31-40

60 4 0
                                    

♥♥♥♥♥♥
♥♥
*SANADIN FACEBOOK* ♥♥♥
♥♥♥♥

~* Visit to Like my Page-https://www.facebook.com/Mshelias-hausa-novels-607015543050170/?referrer=whatsapp*~

~*Take a second & vote me in wattpad if u like the story and don't forget your comments are really appericiated*~

~*☑wattpad @fareedat husain mshelia*~

*Dedicated 2 zulkifil ibrahim mshelia*

*Story & written*
By
Fareedat husain mshelia.

🅿31

Ta bangaren afreen kuwa kirar sallan farko a cikin dodon kunnenta taqarayin wani juyi hade da qara cukuikuye filo tacigaba da sharan baccinta har aka kira sallan asuba aka tada iqama suka gabatar da ita tanaji amma shaidaniyar zuciyarta nanan nayi mata huduba akan ta huta kayanta danko ta tashi ma tayi sallan Allah ba cireta acikin quncin data ke ciki zaiyi ba ,

~ *wa'iyazu billah,duk da tarin iliminta shaidan ya mantar da ita kissar annabi zakariyya Wanda ya shafe shekaru masu yawan gaske yana roqon Allah daya bashi dah amma Allah bai bashi ba har sai bayan daya fidda rai daga samun wannan rabo tunda ya tsufa,annabi kenan fa afreen Wanda ya kasance zababbe mai shiryarwa ga bin hanyar Allah kuma Dan saqo daga rabbis samawati Wanda baya aikata kaba'ir amma yayi hakuri qarshe ai yaga ribar hakurin nashi toh inaga ke karan kada miya da fatan masu hali irin na afreen zasu gyara wannan kuskuren nasu Dan amfanin karanta novel kadauki Abu mai amfanin kabar Mara shi Allah ya datar damu hanya madaidaiciya Ameen*~

Dan haka tasha baccinta sai guraren qarfe 9 kukan yarta ilham taji ya addabeta dan tuni yarinyar ta Dade da tashi daga bacci pampers din dake jikinta yana tsungulinta tunda ya cika fam da bayan gida da fitsari,

Tsaki taja irin Ilham ta dametan nan ta diro daga kan gadon hade da sabar yarinyar a kafadarta tayi cikin falon,

Ko'ina Baja Baja da kaya kasancewar mijinta ya Dade da tashi har ya dumama sauran abincin Su na jiya yaci yaba khairy sauran kuma ya zuba ma afreen a cooler,

Wani haushi taji ya qara tokare zuciyarta ganin aikin dake maqare akan ta wai duk ita zatayi,wankan yara,gyara daki,shara da wanke-wanke uwa uba gyara kanta ,

Fara tsaftace jikin Ilham tayi hade dayi musu wanka nan da nan ta gyara ko'ina tsaf Tayi wanke wanke ta maida komai a'inda take gyarasu, A sannan ta samu zarafin zama domin yin karin kumallo,

Tana kammalawa ta Kishingide akan kushin Ta janyo wayarta domin hawa online,

Nan taci karo da saqonnin Aqeel Wanda ya kusa buga mata zuciya dan ganin harya taso zuwa gurinta,

Tsoro da fargaba ne sukayi saurin dirar mata acikin qahon zuciya na inda zata ajiye aqeel,ma'ana inda zata zauna suyi hira kuma duk da tasan kwana zaiyi ta amsa mishi da yazo,

Ganin yana online yasa ta shirya mishi kalamai masu dadin gaske ta tura mishi ,

Aqeel dake Kishingide a cikin motar hayan da zai kawo shi suleja,fuskar shi yana fuskantar window ,iska ne mai dadi yake buso shi Saboda yanda diraiban keta tsula gudu akan fafadeden titin,

Aqalla ya shafe kusan minti talatin yana kallon yanda ake wuce dajuka da itatuwan su gwanin ban sha'awa jin alert din shigowan saqo yasa ya juyo da fuskar shi kan allon wayar shi,

Qara fadada murmushin fuskar shi yayi ganin saqon afreen kuma duk ta rudashi da kalamanta masu sanyashi shauqi kamar haka

"dearna kar dai kace min kataso yanzu kana mota"

Wayyo dadi ina zansa kaina yau. Hearty shin da gaske ne zanga masoyin raina?

Kataso ne? Yanzu kuna ina?

SANADIN FACEBOOKWhere stories live. Discover now