🍀💖🍀💖🍀💖🍀💖
*CIKAR BURKINA*
🍀💖🍀💖🍀💖🍀💖
*STORY & WRITING ~ BY*
*MURJA WALIEY* wattpad@MurjaWaliey8186*DEDICATED TO MY MOM❤❤*
*PAGE* 1⃣~5⃣
****Tafiya take cikin damuwa da tashin hankali kuka take babu kakkautawa tana tunanin wane hali rayuta zata shiga yanzu mijinta ya sake ta iyayenta sun koreta gashi batasan danginta ba don tun tashinta basu taba zuwa qasarsu ba yanzu ya zatayi, a hankali taji numfashinta na qoqarin rabuwa da jikinta nan take tajita tafad'i qasa sumammiya a gefen titin da take tafiya,
Alh Albubakar ne acikin motarsa yana driving dawowarsa kenan daga office, driving yake a hankali yayinda sauti qira'ar sudais ke tashi acikin motar yana bibiyarsa, kamar ance yawaiga yana waigawa kuwa yahangota gefen titi a hankali ya furta subuhanalilah nan take yayi parking ya fito gurin ba kowa saboda ba hanyar mutani bace sosai hakan ya bashi damar daukarta yasa mota yayi wata private hospital da'ita,.
yana zuwa suka karbeta direct emergency suka wuce da'ita, bayan wasu some minute doctor Sulaiman yafito yana fitowa Abubakar ya zo yana tambayar sa "yajikinta Doctor" Sulaiman yace masa biyoni office. yayi gaba shima ya bishi.
suna shiga office din yace masa wai doctor meke damunta, doctor yace masa zauna tukun Suna zama yace masa "meyasa bakakula da matarka gata da Sabon ciki kuma damuwa tayi mata yawa har ya haifar mata da hawan jini sosai shi ya jefata wannan halin" Abubakar yace "doctor Insha-Allah za'a kiyaye" doctor yace Allah yasa yace ameen sunka tashi sunka je d'akin, suna shiga suka koyi sa'a ta tafarka tana kwance tanata kuka tana tunanin halin da rayuwarta ta shiga, k'arasawa sukai gurinta doctor ya dubata yayi mata qarin ruwa ya wuce,.
A hankali tamaida kallonta ga Abubakar Wanda shima ita yake kallo a hankali ya furta sannu baiwar Allah bari inje in samomaki abinci yana fadar haka yafita, bayan ya kawo mata tace daidai ruwan sunqare Nurse tazo ta cire mata ta tashi tayi sallah,..
***** *****
Kwananta biyu taji sauqi sosai aka sallameta bayan sunfito daga hospital Abubakar yace mata baiwar Allah inane unguwarku kullum idan nayi miki magana sai dai ki dinga kuka meke damunki ne, a hankali ta share kwallanda ke zubo mata tace da shi nagode da taimakon da kayimin Allah yasaka amma bansan ko ina ba ka 'ajeni koma inane,, juyowa yai ya kalleta yace mata ya sunanki tace masa Sakina to miya fiddake daga gidan mijinki gaki da ciki kuma ina iyayenki bani labarinki ko zan iya taimakamiki
*GUNDARIN LABARI*
Mlm Sani Dan Asalin qasar chadi ne matar shi daya Zainab dakuma y'a daya Sakina mai shekara biyar, sun dawo kebbi da zama sanadiyar bokon haram Allah ya hadasu da Alh Aminu lokacin da sukazo kebbi ya taimakesu ya dauki mlm Sani yadinga masa gadi suna zama gidan hankalin su kwance matsalarsu matar gidan mai suna Hauwa don bata da mutunci kwata kwata batabari su shigo cikin gida,mlm sani yasa yarsa makarantar islamiya dake bayan gidan tana zuwa amma yace Sam bazatayi boko ba suna haka sakina kulum sai girma take kyanta sai qara bayyana yake ga hankali da natsuwa,.
Bayan wani lokaci mai tsawo Sakina tagirma tazama y'ammata, watarana tana zaune bakin gate gurin zaman babanta saiga Alh Aminu yazo shiga gida ya dawo daga masallaci yana bude gete ya ganta zaune yayi murmushi har can cikin ransa yana qaunar yarinyarnan amma yana shakun fitinar matarsa duk lokacinda ya ce zayayi Aure sai ta fitineshi da cewa ita ta zauna da shi alhalin baya haihuwa amma yanzu zai cuceta yayimata kishiya amma ya dau Alwashin Auren Sakina idan har mlm Sani ya Amince,.
lokacin da ya iske mlm Sani da maganar ba qaramin farin ciki sunkayi ba amma inna hakalinta yafi tashi idan ta tuna matar gidan amma ta barma Allah komi mlm Sani ya samu Sakina da maganar hankalinta ya tashi amma baza tayi ma iyayenta musuba hakan yasa ta Ameence, lokacinda Hauwa tasamu labari ba qaramin tashen hankali tayi ba hakan yasa Alh Aminu yaba mlm Sani daya daga cikin gidajensa suka koma magana wasawasa takamkama Hauwa da qawarta Samira sunyi yawo wurin boka harsun gaji kamar kulum qarama Alh Aminu Son Sakina ake..
Muje zuwa
Murja waliey on top💋