Kundun Marubuciya

467 28 4
                                    

KUNDIN MARUBUTA!  KUNDIN MARUBUTA!

    💃🏻INA MASU SON JIN TARIHIN SHARARRIYAR MARUBUCIYAR NAN TA ZAMANI WATO NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) ??  KU FITO YAU KUNDIN MARUBUTA YA TATTAUNA FIRA DA ITA. DA YANDA FIRAR TA KASANCE.

[12/4, 9:09 PM] Writer Ashnam: Assalama alaikum barkanmu da sake saduwa acikin shirin Kundin marubuta Wanda ni Dr Ashsham zan gabatar ina ma bakuwarmu ta mako barka da zuwa.

[12/4, 9:10 PM] Nabila Lady: Wslm,  yauwa barka da dare nagode

[12/4, 9:11 PM] Writer Ashnam: Da farko zamu so muji sunan marubuciyarta mu ta yau?

[12/4, 9:12 PM] Nabila Lady: Sunana : Nabila Rabi'u Zango (Marubuciyar Zamani,  Nabeelert Lady)

[12/4, 9:13 PM] Writer Ashnam: Masha Allah Nabilat

[12/4, 9:14 PM] Writer Ashnam: Wane gari kike ?

[12/4, 9:15 PM] Nabila Lady: Katsina state,  ina zaune a Zangon daura.

[12/4, 9:15 PM] ‪+234 706 876 0636‬: Shin ko Jarumar mu zata iya fada mana tana da Aure ne ko kuwa har yanxu dai ana kan yin boko? ☺☺

[12/4, 9:16 PM] Nabila Lady: Bani da aure a yanzu kam.

[12/4, 9:17 PM] Writer Ashnam: Wane mataki gare ki akaratun boko? Kuma kina aikin gwamnati?

[12/4, 9:20 PM] Nabila Lady: Ina a matakin N. C. E,  kuma ina koyarwa a makarantar gwamnati.

[12/4, 9:21 PM] Writer Ashnam: Toh Allah ya bada sa'a.

[12/4, 9:21 PM] Nabila Lady: Amin,  nagode.

[12/4, 9:22 PM] Writer Ashnam: Zamu so muji litattafai nawa kika rubuta ?

[12/4, 9:25 PM] Nabila Lady: Yanzu haka na rubuta litattafai cikakku guda goma sha biyu, amma sha d'aya ne a kasa,  saboda littafina na farko ya b'ace dan na dad'e da rubutashi. Wad'an da na rubuta akwai
FADEEL &FADEELAT....  AGOLA....  SHATU 'DIYAR MAHARBI.... A MAKABARTA AKA HAIFENI.... RAYUWAR MATA AYAU.... KAFIN IN ZAMA LAWYER.... DARAJAR MUHALLI.... KOWA YA TAKA DOKAR ALLAH..... 'YA'YAN MU AMANAR MU..... A WANI GIDA..... ALMAJIRAI MA 'YA'YA NE.... MATASAN MU..... A WATA MAKARANTA.

[12/4, 9:26 PM] Writer Ashnam: Toh wane kika fi so acikinsu ?

[12/4, 9:26 PM] Nabila Lady: A gaskiya duk cikin litattafai na nafi son KOWA YA TAKA DOKAR ALLAH da MATASAN MU.

[12/4, 9:27 PM] Writer Ashnam: Meye dalilin da yasa kika fi sonsu ?

[12/4, 9:28 PM] Nabila Lady: Dalilin da yasa nafi son su saboda sune littattafan da suka fi tab'a zuciyata a lokacin da nake rubutasu.  Akwai wajen da ina rubutawa kawai naji hawaye suna zubar mani.

[12/4, 9:29 PM] Writer Ashnam: Toh masha Allah , Allah ya kara basira.

[12/4, 9:30 PM] Nabila Lady: Amin,  nagode.

[12/4, 9:30 PM] Writer Ashnam: Mai yaja ra'ayinki kika fara rubutu ?

[12/4, 9:31 PM] Nabila Lady: Abinda yaja ra'ayi na har na fara rubutu shine,   akwai wani littafi dana karanta shekaru ukku da suka wuce,  bazan iya tuna sunanshi ba,  akwai abinda aka rubuta a cikin littafin wanda ba haka ya kamata ace anyi ba,  to bayan dana gama karantashi sai na zauna ina tunanin da haka akayi zaifi bada amana.   Da wannan tunanin ne nace bara nima na gwada ko zan iya rubutu,  sai kawai na fara rubuta FADEEL & FADEELAT.

[12/4, 9:33 PM] Writer Ashnam: Shin kin tab'a fuskanta wani cin fuska  ko kalubale tunda kika fara rubutu ?

[12/4, 9:34 PM] Nabila Lady: A gaskiya ban tab'a fuskantar kalubale ba a harkar rubutu,  kuma babu wani cin fuska dana tab'a fuskanta,  tsakanina da masoyana sai godiya,  idan ma wani kuskure na aikata ana samun masu bina ta private suyi mani gyara cikin hikima,  tunda na fara rubutu ban tab'a ganin wata ko wani yayi zagi akaina ba sai dai idan anyi ban gani ba.

KUNDUN MARUBUCIYAWhere stories live. Discover now