", Ummi da anty Maryam suka amsa da "ameen", banda Kausar da tayi kicin kicin da fuska tana hararan Binta, kafin wani ya sake magana ta kalli Binta tace "Binta fada min gaskiya wannan Anwar din shine wanda kika fadamin tin haduwar mu dake", gaban Binta na faduwa ta kada kai alaman "eh", Kausar tace "toh bazaki aureshi ba", da sauri Binta ta dago tana kallon Kausar tareda cewa "anty", wanda batama san sanda ta kira Kausar din ba, Kausar ta maka mata harara sannan ta juya wurin Abba tace "Abba yaron da ake magananshi beda kamun kai", runtse ido Binta tayi jin ance Anwar beda kamun kai, Kausar taci gaba da cewa "wannan yaron shine wanda ake nema wanda ya dauketa daga gidan Hajiya be mayar da ita ba har ta fada hannunmu", hawaye Binta keyi yayin da parlorn yayi tsit kowa na digesting maganan da Kausar tayi.


Anty Maryam ce ta kalli Binta tace "Binta wannan yaron shine wanda ya daukeki har ya kaiki hospital sanda baki da lfy da dawowan ki kuma abokinshi ya nemi ya bataki amma be samu dama ba kika gudu", kada kai Binta tayi tana kuka dan tasan an kusa a rabata da Anwar dinta, anty Maryam da batada hakuri cikin daga murya tace "ba magana ake miki ba kike dagawa mutane kai kaman wata kadangare", cikin kuka Binta tace "anty shine", ta fada tana saukowa daga kan kujera ta zauna kasa ta dunkule wuri daya tana kuka dan harga Allah batasan inda zatasa ranta ba idan aka rabata da Anwar, shiru Hydar yayi dan besan me zaice ba, shi dama yasan Anwar bejin magana amma be taba tunanin rashin jinshi ya kaishi har gidan karuwai ba, amma kuma ta wani bangaren zuwanshi gidan ya kubutar da Binta tinda d'ace bai je ba da kila yanzu rayuwar Binta ta gama tabarbarewa, shikuma Abba shiru yayi dan beyi tunanin irin yaron da Binta zataso ba kenan tinda tanada kamun kai, amma indai har yayi confirming cewar haka yaron yake toh tabbas baze bari Binta ta aureshi ba, Ummi kuwa shiru tayi dan tama rasa wani irin tunani zatayi ga tausayin Binta nan duk ya kamata saboda kukan da takeyi, anty Maryam dake zaune tana kallon Binta tace "tashi ki bamu wuri shashashar banza kawai, kikasan yaran mutane nawa ya lalata zaki kawo mana shi gidan mu gidan mutunci zakisa sunanmu ya lalace a gari, toh wlh baki isa ba, wawiya kawai, kuma kema se nazo na dubaki na tabbatar ba'a tabaki ba dan ban yarda da yaron nan ba, Allah dai yasa be miki komai ba", da kuka sosai Binta ta tashi ta wuce dakin Zeena tasa makulli ta kulle kanta, Abba ya kalli Hydar yace "kamin bincike akan yaron nan zuwa gobe", Hydar ya amsa da "toh", dukda ya riga ya gama sanin halin Anwar, rashin ji, shaye shaye, zuwa club, rashin bin maganan iyaye ba wanda be sani ba akan Anwar amma baya ganin ze iya kawowa Abba wannan hujjojin amatsayin binciken da yayi dan yasan muddin ya fada to ba Binta ba Anwar har abada, shikuma son da yakema Binta baze barshi ya rabata da abinda takeso ba, tinda tace Anwar takeso ze kira Anwar din suyi magana man to man kodan farin cikin Binta, yayinda Kausar taji wani sanyi a ranta dan tasan idan Binta bata samu Anwar ba dole Hydar zesa kai tinda yana sonta kuma a lokacin tana ganin da wuya Binta taki yarda.

Fans kunji wata sabowa, a ganinku za'a yarda Binta ta auri Anwar dan nikam ina ganin da kaman wuya.

Don't forget to vote, comment & share.

Mzzdaddy💋



'YAR HUTU (LABARIN KAUSAR DA BINTA) EditingWhere stories live. Discover now