👨🏻🎓KAFIN IN ZAMA LAWYER👨🏻🎓 👨🏻🎓 👨🏻🎓👨🏻🎓👨🏻🎓👨🏻🎓👨🏻🎓
Nah
Marubuciyar ZamaniNABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)@House of Novella Association
(H,O,N,A)www.NabilaLady5@gmail.com
Season 40 🖤 45
Haka Rayyana ta wuni acikin dakin Ummanta se kuka takeyi sam takasa fitowa dan bataso Nabila ta tambayeta abinda yake damunta, saboda duk wanda yaganta yasan tasha kuka.
Nabila kuwa ganin bata dawo ba tadauka ko aikenta Ummansu tayi, haka ta kwanta tana me cike da farin ciki, tunanin Anwar kawai takeyi, jitake kamar tajawo dare kawai danta ganshi. Har lokacin islamiyya yayi Rayyana bata fito ba.
Hakan yasa da Nabila tashirya tashiga falon su Rayyana dan taji kota dawo, Ummanta tasamu azaune tana kallo, sallama tayi da kyar ta amsa, gaisheta tayi tace Umma ko kin aiki Rayyana ne?
Banza tayi da ita har seda ta maimata sannan ta kalleta cike da bacin rai tace idan na aiketa se akayi yaya? Nabila cike da mamaki tace bakomai dama makaranta zamuje shine banga tafito ba.
Tashi Umma tayi fuska adaure tace to bakar munafuka, ke yanzu ko kunya bakiji ba, kika iya anshema kanwarki saurayi? To bara kiji nafada maki, daga yau babu inda zaku kara fita keda Rayyana.
Dama shegen bakin jini gareki shiyasa kike like mata kuna fita, ranar badake na aiketa gidan su Anwar ba, amma saboda kinsan akwai namiji agidan shiyasa kika nace seda kika bita, kuma kina zuwa kikasan yanda kikayi kika yaudareshi harya fada tarkonki.
To wlh koma me zefaru se Rayyana ta auri Anwar, domin itace aka fara zaba mashi. Da gudu Nabila ta fita dakin tana kuka, a tsakar gida ta wuce Ummanta tana aiki, duk abinda sukeyi tana jinsu.
Bin Nabila tayi dakin tasameta tana kuka, zama tayi tana bata hakuri, sannan tace kinajina ko Nabila, kada wannan maganar ta tsorata ki, idan har kinason Anwar kada ki kuskura wannan maganar tasaki canza mashi.
Allah ne yahadaku babu wanda ya isa yarabaku, dan haka tashi ki wanke fuskarki kitafi makaranta, kuma bance kicanza ma Rayyana ba, sede idan itace tacanza maki, tashi kije Allah yayi maki albarka.
Tashi Nabila tayi ta wanke fuskarta ta tafi makaranta, koda taje ba komai take fahimta ba har aka tashi. Zarah ce take tambayarta abinda yake damunta.
Sanin basa boyema junansu komai yasa Nabila tafada mata duk abinda yake faruwa, sosai Zarah ta tausaya ma kawarta domin tasanta akwai hakuri. Zarah tace kinaji ko Nabila?
Kada kibari barazanar Umma tasaki hakura da Anwar, daga jin yanda kika bani labarin nasan kina sonshi, kuma shima yana matukar kaunarki, dan haka mucigaba da addu'a, idan har rabonki ne wlh sekin aureshi.
Kada ma kibari yasan akwai matsala,agidanku, sede idan shine ya tambayeki, kuma kada ki boye mashi domin yasan hakan ze faru, kima godema Allah da ba Ummanshi bace tayi mashi wannan zabin.
Nabila tace nagode Zarah, kuma insha Allah zanyi yanda kikace, nima har a raina naji bazan iya hakura da Yaya Anwar ba, so daya kawai mukayi wayar soyayya dashi amma jinake kamar munfi wata atare. Zarah tayi murmushi tace yauwa kawata, haka nakeso, nizan wuce senajiki.
^^^^^^^ ^^^^^^^
A gidansu Anwar kuwa duk yanda Abba yaso yashawo kan Aunty yakasa, lallashi babu irin wanda beyi mata ba, amma sam tasaka rigar rashin mutunci ajikinta.
YOU ARE READING
Kafin in zama lawyer
Fanfictionlabarin wani matashi dayasha gwamarmaya kafin yazama cikekken lawyer. Labari ne daya kunshi cin amana, son zuciya da kuma ha'inci