CIKAR BURINA

88 3 0
                                    

🍀💖🍀💖🍀💖🍀💖

              *CIKAR BURINA*

🍀💖🍀💖🍀💖🍀💖

*STORY & WRITING ~ BY*
*MURJA WALIEY* wattpad@MurjaWaliey8186

*DEDICATED TO  MY MOM❤❤*

*EDITED - BY AUFANA*

*PAGE* 6⃣~🔟

****Yau saura sati d'aya a dauma Auren Alh Aminu da Sakina hankalin Hauwa yayi matuk'ar tashi tayi masifa har tagaji ga kud'in ta na tafiya abanza tayi zaune sai tunani take wai mi Alh Aminu ya gani ga Sakina gamata nan zube har Wa,enda sunka fita amma ya mak'ale mata qaramar yarinya sai yanzu take datasani da talalata mahaifarta don yanzu tasan idan Alh yayi Aure Asirinta zai tonu kuma Alhj ya saketa bata tashi da komiba kai dasake dole ta dauki mataki,

Yanzu ya zatayi ta zari   hijab dinta bata tsaya ko inaba sai gidan qawarta Haj Hafsat,,
Nocking tayi tana jiran A bude mata Haj Hafsat tana bud'e gida taga aminiyarta da murmushinta tace sannu da zuwa qawa "hmmm sannu dai bari Hafsat na shiga uku asirina na son tonuwa bansan ya zanyiba"  to shigo mana, suna shiga ta fayyacema Hafsat komi tun daga farko har qarshen abinda tayi, Hafsat ta nisa tace Hauwa kin tafka babban kuskure Amma idan sunsan wata basu San wataba yanzu muje gurin boka na bakin tudu,,,

'to qawata shiyassa nake sonki kwanaki nunje da Laure bangane komi ba,'

"karki damu kedai muje kawai"

Alh Aminu zaune suna tattaunawa da Mlm Sani game da Auren, "Alh ni gaskiya bansan da wane baki zanyima godiya ba munzo garinga ba musan kowa ba ka taimaka min da gurin zama yanzu kuma kace kai zakayi kayan d'aki gaskiya Alh sai dai muce Allah Sakama da Aljanna"

Alh yace babu komi ga kudin sadaki da lefe aba Sakina,Mlm Sani ya karba harda hawaye saboda farin ciki  baisan me zaiyima Alhj ba ya biyashi sai dai Addu'a Allah ya saka shi Aljanna ya biya masa buqatocinsa,,,..

Yau ce Ranar daumin Auren Alhj Aminu da Sakina, dayake basuda wasu dangi Auren baiyi wani taroba Abokan Alh Aminu ne kawai sai makota, Amaryarma walima kawai tayi tareda qawayenta na islamiya, dare nayi Alh Aminu da kaine yazo daukar Amarya, Tayi kuka saboda sanin halin matarsa Inna da Mlm sunyi mata nasiha da haquri da biyayya suma sunyi kuka saboda rabuwa da yarsu kwaya daya haka suka rakata har mota Alhj Aminu yayi musu sallama suka wuce,..

Da zuwa parlor suka fara isa yace mata zauna Sakina kamin inkira yayarki tace to yawuce yana jin son matarsa har cikin ransa,.

Assalamu Alaikum uwargida sarautar gida tayi kamar bata jinsa yayi murmushi yace zo muje parlor muyi magana, "babu inda Zanje" tayi kwanciyarta, haka yayi har yagaji yatafi abunsa badan yaso hakan ba

Parlor ya sameta tana wasa da yatsanta yace Amarya muje ciki ya riqo hannun ta suka wuce gabanta sai faduwa yake Alh ko Ya qagara su shiga dakin, bayan sunyi sallah yayi musu Addu'a ya qare ya ciyar da ita abinci daganan zance ya canza....

Da safe ya samata ruwan zafi ya gasata da yake bata wani wahalaba,
Hauwa hankalin ta yayi matuqar tashi ina Zatasa kanta idan asirinta ya Tonu ita kam ta boni kai bazai ma yuwuba da sake shin yanzu ya zatayi gashi ta gaji da zuwa gurin bokaye daban daban amma ba biyan bukata kai yanzu ya zatayi a haka tayita tunani har tagaji,

Yau watan Sakina Bakwai da Auren ta tashi da ciwon Mara mai tsanani hakan yasa Alh Aminu rudewa ya dauketa zuwa hospital, da zuwan su Aka karbeta bayan wasu mintoci ankayi mata test aka gano tana da ciki wata biyar, Alh Aminu yayi mamaki matuqa domin doctor ya tabbatar masa baya haihuwa to yanzu ya akayi haka kai wanna al'amari Nada rikatarwa, A haka yayita tunani har suka dawo gida, gurin Sakina murna takeyi amma taga Alhj sab'anin hakan shi baya farincikin abin ya d'aure mata kai mutum ya shekara dayawa bai haihu ba yau Allah ya bashi amma baya farin ciki,,..

Lokacin da Hauwa tasamu labari hankalinta ba qaaramin tashi yayiba  nan take tayi gidan Hafsat dazuwan ta Hafsat tace mata "lafiya qawata naganki haka kamar wadda akakoro"

'Bari Hafsat na shiga uku asirina na dab da tunuwa"

Me yafaru...?

"cikine da Sakina"

Hafsat tace to minene abin damuwa Ai insunsan wata basu San wata ba yanzu kinsamu damar fita da ita, "tayaya Hafsat bayan kinsan asirina tonuwa zaiyi"

haba kwantar da hankalinki komi yazo da sauqi yanzu bari inkira sangami shi zaiyimuna aiki...

Muje zuwa

Murja waliey on top.

*CIKAR BURINA*Where stories live. Discover now