_*INTELLIGENT WRITERS ASSO*🖊_
🌺 *UWAR MIJINAH..!*🌺
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri, Tareda biyayyah mai Tsanani)_*ALKALAMIN:JANAF*💕
*WATTPAD:JANAFNANCY**DEDICATED To my BLOOD Sisters JANAF*
_Failure is d apportunity to begin again more..INTELLIGENTLY.,Assalamu Alaikum janaf_
*HAPPY JUMMA"AT MUBARAK*
*FRIDAY 12/07/2019*
*6:00am**NOT EDITED*⚒
*NO 5*
""""Kai tsaye Tanema masa Addmission Alegal dake kano,bayan shekara uku yakammallah karatunshi yadawo gida,bayan dawowarsa ya nemi Addmission a B .U .K Cikin sa"a suka bashi Direct faculty of low old site yana kammallah karatunsa na law ya wuce law sch yana gaf da kammallawane, aka aiko daga daga federal court Abuja na bukatar sabbin lauyoyi yara kanana masu jini ajika, da suke kammallah karatunsa awannan shekaran, don haka suna kammallahwa akayi posting dinsu Sunan mu"azzam ne awanda aka tura domin ya samu kyakyawan Sakamako.
Kafim faruwan Wannan Abubuwa da dama sunfaru ciki harda Rasuwar Fadi..Wacce ta rasu bayan ta haifi yarta mace ko ganin kalan yarinyar batayi ba Allah yadauki rayuwarta...Hakika Lokacin da lbrin mutuwar ya iske Suhaima jikinta yayi sanyi matuka ammh duk da haka hajiya baraka tayi tayi suje gaisuwa Suhaima tace atafau bazata ba..Domin ita ko sunan Fadi aka ambata ranta baya mata dadi..Lokacin mu"azzam yana Kano akayi Rasuwar sai da yadawo yaji lbrin shima ya girgiza duk da Fadi bawani mugun saninta yayi ba don acewarsa bata da fara"a..Shettima maraici ya lullubesa ba uwa ba uba..Kuma ba babu yan"uwa moodu yatafi ya barshi..Ga Fadi yau bata agidan duniya..Yayi kuka kamar ransa zai Fita babu mai rarrashinsa..Ahaka Bahgana yasama Yarinya Suna taci Sunan *ZAHIIRAH* wacce tataso cikin gata da tsausayi mai girma..saboda tazama baiwa ce daga Allah sai da uwarta ta shekara ashirin da biyar da Aure kana tahaifeta wanda har sun fidda rai ga haihuwa..,Sai gashi wanda tunda tasamu cikin bata kara lafiya har Ta haifeta kuma ta sanadin Allah yayimata Rasuwa..Yakura ita ta shayar da zaniirah hartakai shekara hudu Ahannunsu lokacin Da Abubakar bahgana yayi Aure da Halimatus Sadiya..Sai yanuna yana son karban Zaniirah tadawo gunsa saboda yadda yarinyar tashiga ran kowa..To babu yarda Shettima zaiyi yafi shi iko daita..Sunaji suna gani Zaniirah tabar hannunsu takoma hannun mahaifinta ya sanyata makaranta ammh tana zuwanmusu wekeed....
Shekaranta Tara Aduniya Halima ta haihu yan biyu Wanda suka ci suna idris Da Aleyu..Tun Tasowar Zannirah aka Fahimci yarinyar dabam ce kwatakwata bata da hayaniya bata sa karkashi da dafarima sunzata sikila ce sai da aka kaita Asibiti suka tabbatar da cewa lafiyarta kalau..Kawai halitarta ce..sai Zaniirah ta wuni adaki ko mgana batayima kowa ko mgana kake mata in kaci Sa"a,ne zata maka mirmishi har hakoranta su bayyana,komai nata cikin Sanyi take gudanarwa Mahgana tana iya bakin kokarinta akan Zaniirah kamar yadda mahaifinta ke kokari akanta..Saboda girmamawan Bare bari yasa Suke kiranta *YAHNA* ma"ana Anty kenan..
