NA TAFKA KUSKURE

1.3K 48 20
                                    

    NA  TAFKA KUSKURE

          NA

     Janaf ce✍

DEDICATED TO MY MOMMA HAJJA HADIZA MUH'D BA'ARE

©INTERLLIGENT WRITERS ASSOCIATION

_*Bazan taba mantawa dakuba yan"uwana abun alfaharina akoda yaushe sonka kara kwaranya ake araina..Kudin na dabam ne
Bari na fara takaina*_
_Jamila umar_

_Asma'u m yusuf_
_Nafisa yusuf_
_Aishatu m yusuf_
_Fatima umar_

_*JANAF...*_ U GUZYS KUSANI INA MUKU SON KAUNA MAI INGANCHI..

_Walle Nafi da Fati kudaina labe wallahi bbu kyau ato😜

*36*

Shirye shirye takowani bangare ya kamkama Tahir dayaci lbrin komai shima kansa yayi mamaki ammh kuma mamakinsa ya gushe domin tare suka koma kt shida Safwan jin shirye shiryen da take gudanarwa abun mamaki Sakina tace bata dawani shiri itakanta walima ce kuma sunyi mgana da Safeena ranar asabar za"a shirya ma'ana bayan ta taren.

Ranar jumma"a Daddy shi yazo kaduna bayan sallar jumma'a amasallachin sultan bello aka maida aurensu akan sadaki dubu talati,kuma ana gama daura auran Tahir ya wuce yaje ya taho da',ita domin daddy yace kada wacce taje Anty salma dama bata samu zuwa ba Anty lailace tazo itama kuma Daddy yace gobe takoma gidanta,Anty mariyace kadai tarakata bayan tarin masihohin data sha gakuma gyaran da Antyn nata ta zage ta Mata.

itakanta Anty mariyan bata jima ba ta musu sallama Daddy ya zo suka wuce...Suka barta nan shashen momma ita dasu Safeena da Adil wanda ke yaketa tsalle Sakina tadawo gidansu bbu wani gyaran da Safwan yayi ma gidan ba sakamakon yana chan yana kera musu wani gidan a Malali Gra katon gidane sama da kasa shima din bangare biyu yayi musu ammh shi wannan din wlh duniyace ko su hajiya basusan da gidan ba Shida Tahir ne kadai suka Sani.

Sakina Da Safeena sai da Dr Safwan yadawo su hajiya suka tarasu suka musu Nasiha kan su hada kansu su zauna lpy,sai wajen 9 na dare suka Nufi shashensu achan din ma dumguma sukayi dakin Sakina suna hira Safwan duk sanda ya kalli Safeena ransa kara fari yake domin komai yake faruwa ayu wlh itace sillar daidaituwan komai...sai da taga Dare yayi kana ta musu sallama Safwan yadaukan mata Adil dayayi barci yarakata daki wanda Sakina tace ta yafe yaje gun Safeena ya kwana tunda ita tana da lalura...Kin yarda Safeena tayi shiyasa yana kwantar da Adil  tashige bayi tana fadin"Unku mu kwana lpy...girgiza kai kawai yayi yawuce saboda yasan da gangan tashige bayin don karya mata wani mgana ne.

dakinsa ya koma yayi wanka ya sanya jallabiya yafeshe jikinsa da body spry masu kamshi kan ya nufi dakin Sakina da Sallama ya shiga ta amsa ta ninke darduma kallonta yayi kan yace"Me kikayi...Tace"sallar issha'i...Yace'ok...Koma muyi sallah don yau ta dabam ce you know...Mirmishi tamai kawai yajagorancesu sukayi Ra'ka"a hudu yadade yana musu addu'a kafin su kammallah yasan Sakina nada rauni a addini dat why yai mata alkwarin koyar da ita Insha Allahu.

Tabbas Daren na Alkhairi ne domin Safwan da Sakina sun darji juna iya son ransu an famshe watannin da'aka diba ba'a tare...Tun asuba sakina bata koma ba tahau gyaran gida tana kammallawa takoma kichen doya ta soya musu da kwai sai ruwan tea domin dai girkin ba wani iyawa tayi ba wannan ba don komawarta ne take gani gun Anty mariya yasa ma ta iya wasu Abun.

Hakika zamansu yana gudana cikin kwanciyar hankali da zaman lpy duk da Sakina na iya bakin kokarinta yanzu ammh duk da hakan tasani kuma tana gani safeena tanada wani mtsayi agidan wanda daga Safwan har su momma girmamata sukeyi...Tasani ita tabar damanta har wata ta kwace sai dai kawai tayi yar hawayenta ta share,kwana uku yabar dakinta bisa na al'ada yakoma suna kwana daya akowani daki.

Bai bafamusu mganar sabon gida ba saida ya bari weekend kana yace kowa ya shirya za'a fita hardasu momma mota biyu sukayi safwan na tuka su momma da hajiya sai Tahir ya tukasu Safeena basu gama mamaki ba sai da suka gansu a wani makeken gida upstair kamar ba'a kasar turai ba kai tsayawa bada lbrin wannan gidama kauyancine sai dayagama zagayawa dasu ko'ina na gidan yaji alatun kayan more rayuwa gida dai wallahi ko akasar turai.

