🍀💖🍀💖🍀💖🍀💖
*CIKAR BURINA*🍀💖🍀💖🍀💖🍀💖
*STORY & WRITING~BY MURJA WALIEY*
Wattpad@Murjawaliey8186*DEDICATED-TO AUFANA*
_*Aminiyata AUFANA Barka da qare littafinki mai cike da tsintsar fad'akarwa wa'azantarwa dakuma Nishadantarwa wato GANI GA WANE....lapia Allah Ya qara basira hazaka kaifin tinani dakuma zazzaqan hannu Ameen, saikuma mun sake jinki a sabon littafinki.*_
*EDITED - BY AUFANA*
*PAGE* 1⃣1⃣~1⃣5⃣
Nan da nan takira Sangami, "Hello Sangami zo gidana yanzu" to yayi Hajiya,, ba'afi 30mint ba yazo,,,..
"Sangami wani aiki muke son kayi muna nasan zaka iya kud'i ko nawane zamu baka indai ba'a samu matsalaba"
Hajiya kinsan indai da cash komi zamu iya kar kidamu fadi me zamuyi maki,,, nan tafada mai abinda suke so, yayi murmshi "Hajiya wannana ai qaramin abune indai da naira, "karka damu buqata dai tabiya" nan suka yanke yanda zasuyi abin cikin sauqi dukansu suka yarda da shawara Hajiya Hafsat suka wuce,.
Dare nayi dama Hauwa ke da girki bayan ta kammala tace "ke larai jeki daukomin phone dina parlor" tana fita ta bud'e abincin Sakina tazuba maganin barci mai nauyi acikin miya da yake gari ne baza'a gane ba dai dai larai ta dawo ta bata phone din ta,.
Tad'auki abincin Sakina ta kaimata dakinta da yake bata jindad'i ba fito Wa take ba,dama yunwa takeji shiyasa da kawo abincin taci, tana qarewa ta hau gado sai bacci ko Addu'a bata samu yi ba bale rufe d'aki hakan ya ba Sangami damar shiga dakin yacire kayansa ya kwanta bayanta,.
Hauwa na baccinta na qaryar ta tashi tana Salati, Alhj yacce lafiya Hauwa meke damunki,tace "Alhj nayi mumunan mafarkine akan Sakina" yace mafarkine ai yi Addu'a ki kwanta ko,ta ce "Aa Alhj muje karakani indubo ta hankali na yafi kwanciyar" yace to Mike,,...
Suna zuwa Alhj ya bud'e d'akin sukayi Sa'a bude yake Subuhanallah Alhj ya furta lokacinda yaga Sangami ya tashi da sauri yana qoqarin jawo kayansa ita kuma Sakina bata Masan meke faruwa ba, Hauwa sai buga Salati take tana cewa "kagani Alhj shiyasa nake cema wanna cikin banaka bane bakayardaba to ga shinan" Alhj ya hassala ya zabgawa Sakina mari ta farka a gigice nan ya damko sangami yadinga jibgar Sa
Sakina da batasan mekefaruwaba kanta ya daure
Alhj yace ma Hauwa "muje yau sai nayi maganin su" yaja qofa ya rufe ta waje,.Sakina kuka tadingayi sosai saboda rashin fahimtar abundake faruwa batasan mekefaruwa ba tace ma Sangami,.
"Mlm lafiya me yakawoka dakina" yayi dariya yace mata ni kwartone Kuma mijinki ya ganmu tare yanzu ki shirya fita da safe hhhhhhh yayi dariya,,,,,
Sakina ta rasa yazatai ta wanke kanta Hasbinnallahu Wani'imalwakin take furtawa,,..Safiya na wayewa Alhj ya kira Mlm Sani da Inna duk mamaki ya kamasu meke faruwa tunda safe Alh kene mansu haka suka bishi gidan, da zuwansu dakin Sakina suka nufa Alhj ya bud'e d'akin yace ga abinda yar Ku ke aikatawa Ku gani da idonku suna shiga mutuwar tsaye sukayi ganin Sangami bako kaya Sakina na gefen gado tana Rusa kuka,tana jinsu tataso tana cewa wallahi inna sharrine bansan shiba Ku tambaye shi kamin suyi magana Sangami ya buge Mlm Sani dake bakin kofa ya kasa ko motsi ya guduu Alh yabishi ina haryakai ya buge mai gadi ya wuce,.
Alh ya dawo zuciyar shi nayi masa suya ya ce Sakina kin cuceni kin cuci kanki kije Nasakeki saki biyu, mlm Sani ya wanketa da mari yace Sakina bani bake kije duniya ta isheki Sakina ta rude tarike Inna, inna kuka yaci qarfinta Don har ga ALLAH bata yarda ba tasan yarta bazata taba aikata zina ba amma ya zatayi abinda kowa ya gani da idonsane Mlm yaba Alh Hakuri ya wuce yana Allah waddai da halin Sakina,..
Sakina tarasa ya zatayi Abinka da Uwa Inna tajata suka fita
Da zuwan su Mlm Sani yace "dakata Zainabu Wallahi karki kuskura Shigo min gida da ita kokuma ki bita kubi duniya bani ba ita"
Innah kuka Sakina kuka
Haka tanaji tana gani yarta kwayad'aya tak ta tafi
Batasan ina zataba, kawai ta mike tasha da zuwanta batasan garinda zataba taji ana kano,kano ta fada ALLAH yasa kudin da ke hanun ta suna kaita kano
Suna isa kowa yakama gabansa ga shi sunyi dare,batasan ina zataba kawai tafiya take ga dare nayi ta samu wata bishiya da benci qar-qa shinta ta kwanta bacci barawo yayi gaba da ita, sai safe ta farka ga gajiya ga wunwa Sundameta haka taje gurin mai waina tace tayimata wanke wanke ta bata masa sannan ta samu abinda taci.wannan ke nan.
Muje zuwa
Murja waliey on top.