***** ******* ****** *****
Dr Shureim Wanda ke matsayin likitan akwakwal a babban Asibitin ABU Chika dake zaria..Shekaru takwas ya kwashe akasar malesia kafin yadawo gida Nageria..yana dawowa ba dadewa, yafara aiki da ABU Chika..Tafiya yake yana Dawowa weeked lokacin Mu"azzam na law school..Hajiya baraka tafara manyanta wacce Su mu"azzam ke kira Hajiyarmu,Suhaima wacce tazama babbar mace sosai takara wayewa,..Shekarar Da Mu"azzam yafara aiki da federal court..Shekarar farko ya gina wani tamfatetsen gida A MAITAMA DISTRICT wanda yaji komai na alatun Rayuwa..Shima ashekaran Shureim ya tamfatsa nashi azaria cikin GRA..shekara na kara zagayowa suka daga dasu da iyayan nasu suka lula kasa mai tsarki...Suka sauke farali..Mu"azzam yaso yahada harda Baffa Shettima ammh tunawa dayayi wlh Sai dai Ummi tahakura da zuwan Saboda zencen wani dangin sa yanzu Ransa zai baci..Duk Hanasan datake bai gujesu ba yana zuwa inda suke wanda Suhaima bata da yarda ta iyane kawai.
Mu"azzam baida aboki baida Amini face Shuraim wanda suka tashi tare sukayi wayau Tare...Mu"azzam Miskili ne nakarshe baya da haniya shima din ba magananne bane..Yana da zuciya ammh yana da hakuri, yana da riko da addini,,baya dawani aiki aduniya bayan Biyayyah ga Umminsa komai tace dashi yake aiko baya iya tsallake umarninta..mtsalanshi da ita danginshi shine ke damunsa domin ko taimaka musu zaiyi sai dai in aboye ammh Ummi bata da makiyi duk Duniya irin Shettima wanda yanzu Nadamar Duniya ta tsufa suka dabaibaye..Yayi nadama ammh baida halin gyarawa don kullum sukayi mu"azzam yazo yafadamai yafadama Mahaifiyarsa Ta yafemasa..Ko yakura dasukayi zaman mutumci Da Suhaima ta yanke alaqa da ita saboda matar Shettima ne ita...
Lokaci Daya mu"azzam da Shureim sukayi shawaran daukan iyayansu zuwa inda suke aiki..Lokacin dayajema Sheettima Sallama yana fadamsa zai dauki Ummi sukoma Abuja da zama saboda ragema kansa zirga zirga na wahalan hanya..Haka Shettima ke kuka ya rumgume Mu"azzam yana fadin kada yabari mahaifiyarshi ta rabasu kada ya gujesa shikadai yake gani yaji dadi..Shikanshi moodun Sai da ya zubar da kwallah Saboda tsausayinsu haka ya jibge musu kayan Abinci da kudi kana yatafi..Wanda yakura sai da tafadama Shettima Tana Fadin" _Wannan Ranar take jiyemaka Shettima gashi tazo maka..Babu kuma wanda zai iya magance maka ita_
Rabuwar Hajiya baraka Da Suhaima Rabuwace ta kuka ta sabo..Wanda suka shude shekaru tare..Ammh yau zasu Rasu..Sunaji suna gani Dr Shuraim yawuce Da mahaiyarsa zuwa Zaria yayimda Mu"azzam suka lula Abuja..Wanda acham ne suka fara gina Sabuwar Rayuwa mai cike da jin dadi,Dr Shuraim yayi Aure da matarsa Zulaika...Ayayinda Hajiya baraka girma yafara kamata tana fama da ciwon kafa ne..Wanda danta ke tsaye kanta da kudinsa da lafiyansa.
