Part 27 and 28

1K 70 4
                                    

® *Real Pure Moment of Life Writers* *P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035

💫💫💫💫💫💫💫💫💫
           *RAYUWAR SUMAYYAH*          💫💫💫💫💫💫💫💫💫

                        ©
    *SA'EEDA MUSA DAUDA😍*

            *PAGE2⃣7⃣—2⃣8⃣*

                   Tun bayan fitan munir *Sumy* ke ta aikin kuka, ta rasa wani makiyin ta ne da ya tsane ta haka yake son ganin bayan ta ??  Ta yaya hakan ma ta faru, da kyar Mum tayi ta bata baki har ta tsagaita kuka. Daren ranar da kyar barci b'arawo ya sace" Mum da daughter dinta, Munir kam barcin shi yayi har da minshari, dan tsabar zumud'i har mafarki yake yi a kan *Sumy*  har an yi aure yana making love da ita, yana tashi ya tsarkake jikin shi, sanan ya fara gabatar da sallolin shi.

**************************************

                 Washe gari da misalin karfe goma na safe, gaba d'ayan su suka hallara a main parlor, kowa na jiran zuwan doctor. Sai da ya d'auki tsawon minti 40 kafin Allah ya bashi daman isowa gidan, kasan cewar ya tsaya tattara report akan aikin da Mum ta bashi.

           Yana isa yayi parking d'in motar shi, ya d'aga a wayak'ira Mum, tana d'agawa  yayi mata  sallama cikin girmama wa, a mutunce ta amsa mishi. Yace" hajiya gani na iso yanzu ina parking space". tace" haba Aliyu sai kace wani bako, tun ba yanzu ba muke tare da kai amma yanda kasan bako haka kane, please ka shigo muna main parlor i'm eager to hear from you". Yace" kar ki samu damuwa hajiya ganinan shigowa". Maganar shi d yayi dai dai da lokacin da ya fara shigowa cikin gidan.Sai da ya iso wurin su kafin nan ya kashe wayar ya saka a aljihu, cikin girmamawa ya duka har k'asa ya gaishe da hajiya, ta amsa mishi cikin farin cikin dan yana bala'in mutunta ta.

         Suna gama gaisawa ya zauna a d'aya daga cikin kujerun da suke wurin, cikin nitsuwa ya sa hanu ya zaro result d'in gwajin, ya fara yi mata bayani yana cewa" wato a zahirin gaskiya hajiya, binciken da nayi ya nuna min cewa akwai wani magani mai k'arfin gaske da akayi amfani dashi, k'arfin maganin yana iya ja wa mace lalacewar mahaifa, kuma idan mutum yayi amfani da wannan maganin yana iya d'aukan lokuta da dama yana barci ba tare da ya farka ba, idan kuma Allah yayi kwannan mutum zai k'are sai kiga ma bai farfad'o ba".

              Duk uban AC d'in da yake d'akin bai hana zufa k'aryo ma Mum ba, bata tab'a zaton haka daga gare shi ba, bata san lokacin da ta mik'e tsaye ta shak'e shi, ta bashi wasu tagwayen lafiyayun mari guda biyu ba, cikin tsananin bak'in ciki ta nuno shi da hannu tana cewa" wallahi ka ban mamaki Munir, yaushe ka rushe duk wata tarbiyar da na baka ??  Ni nasan nayi iya k'ok'ari dan naga na d'ora ka akan hanya mai kyau, na sani koh yanzu Allah ya d'auke raina, na sauk'e duk wani hakkin ka a kaina,saboda na guje maka fad'awa halaka ne nake yi maka zancen aure kayi biris dani, ashe da abun da kake saka wa a zuciyan ka"??  tana kawo nan ta  fashe da kuka, ta jawo *Sumy* da tun farkon fara maganan doctor, ta kifan kanta a saman cinyan ta, take ta rusa uban kuka mai cin rai, sannan ta d'aura da cewa" ka san a wani irin hali na tsinci yarinyar nan a ciki ?? Kasan sanadiyar barin ta gida ?? me yasa kake k'ok'arin raba ta da mutuncin ta" ??

            Ta dube *Sumy* tace" daughter kiyi hak'uri akan duk wani hukuncin da zan yanke, ina so ki saka a ranki bazan tab'a cutar da ke ba kamar yanda na fad'a miki a baya, ina so a yau d'in nan a d'aura auren ki da Munir saboda gujewa gaba, dan bamu san mai zai faru ba a gaba, ki kasance mai hak'uri zaki ci riba a rayuwar ki, kar kiga ina k'ok'arin had'aku aure ki d'auke ni a matsayin mace mai son kanta". Ta d'an tsaya kad'an, ta sa hanu ta share ma *Sumy* hawayen dake kwaranya a idon ta, sannan ta juyo ta sake juyowa ta dube Munir tace" Idan har kaci amanar yarinyar nan Allah na gani, ba zai bar ka ba wallahi. Muddin ka zalunce ta sai kazo har gabana kana kuka wiwiwiiii a lokacin da ni kaina bazan iya yin komai a kai ba, kuma a lokacin da kake tsananin bukatar kasan cewa da ita. Abu d'aya kawai ya rage maka shine ka bi umurni na. Yin yakan shine kad'ai zai fidda kai daga cikin abubuwan da na fad'a maka, dan haka zab'i ya rage ga mai shiga rijiya".

RAYUWAR SUMAYYAHTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang