Page 60

3.2K 266 18
                                    

Kiran sallah farko Binta ta farka daga bacci, seda tayi wanka sannan tayi alwallah ta fito, hijab tasa har kasa tayi raka'atainul fajr sannan tayi sallah asuba bayan taji kira, kafin wayewan gari ta riga ta gama shiryawa cikin jallabiya tana zaune tana tunanin hanya batama Kausar rashin adalci ba idan ta tafi, tasan matukar Kausar ta gane Binta bata gidan baza taji dadi ba, amma kuma she has no other choice than to leave dan gani take kaman idan ta zauna gidan Kausar zatace dole se ta auri Hydar, wanda ita ko digon sonshi bata taba ji a zuciyarta ba illah soyayyan en uwan taka.


Seven on dot ta dauki jakanta da duk wani abu da tasan zata bukata ta fito, a compound taga David yana ganin ta ya karaso wurinta yace "Hajiya where u wan go", "oga's house", ta fada gabanta na faduwa, David na jin tace oga's house yasan gidan iyayen Hydar take nufi amma se yace "but oga never tell me say u go commot", kallonshi tayi tana tunanin wani irin karya zata mai ta samu ta kubuta, murmushi tayi tana kallonshi tace "I'm going there to spend my weekend", David tantama yakeyi ya kaita ko kar ya kaita dan bayason abinda ze janyo mishi magana wurin oganshi, kallon Binta dake tsaye yayi kawai seya dau trolley dinta yasa a bayan mota sannan ta shiga ya zauna ya jasu.


Tinda David ya fara tafiya Binta tayi shiru tana tunanin maganan Kausar da kuma Anwar dinta, a yanda takeson Anwar bata tunanin zata iya barinshi, koda yaushe tana bin maganar Kausar dan ta dauketa ne kaman uwa amma unfortunately not this time around dan abinda Kausar ke nema a wurinta yafi karfinta. Batasan sun kai gidan ba seda David ya juyo yace mata sun iso sannan ta fito, shiya ja mata trolley dinta har bakin kofa ya kwankwansa sannan ya juya ya wuce, me aikin da aka samowa Ummi tana bude kofa taga Binta tsaye seta matsa mata ta shiga da kayanta ciki sannan ta  kulle kofan tana kallon Binta, juyowa Binta tayi tace "Ummi ta tashi?", "a'a bata tashi ba", ta bata amsa, kada kai kawai Binta tayi sannan taja jakarta zuwa sama dakin da Zeena ta bari, ta ajiye jakarta itama ta kwanta saboda baccin dake idonta, ba dadewa kuwa baccin ya dauketa.

Ummi bata tashi ba se wuraren karfe goma, tana saukowa 'yar aikinta ta fada mata Binta tazo tana sama, sosai Ummi tayi mamakin zuwan Binta kuma da sassafe, zuwa tayi ta leka dakin Zeena ta kuwa ganta tana bacci saboda haka seta kyaleta dan ta huta, se wuraren sha daya Binta ta tashi ta sauko Ummi dake kallon news ta kalli Binta tace "en matan gidan Kausar", murmushi Binta tayi ta zauna kusa da Ummi tace "ina kwana Ummi", "Lfy lau, ykk", "Lfy lau ", Binta ta amsa mata dashi tana jira Ummi ta fara mata tambayoyi kan meyasa tazo da sassafe amma se Ummi ta basar tace "tashi kije kici abinci, gashi chan kan dinning", tashi tayi taje ta cika cikinta sannan ta dawo ta zauna kusa da Ummi, Ummi ta kalleta tace "kin koshi", ta kada kai Ummi tace "toh yanzu fadamin meya baro dake gidanku da sassafe", shiru Binta tayi dan batasan me zatace ba, tace saboda Kausar tace ta Hydar ita kuma bata sonshi, ai Ummi baza taji dadi ba tinda Hydar din ai danta ne, "Binta", Ummi ta sake kiranta ta dago ta kalli Ummi tace "na'am", Ummi tace "hala suna miki abinda bakyaso ne", shiru Binta tayi ta girgiza kai Ummi tace "to menene", cikin sanyin murya tace "anty Kausar ce tace wai in auri ya Hydar, nikuma bazan iya ba shine na bar gidan", shiru Ummi tayi tana tauna maganan da Binta ta fada mata kafin daga baya ta dago ta kalli Binta tace "ita Kausar din da kanta", kada kai Binta tayi Ummi tace "shikenan yi zamanki anan zan musu magana", da haka Ummi ta samu Binta ta warware sukaci gaba da kallon tare.

