Aure shi ne hada Wata irin alaka tsakanin mace da namiji , wannan yana nufin hade rayuwarsu ta zama daya, haka nan kuma makomarsu ta kasance daya.
Ko wacce irin al'umma akwai irin matsayin da ta bawa aure .Aure a musulunci wani dauri ne da yake halatta wa ma'aurata (mata da miji) jin dadi da junansu ta hanyar saduwa irin ta jima'i (sex) da sauran mu'amaloli.
Allah (s.w.t) ya halicci mace daga hakarkarin namiji ya kuma sanya soyayya da tausayi a tsakaninsu (kamar yadda ya gaya mana a Alqur'ani mai tsarki). Wannan yana nuna mana cewa alaka tsakanin mace da namiji Allah ne ya kulla ta tun fil azal. Abin da Allah ya hada , kuwa, babu wanda ya isa ya raba. Wannan shi ne yasa a, dabi'ance kowani namiji yana bukatar mace , haka kuma ko wacce mace tana bukatar namiji. Wato ko wane daya bazai iya wadatuwa da kansa ba ya rayu shi kadai dole sai dai hade da waninsa.
Allah (S.W.T) da ya sanya wannan dangantaka tsakanin mace da namiji bai barsu haka nan kara zube ba , suyi ta saduwa barkatai ba tare da wani tsari ba. Sabo da idan abin ya zama haka tsarin rayuwar yan adam zai wargaje .Domin kuwa za, ayi ta samun 'ya'ya ba tare da an samu mai daukan nauyinsu ba .Don kuwa basu da, wini abu guda tsayayye wanda zai dauki dawainiyarsu. Wannan zai sa a rasa samun tausayi a tsakanin al'ummah, domin kuwa ba wani wanda zai dinga jin cewa akwai wata alaka ta jini tsakaninsa da wani , Wanda har wannan zaisa ya rinka jin tausayinsa yana raga masa.
Sabo da haka ne Allah ya halatta aure a tsakanin mace da namiji , ya zama kuma cewa aure sunnar Annabi ne da yake wajibi akan duk mai iko yayi shi. Kuma ya zama dole kafin ayi sai da sadaki da waliyyi da kuma shaidu.Sadaki yana nufin ladan da za'a baiwa mace sabo da halatta farjinta, kasancewar kuma mace bata aurar, da kanta, ya zama dole a sami waliyyi (mahaifinta, ko danginta maza ko alqali, ko sarki) da zai aurar da ita .wannan zai iya zama garkuwa a gareta daga wulakanci da zai iya yiwuwa mijinta ya mata .shaidu kuwa domin su shaida kulla dankantakar aure tsakanin ma'auratan domin kiyaye da yin shaida kan dukkan wasu hakkoki da suka rataya da aure, zuri'a da sauransu.
A page na gaba zakuji Aure a kasar hausa. SHUWAH CE🧕
YOU ARE READING
GIDAN AURENMU AYAU
Non-FictionAssalamualaikum. wannan ba labari ba ne. zan fara wannan rubutu ne kawai don fadakar da matan aure yammata masu niyyar shiga ga me da auren da ma yadda zatayi da sauri tun a waje. Bugu da kari ana iya neman sharawa ta akan, abn da ya shige ma mutum...