🍀💖🍀💖🍀💖🍀💖
*CIKAR BURINA*
🍀💖🍀💖🍀💖🍀💖
*STORY & WRITING ~BY MURJA WALIEY*
Wattpad@Murjawaliey8186*DEDICATED-TO AUFANA*
*EDITING - BY AUFANA*
*I Am sorry reader's daga yau wannan novel ya tashi daga BURINA zuwa CIKAR BURINA saboda akwai novel mai suna BURINA da wata sister ke rubutawa*
*THANKS*
*TAKU MAI QAUNAR KU MURJA WALIEY**PAGE* 1⃣6⃣~2⃣0⃣
*Shin wanene Alhj Aminu.....?*
Alh Umar haifaffen garin kebbi ne yanada matansa biyu Lauratu da Na'ima dakuma yaransu biyu Aminu da Aisha, duk Ya'ya'n Lauratu ne Allah bai ba Na'ima Haihuwa ba hakan na damunta tun tana zuwa Asibiti har tafara zuwa waje Bokaye amma shiru ba don komi ta auri Alh Umar ba sai don dukiyarsa yanzu ga shi bata haihuba,.
Kullum cikin masifa ita da Lauratu don gani take ita ta hanata haihuwa (Wanda hakan babban kuskure ne)
Wata ranar Asabar dasafe Alh Umar ya tashi da matsanan ci ciwon ciki Wanda ya bamakowa tsoro bayan sallar la'asar Rai yayi halinsa, mutuwar ta tab'a lauratu ba kadan ba hakan yayi sanadiyar takamu da ciwon zuciya mai tsanani bayan Ankaita Asibiti da safe itama tace ga garinsu, Abin ya ba Aminu da qanwarsu Tsoro da tashin hankali sunyi kuka kamar ransu zai fita ganin hakan bashine abunyi ba sai suka hak'ura suka barwa Allah Komi,,.
Bayan wasu watani Aminu da Yar uwarsa sun zama abin tausayi don Na'ima bata kula dasu ga wahala da take basu,
Haka Rayuwa tacigaba da tafiya har Aminu ya kammala secondary dinsa Aisha kuma tana js3, bayan an rabamusu gado Aminu ya tafi Lagos gurin kasuwanci har kurkusan shekara daya bai dawoba,,,,,
Aisha kullum cikin wahala take tayi jiran dawowar yayan ta har tagaji abin da ya bata mata rai wai yayan ta ya gudu ya barta cikin wahala,.Watarana taji wahala ta'ishe ta ta kwashi kayanta ta gudu hartayi nisa ta fita unguwarsu tagamu da wani teachernsu mai suna Ahmad coper ne yazo daga Maiduguri, yana ganinta ya yashaidata
"Aisha where are you going at this time" abinda ya furta kenan bayan ta gaidashi, yayi mamaki matuqa domin dare yayi sosai shima zafi yayi yawa gashi ba wuta shiyasa yafito ya sha iska dai dai tana kawo Wa gurin lodge insu,.Kuka kawai tafashe mashi dashi kamin tafada masa dalilinda yafitar da ita daga gida kuma a daidai wannan lokacin, ta bashi tausayi sosai har kwalla saida yayi yakalleta cikin tsintsar tausayi yace mata "Aisha yanzu kiyi haquri kikoma gida bakisan Indi zakiba ga dare kar wani abu ya cutardake amma nayi miki Alqawarin idan naqare service dina saurana 6mounth sai intafi da ke garinmu nasan mamata zata riqeki tamkar ita ta haifeki kinji" wani irin dad'i taji a zuciyarta saboda kobakomai zata fita cikin k'angin wuya,.
Murmushi tai sannan tace "to" har cikin Ranta ta gamsu da shi don bata masan ina zataba,,,,, nan yarakata har layin gidansu kar a zargesu sai yabarta haka tak'arasa, gini tahaura tafad'a gida kuma cikin ikon Allah har tashige d'aki Na'ima batasan ma tayi ba,,
Haka taci gaba da wahalar yau da ban ta gobe daban,.Ahmad na kula da ita tamkar yayanta duk abinda akace asaya shi ke biya komi dai take so shi keyimata har akafara zargin sonta yake,,,
Bayan wata shida Ahmad ya dauketa suka gudu ko ajikin Na'ima b'ata Aisha yan unguwa sunyi tsegumi har sungaji,.
*******
Da zuwansu garinsu Ahmad yayi iyayensa Umma da Abba bayanin Aisha, sun tausayamata sunkuma sama dansu Albarka da har yayi tunanin yazo da ita bai barta tatafiba da ba'asan halin da zata shigaba kilama idan tarasa gurin zuwa sai ta Shiga karuwanci ALLAH Ya kiyaye Amin,.
Umma wato Amina yar Asalin Maiduguri ce sunyi Auren soyayya da Abba wato Alh Ibarahim,yaransu bakwai duk maza Ahmad shine na biyu,.
Allah ya jarabeta da son y'a mace bata samu ba shiyasa take son Aisha har cikin ranta,,,, Aisha tacigaba da karatunta na ALLAH dakuma na boko,.
Alhamdulilah Aisha na jindadin rayuwarta a haka har takammala karatunta bayan ta gama Ahmad yace yana sonta Umma taji dadi sosai amma tace sai ta shiga makaranta haka ko akayi badon Ahmad yaso ba, Abba ma yaji dad'i sosai,.
Bayan tashiga makaranta a Federal University inda take karantar medicine, akayi bikin Aurensu da Ahmad.
Muje zuwa
Murja waliey on top.