MATSAYIN AURE A KASAR HAUSA

3.6K 78 3
                                    

Aure yana da matukar muhimmanci a rayuwar Hausawa. Domin kuwa wanda bashi da, aure a kasar hausa ba'adaukeshi cikakken mutum ba .kuma baya shiga sahun manyan mutane wato dattawa komai tsufansa kuwa. Ba wannan ma kadai ba, har ma yana haduwa da wulakanci iri-iri daga wurin jama'a.Arika masa gori wai ki yaji haushi yayi aure.
Ga misali Nalako mai kama gwagware ba boyayyen mutum bane a kasar hausa musamman kano, inda in watan azumi ya kama yayi kwana goma Nalako, yanayin hawa, rika kewayawa lungu-lungu cikin garin kano yana kama gwagware yana muzantasu a bainar jama'a , ba don komai ba sai don suji zafin abun , hakan yasa suyi aure.
A kasar hausa mutumin da bashi da aure baya kwana cikin gidan masu aure, sai dai ya tare a shago, idan kuwa babu ya dinga kwana a zaure. Har ma inda aka samu kani ya riga yayansa aure, in za'a aiko dansa ya kawo wa yayan wani abu sai ace ungo kaiwa baba na soro! Wannan shi ke nuna irin kaskancin da gwauro yake dashi harma da tuzuru wanda bai taba yin aure ba a kasar Hausa.

GIDAN AURENMU AYAUWhere stories live. Discover now