21-30

74 4 5
                                    

♥♥♥♥♥♥
       ♥♥
    *SANADIN       FACEBOOK* ♥♥♥
              ♥♥♥♥
                      ♥
    

~* Visit to Like my Page-https://www.facebook.com/Mshelias-hausa-novels-607015543050170/?referrer=whatsapp*~

~*Take a second & vote me in wattpad if u like the story and don't forget your comments are really appericiated*~

~*☑wattpad @fareedat husain msheli*~
  

*Dedicated 2 zulkifil ibrahim mshelia*

~*ina taya daukacin al'ummar zama na amana 2 jaje akan halin da group din mu ya shiga ciki,muna roqon Allah akan Allah ya dawo mana da group dinmu cikin izza da daukaka Ameen*~

   *Story & written*
                 By
        Fareedat husain mashelia.

🅿21

A ranar ya zayyana mata ciwon daya Dade yana damun zuciyar shi na soyayyarta amma sai maganganun shi suka bata dariya Dan ita har ga Allah wasa ta dauke su cikin zolaya tace haba belovy ni zaka maida Jerry fisabilillahi?

A'a tom tom na maidaki ba jerry ba ya furta hakan cikin jin haushi,Yaya inayi maka maganan abinda ke damun zuciyata kina kawo wasa aciki?
Rausayar dakai tayi tamkar yana ganinta tashiga bashi hakuri dan ta tabbatar da saqo ne daya ke FIta daga qarqashin zuciyar shi zuwa gareta batayi la'akari da da nauyin da Allah ya daura mata ba na igiyoyin aure har 3 dake kanta.
su,,

Nan da nan suka fara soyayya na haqiqa mai wuyar fassara sunajin son junan su a can cikin jinin jikin su

Gangan jikin su na musayar saqonni dake maqale acikin zuciyar su Wanda koda ciwo daya yakeyi toh dayanma saiya amsa kuma saiyaji ajikin shi,

Afreen wacce damuwa ya zamto mata ruwan Shanta Dana wankanta haka ya kasance suna raba dukkannin damuwar su,

Ta bangaren cikin da ke jikinta kuwa yana nan yana ta qara girman shi dan daf take da haifar shi duk da babu wani shiri Wanda mahaifin shi yakeyi domin tarban shi amma Allah yasa yana motsawar shi cikin qoshin lafiya cikin ikon Allah da iradar shi.

Tana cikin watan da zata haife shi Allah yasa qanwar ta tayi mata kyautar wayar dake hannunta bayan maheqin zuciyarta ya canza mata wata ita kuma aka bata kyautar itel 1556plus,

Tana rainon kyakykyawan yarta a gefe guda kuma tana zankada soyayyar su da aqeel mai cike da armashi Wanda babu wani mahaluqi Wanda zaiga yanda suke gudanar da soyayyar su a "FACEBOOK" baiji sun tafi da imanin shi ba.

~*DAWOWA KAN ASALIN LABARI*~

Sanye take cikin wandon jeans Wanda ya tsaya daidai gwiywarta,yayi maseefar kamata tare da fito da coka-cola shafe dinta ,Riga CE fara armless Wanda Rabin dukiyar fulanin ta suna waje ,fuskan nan tata tasha kwalliya tamkar wacce zataje gasar zaben sarauniyar kyau,pink ribom ne akanta Wanda ta kama yalwataccen gashin kanta Wanda jelar gashin ya zubo a gadon bayanta,

Wani sihirtaccen qamshi ne ke fita a jikinta mai rikitar da zuciyar mai shaqar su sai takalmi plate mai gashi- gashi ta sama da tasa,

Kallon kanta a madubin dake tsaye kekyam a side corner na bedroom dinta taga tayi kyau yanda take buqata dan haka ta zaro wayarta daga cikin aljihun wandon jeans din dake jikinta ta fara daukan photo(selfie),

Ta dauki hotuna sunfi 10 wani ta tsuke baki tamkar mai shirin yin kiss,wani ta baje shi,wqni ta turo kirji wani ta banqare shi har dai taji ta gamsu tana rawa tana juyi ta isa cikin matsaikacin kicin din nata ranta fes,

Daya daga cikin kujerun dake girke a falon ta samu kanshi ta zauna tare da janyo center table ta daura qafafunta akan bayan tayi crossing 1 akan 1,
A daidai wannan lokacin NEPA suka kawo wuta cikin ihu da doki ta miqe tare dayin wani Irin juyi sai gata a gaban TV da redio dinta three loaders.kuna shi tayi tare da sake waqar umar m Sharif cikin waqan shi na jirgin soyayya,

SANADIN FACEBOOKWhere stories live. Discover now