Sai da suka koma gida ya tarasu yafada musu cewa achan zasu koma dukkansu bayan haihuwar Safeena kwarai da gaske sunyi murna ammh sai Hajiya mama tace"Hakika naji dadi safiyanu kuma muna maka murna ammh zahirin gaskiya nida Hadiza bazamu biku ba domin me muke nema arayuwa komai kagama yimashi sai muyi ta maka addu"a da fatan dacewa muna nan gidan ya ishemu jin dadin rayuwa ko yi komawarku chan kai da matanka Allah in kunsamu lokaci kwa leko agaisa"Babu yadda sukayi iya domin Hajiya mama da ce wlh baza koma chan ba dole aka barshi ahakan.

yau Sakina keda sati uku da tarewa misalin karfe goma da wani abu na dare barowansu kenan itada Safwan daga dakin Safeena safwan yana bayi itakuma tafito falo daukan wayanta sai kawai taji nishi kuma daga dakin Safeena abun ke fitowa ai da gudu ta shiga dakin ta isketa durkushe tana nishi gashi wani ruwa na biyota ai A sitti takoma daki tana kwalama Safwan kira fitowarsa kenan daga wanka da sauri yazira jallabiya suka rankaya Suna zuwa kofar dakin sukaji kukan jariri ai da gudu suna bugan kafadar juna suka antaya dakin shigansu yayi dai dai da sawo kan dawani jinjirin yayi da sauri Safwan yasa hannu ya jawoshi Safeena takoma ta kwanta tana maida Numfashi cikin farin ciki Sakina tadauki dayan tana fadin"Alhamdulillah Ala kulli Halin Safwan yan biyu ne Safeena ta haifa shima bakinshi yaki rufuwa Safeena kawai yake jerawa sannu harda hawaye da jinin da komai yahada da yayan ya rumgume yana zubamata godiya sakina sai da tayi kwallah tana tuna da itana yamzu Safwan zai ma wannan rawan jikin.

cikin lokaci kankani suka gyara komai Safwan ya yankema yara cibi itakuma Sakina tagyara wurin safwan dakanshi yadauki Safeena sai toilet yahadamata ruwan wanka yahau gasata yabarta ciki saboda taji dadin jikinta,komawa yayi shida Sakina suka zage suka wanke yara tas suka sanya musu kaya suka jerasu kan gado suna kallo,safeena na fitowa suna rigen rigen mata Sannu sakina tahadomata shayi mai kwauri tasha ...Kai in takaice muku nan suka kwana suna dawainiya da Safeena sai da Safe da Safwan yadawo sallar asuba yashiga yake fadama su momma safeena ta haihu cikin farinciki suka dumguma kan kace kwabo haihuwar Safeena tazagaya dangi shida kanshi suka tafi asibiti yaduba da ita da yaran ya tabbatar da komai normal kana suka dawo,mutane sai zuwa barka suke da ganin yara masu kama da ubansu akuma haihuwarne hajiya kari da Anty mariya suka zo harda kwamishina da kayan arziki iri Sunkoma washegari sai ga Anty laila itama harda amaryan da'a mata sunzo barka suna da abun arzikinsu hakika safwan da su hajiya sunji dadi sunkuma yarda yanzu za'ayi zumunchi mai tsafta sakina kuwa Allah kadai zai biyata domin tadaukema su momma hidima ita ke komai na gidan ga dawainiyar mai jagejage Safeena tayi alkwari yadda Sakina take kokarin farantamata ita sai ta faranta mata shikanshi Safwan tun bai sakin jiki da ita har yafara domin alkhairan Sakina yadakushe sharrinta na baya,shikuwa Adil kuka yake dayaga Safeena da dauki yaran sai yahau kuka wai a ijiyesu adaukesa sai Safeena ta mika sakina su tajawoshi ta rumgume tace ya'yanta gaka ma nabata abunta akai kadaine dana ko"sai yahau murna yace"Mami ai ya'yan Ummi ne ko ta gyadamai kai shikuma yana dariya.

Sai ana gobe suna suka samu damar komawa sabon gidansu tareda rakiyar yan"uwa da abokan arziki ciki harda Aisha kawar Safeena da inna husai harda maman Aisha da matan kawu isuhu momma da hajiya sun rakasu suma komai yaji baanda tsiya kowa yaga gidan sai dai kaji ya furta masha Allahu dare nayi su momma suka koma gida su koma akabarsu nan da masu shagalin suna.

Su suka zauna akasa mai dauke da falo guda biyu da manyan dakuna guda hudu kowanne yana dauke da falo da toilet sakina ta dau daya safeena ta dau dayan sauran biyun kuma daya aka barma baki dayan kuma ba'a budesa ba.

Commet
And
Share

*Janaf*✍

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 05, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

NA TAFKA KUSKURE!Where stories live. Discover now