page 11-12

138 4 0
                                    


Amatullah
    (baiwar Allah)

Pat 2

By
Zainab Abdullahi
    Real_shaxee

Zamani writers association

____________________________________

Pat dinta ta koma ta zauna tare dayin malalacin murmushi. " Zaku gane baku da wayo da nikuke wallahi daya bayan dayan ku saina koya muku han kali nice fa Zeenatu." wata muguwar dariya ta kwashe da ita.

Indo! Indo! Ta kira mai aikin ta, wata budurwa tayi saurin zuwa ta tsugunna agabanta. Gani hajiya." "maza yau ku dafa mun tuwin shin kafa miyar taushe da nama yaji sosai kuhad'a mun zobo mai dadi kuma daga yau sai nafadi abunda za ada dafa agidannan kunji ko." "To hajiya." tashi tayi ta nufi kicin wanda tacan akwai kofa da zaka bi ta kaika ban garan masu aiki inda suke kwana.

" Ba ance mace tana zama ishashshiya ba agun mijin ta indai tana girki mai dadi to daga yau zan dinga, sasu suna mun mai dadi inga ni da gaske ne, inku wa haka ne na hada abu biyu kenan inta tsula tsiya ta agidannan."

________________________________

Alhaji Muktar kuwa da kansa ya zabowa amaryar sa nana kayan daki masu mugun tsada domun ya haka iyayen ta yin komai shiya yi mata nakece raini.

Gidan amar ya kuwa iya yen ta sunyi rawar gani daidai gwar gwado duk da yayi mata kaya amma saida suka yi mata wasu abu buwan kullun cikin yimata nasiya suke.

Yau Zeenatu tana cikin farin ciki kasan cewar jiya tagama turaren da boka ya bata dan haka tasan aiki yagama yi, shiyasa take cikin farin ciki.

Tana cikin kallo saiga Kamal da wasu maza sun shigo pat din ko kallonta baiyiba ya nuna wa mazan dakuna guda biyu yace. " A wadannan zaku jera kayan kuma ku tsarasu yadda yadace duk da nasan aikin kune, sannan wancan sito din shi zaku mayar kicin ina fatan kun gane." a zabure ta mike." Mai kake yi haka nida gidana zakazo kana canza mun tsarin sa lafiyar ka kuwa." wani kallo yayi mata. " Gidan ki ko gidan ku to kayan amarya ne wacce zata zo nan da jibi su za a jera in kin isa ki hana mugani." kujera yasamu ya zauna inda sukuma suka shiga aikinsu suna futo dana ciki suka jera sababbi, kicin dinma suka daura masa kanta suka jera kaya nan da nan gu yayi mugun kyau falon ma aka canza wasu abu buwan.

Zeenatu kuwa kamar tayi bunduga tashin hankali ya dirar mata dakinta tashiga ta kira wayar Muktar. " Kaika turo wannan mara kunyar yazo tana jera mun wasu kayan banza agida." daga can yace. " E nasan za azo mantawa nayi ban gaya miki ba jeran amar yane kuma ki duba durowar gadonki na ajiye miki kudin zaki yi amfani dasu agun biki,anji ma kuma taila zai kawo miki d... Ko jiran karshen maganar sa bata yiba ta kashe wayar mai hakan yake nufi? Maga nin bai yi aikiba kokuma karya bokan yayi mata?

Tqna jin su Rashida sun shigo sunata maganan ganun su ranta ya sake baci ba adade ba kuma taji mutane sun shigo da yawa can taji Khairi tana cewa yan uwan amaryar ne sunzo ganin daki.

Ji take uwa ta futo tayi musu rashin mutunci amma kuma inma tayi aban za tunda Kamal yana gun zai iya yi mata rashin mutun ci haka ta zauna tana kunci tare da naiman mafuta.

Sai magariba sannan taji shiru futowa tayi falon. " Za kusan nikuka yiwa bara in kona dakin inga ta tsiya badai jeran amar yaba to gobe zaku kwashi toka da gawayi." da sauri ta nufi kicin  ta futa ta baya ta debo fetur din inji ta dakko ashana tanufo falon, cikin rashin sa'a dakin akulle suke duka d'akin Muktar ta nufa dan daukar safaya tana dauka ta sakko cikin farin ciki amma kash Kamal ya canza wa kofofin mukulli wani kututturen haushi ne ya kamata burun ta bazai cikaba maida fetur din tayi ta k9ma dakinta.

Biki yau aka fara shi gida yaci ka makil amma ko kare bai nufi pat din Zeenatu ba ita kuma tana can tana jiran wanda zaizo tasauke masa buhun rashin mutunci amma shiru gashi sun cika gida da kida sai bikin su suke shikuma angon yau kwanan sa biyu ma bata ganshi ba bare ta huce haushi akan sa.

Saboda bacin raima har kuka tayi gashi bada mar barin gidan kar ta futo suga ta futa suyi mata dariya.

Kawar tace ta shigo falon Mumina da sauri ta karasa gun Zeenatu taga tana kuka." ke banzar inace kike kuka tun kan kishiya tashigo to nazo miki da wani abu sai kace ba maceba zo kiji."



Adadin cooment adadin type

AMATULLAH Pat 2Where stories live. Discover now