Mu"azzam ya zubema Ummi yan aiki acikin gida Tundaga farfajiya har cikin gida ga tsalatsalan motoci ya zubemata da direba..Ga masu girki da masu gyara mata dakuna..Kai komai najin Dadin Rayuwa mu"azzam ya mallakamata shi..Baya da buri Sai nata komai ya Samu *UMMI NA* komai ita domin itace ginshikinshi domin bada din Tsayuwarta kanshi dayanzu wuya ta kashesa..Mu"azzam aboye yake aikama Baffansa Shettima sako in kuma yasamu lokaci yana zuwa gunsu da Abun arziki..Cikin shekaru biyu Brr mu"azzam yayi dukiya mai tarin yawa domin bayan aikinsu Shida Shuraim suna da hannun Jari akasashen waje inda suke gudanar da Kasuwancinsu cikin Turawa.
Ummi tasamu jindadin Rayuwa Da kwanciyar hankali ammh daidai Rana daya bata manta da Abunda Su Shettima suka mata ba..Lokaci bayan lokaci in ta tuna to Ranar wuni zatayi kuka ko dan lelen nata bai isa ya rarrasheta..Tabawa Mu"azzam lbrim Abokin Mahaifinsa khamis wanda yayi mata alqawarin bincikarsa akasar Sudan din..Ummi duk Sanda taji son ganin HajIya baraka direba kawai zata ma mgana ta shirya yakaita sai yamma su kamo hanya..Suhaima Tadauki hajiya Baraka mtsayin yayartace itace kadai zata iya fadamata taji ammh bayan nan babu wanda ya isa..
Zuwan Da Mu"azzam yayi Maiduguri ne Baffa Shettima ya tareshi da wata mgana wacce ta girgizasa ainun takusa sawa Numfashinsa daukwa..Na yabashi *ZANNIRAH DIYAR FADI YAZO YA AURA* wanda babu yarda ya iya Baffa mtsayin Ubansa yake gani inhar ubansa in yanada Rai zai basa Umarni yabi haka Baffa Shettima zai bashi yabi..Babu yarda ya iya illah godiya da nuna biyayya wanda ya sanyayama Shettima Rai harda zubda kwallah..zullumin da Mu"azzam yadawo dashi kenan yana hanya yasamu kiran Ummi wanda daman bai shaida mata zuwanshi maiduguri ba,sakamakon bata tashi ba,Sanda yafice daga gidan bayan yasamu kiran Baffan na gaggawa...
Lokaci daya Shettima yasaki ajiyar zuciya Bayan yadawo daga dogon Tunanin daya dauka Tunanin Abunda yashude achan baya..hawaye suna Shatata bisa idanunsa..gaban babban Rigansa yajike sharkaf da hawaye harda majina lokaci daya, yasaka hannun rigarsa yana sharewa yake Fadi afili.." _*NASANI ADA NA TAFKA KUSKURE AMMH YANZU INA NEMAN HAYAN GYARAWA..NABIYE SHARRIN ZUCIYA DANA MACE TAKAINI TA BARO,AMMH YANZU DA IZININ LAHI ZAN KULLA WANNA AURE FATA YAZOMO HAYAR WARWARAN KOMAI..YA ALLAH KAGA NIYYATA KADAFAMIN*_ yakarshe fada yana fashewa da kuka yakura dake labe agefe itama kukan take lokaci daya tana jin Tsausayin zaniirah domin ta tabbarta bazata taba jin Dadin zama Da Suhaima Saboda yadda ta rike Abun Aranta..
_*Tabdijam akwai badakala..Tayaya Ummi zata amshin wannan zencen..Shin yaya Rayuwar marainiyar Allah ZANIIRAH zata kasance..Duk kubiyo ni cikin Salona na UWAR MIJINA...UWAR MIJINA...Salon na daban ne kada ku manta Janaf dinku ce..*_🌹
*COMMENT, SHARE AND VOTE*
*#Intelligent writer's#*
*#Uwar mijina..!*#
*#Janafi#*