Kausar ta tashi ta shiga kitchen ta kokarta ta hada breakfast tareda jerawa a dinning sannan ta koma dakinta, koda ta shiga Hydar ya tashi ta karasa ta gaisheshi ya amsa mata yana rungumota jikinshi yace "Mommyn Nawaf kin tashi lfy", tace "lfy lau, kimtsa muje muyi breakfast", murmushi yayi dan sosai yakejin dadin yadda Kausar ke kokarin bashi kulawa yanzu, tashi yayi ya shiga bathroom ita kuma ta dauki Nawaf zuwa dakin da suka ware mishi ta mishi wanka ta shirya shi sannan ta bashi nono, sosai tayi mamakin abinda ya hana Binta zuwa dan kusan kullum tare sukewa Nawaf wanka indai weekend ne haka ma tana zuwa kitchen ta tayata aiki amma yau setaga tsabanin hakan, Nawaf na gama shan nono ta sauka kasa zuwa dakin Binta rike da danta a hannu, kwankwasawa tayi taji shiru saboda haka ta shiga da sallama dan duk a tunaninta bacci Binta keyi, amma koda ta shiga bataga Binta ba, tayi tunanin ko tana bathroom ne saboda haka ta zauna tana jiranta amma tayi ten minutes bataji karan ruwa ba seta tashi taje tana kwankwasa kofan bathroom din amma shiru, bude kofan tayi amma babu kowa a ciki da sauri ta fito ai kuwa sukayi karo da Hydar ya kalleta yace "lfy, meyafaru", ya hargitse tace "Binta bata gidan nan", kallonta yayi yace "ban gane ba", tace "nace maka Binta bata gidan nan", kallon mamaki yawa Kausar yace "toh ina zata?", shiru Kausar tayi tana tunanin Hydar ya kama hanyar waje, yana fita ya fara kwalawa David kira dan shi ke kai Binta duk inda zata, da sauri David ya karaso gabanshi na fadawa saboda irin kiran da Hydar ke mishi, yana zuwa ko amsa gaisuwan da David ke mishi beyi ba yace "ina Binta?", cikin David ne ya duri ruwa baki na rawa yace "oga she dey ur mama house", Hydar ya kalleshi yace "with whose permission", shiru David yayi Hydar yace "you've been suspended from work for a month since u don't know ur job", shiru David yayi dan yasan ran oga ya baci, Hydar cikin gida ya koma sannan ya kalli Kausar dake zaune idonta cike da kwalla ya zauna kusa da ita yace "ki kwantar da hankalinki tana gidan Ummi".

Girgiza kai Kausar tayi hawaye na tsiyaya kan kuncinta tace "ashe yanzu har akwai abinda zesa Binta barina, akwai abinda zesa Binta ta bar gidan nan", lallashin ta Hydar ya shigayi tareda cewa "bari mu gama breakfast se muje mu dawo da ita", girgiza kai Kausar tayi tace "bazani ba, tinda ta zabi ta bar gidan nan shikenan taje, amma koda wasa ni bazanje da sunan naje daukota ba", tana fadin haka ta tashi ta wuce sama ta bar Hydar wurin yana tunanin zuciya irin na Kausar.

Anwar ne zaune kan dinning suna breakfast ya kalli Dad yace "dad akwai abinda nakeso na gayama when u ar free", kallonshi Dad yayi yace "yanzu ma I'm free ina jinka", susa keya yayi yace "Dad dama akwai wata yarinya da nakeso kuje kuma iyayenta magana", kallonshi Dad yayi da kyau sannan yace "ka shirya aure ne?", gyara zama Anwar yayi yace "Dad indai zaka nemamin aurenta a shirye nake", jinjina kai Dad yayi yace "bataka stable job, at the same time zakayi masters, tell me ta yaya zaka rike matar", sosa keya ya sakeyi yace "u don't have to worry about that Dad, zan samu stable job kuma zanyi masters dina dan Allah Dad karkace no", kallonshi Dad yayi da murmushi yace "ai bazance maka no ba tinda sunna zaka raya, 'yar wace gidace?", " 'Yar Alhaji Mahmoud ce, cousin sister din Hydar abokin Khaleel", murmushi Dad yayi yace "kace en gida daya kuka kwaso mana da kai da yayanka", Mom da tin dazun tayi shiru tace "nima shi na gani, ya sunanta?", "Binta", ya bada amsa, Mom tace "Allah ya sanya alkahiri", duk suka amsa da "ameen", sannan Dad yace "gobe Sunday zanje naga mahaifin nata", dadi a wurin Anwar bata misaltuwa, a yanzu burinshi be wuce Abba ya amince ya bashi Binta a matsayin mata ba dan baya ganin ze iya rayuwa idan waninshi ya auri Binta wanda bashi ba.

Kuyi hakuri na rashin jina da bakuyi ba kwana biyu, abubuwa ne sukamin yawa.

Don't forget to vote, comment & share.

Mzzdaddy💋

'YAR HUTU (LABARIN KAUSAR DA BINTA) EditingUnde poveștirile trăiesc. Descoperă acum