1-2

8.7K 290 6
                                    

[8/10, 17:40] Aishat Muhammad: *MADINAH*
1...

Da wani irin mugun gudu take sakkowa daga stairs tana ihu "Mumy-Mumy"  hawaye fall idanunta tana gudu tana waigen baya wani yaro matashi kyakkyawa wanda kansu daya ke binta shima da gudu a zuciye cikin tashin hankali tace "wayyo Allah Mumy"  a firgice Mum tafito daga kitchen daidai lokacin ta karasa saukowa wani tsalle tayi ta labe a bayan Mumy ta kankame ta sosai tana kuka kaman za'a zare ranta tace "Mumy Khalifa zai dakeni, wayyo Allah Abba na" ganin irin kallon da Mumy kemai yasa ya tsaya bai karaso ba ranshi a bace ya turo baki Yana hura hanci. cike da bacin rai yace "Mumy itace fa ta cinye min chajin game pad dina fa, Kuma..."  wani mugun kallo da mum tamai yasa yakasa karasa maganan cikin tsawa Mum tace "shine kazo zaka daketa saboda gaka isasshe mai karfi ko? , Khalifa! Khalifa! ka kiyaye nifa, duk randa kakara yowa kan yayar ka zaka daketa saina mugun sabama, common get out of here my friend"  cikin fushi ya juya yay Sama kaman yay kuka saida Mum taga yabude dakin shi ya shiga sanan ta juyo ta kalleta hakan yasa jikinta yafara rawa sosai tana goge hawayen idonta muryan ta har rawa yake tace "Yakuri Mumy bazan karaba Allah kuwan"  kwafa Mum tayi tace "bakya rike girman kiko Madina, duk randa Khalifa zai miki shegen duka bazan cemai kalaba saidai nakara miki wani, barima nakara ma ganin ki a dakin shi Sai kinyi mamakin abunda zan miki stupid girl"  hawaye taciga da sharewa tana haki wani harara mum ta galla mata tace "wuce muje kitchen kimin aiki" sumi sumi tabi bayan mum tana goge fuskar ta. 

Wani katon doya Mum ta mika mata tace "oya fere doyan nan and be fast" karba tayi ta ijiye, tray ta dauko a wajen ijiye tray ta dauko big bowl  ta je wajen sink ta Bude tap ta tari ruwa daidai sanan ta dawo tsakiyan kitchen din ta tsugunna, dogon gashin kanta tafara hadawa ta tupke da kyar har wani ajiyan zuciya ta sauke hakan yasa mum ta kalleta ta balla mata harara da sauri ta dukar da Kai saboda tasan yau ita mai laifi ce.  Ahankali tafara fere doyan ta gama ta yayyanka takai gaban sink ta wanke tass sanan ta karasa kusa da Mum dake starring soup ahankali tace "Mumy nagama"  batare da Mum ta kalleta ba tace "ki daura a wuta ki dafa"  da sauri ta juya ta Bude carbonate din da ake ijiye pots ta ciro madaidaicin pot ta dauraye sanan ta zuba doyan tasa ruwa kadan da small salt ta daura a wuta.  Kashe gas din gaban Mum tai taje wajen sink ta wanke hanayenta tadau towel ta goge hannunta ta ijiye sanan tace "in yayi ki zuba a warmer kikai dining, saura na ganki a Sama batare dakin gama abunda nasaki ba"  ta karasa maganan tana hararan ta, langabar da Kai tayi Mum ta juya tabar kitchen din. Sai wuraren shida da rabi tagama komi tai arranging akan dinning sanan tai sama tana goge zufan goshin ta kaman ta shiga dakin Khalifa tunawa da warning din Mumy tamata yasa ta wuce dakin ta sumi sumi kaman mara gaskiya. Bude dakin tai ta shiga daki ne mai kyau dan babba anmai fenti pink zanin gadon ma pink Sai kamshi ketashi daga dakin bayi ta shige ta watsa ruwa tai alwala ta fito, wardrobe ta bude ta dade tsaye kafin tasa hannu ta zakulo riga da sket na atampa agurguje tasa ta zira hijabi tai salla saida ta Idar sanan ta shafa mai ta fesa turare da Mumy ta siyo mata sanan ta bude kofa Jin maganar Abban ta. dan dukawa tayi tace "sannu da zuwa Abba" wanda takira da Abba yakara sa cire malum malum jikin shi ya mikama Mum dake gefenshi ya kalleta da murmushi a fuskar shi yace "Madina ya gida, kinyi salla?"  murmushi tayi dake kara mata kyau tace "eh Abba nayi"  murmushi yay yace "Dats good, kutafi dinning kufara cin abinci I will join you soon"  bude dakin shi yay ya shiga Mum nabiye dashi itakuma ta sakko kasa. 

Bai wani dade ba suka sakko tare duk suka zauna har zasu fara cin abinci Abba yace "ina babana?"  tabe baki Mum tayi ta kalli Madina tace "ke jeki kira Khalifa"  da sauri ta kwalalo manyan idanunta cike da tsoro ta kalli Mum, hararan ta Mum tayi tace "I said go and call Khalifa bakiji bane?"  da sauri ta juya har tana tuntube tai sama ahankali ta bude kofar Yana zaune kan gadon shi da aka shimfida bedspread na football a fusace ya kalleta hakan yasa tadanyi baya da sauri sanan tace "Abba yace kazo"  tana fadin haka ta juya da sauri ta sauka kasa taje ta zauna sanan tace "gashi nan zuwa Abba".  Karasowa yay dinning din Yana sanye da jallabiya fara Sai a lokacin nakara ganin kamanninshi da Madina sosai zama yay a kujeran dake kusa da nata ahankali yace "Abba sannu dazuwa"  da murmushi akan fuskar Abba yace "waya tabamin Kai babana?"  kaman jira yake yace "Abba  ba Madina bane ta cinyemin chajin game pad dina kuma shine Mumy taitamin fada"  karasa maganan yay Yana turo baki Abba ya kalli Mum yace "Haka akayi wife?"  murmushi tadanyi dataga yanda Khalifa ya kumbura fam ahankali tace "Alhaji I've been warning Khalifa batun yauba bakomi Madina zatamai ba ya wani taso mata zai daketa saika ce babanta, baida kyau yayar shi ce ba sa'arshi bace, saisa namai fada dan inda bana gidan nan da Allah kadai yasan irin dukan dazai mata inya Kamata, yaro Sai shegen zuciya kaman kuturu " takara she maganan da tsaki shiru Abba yay nayan sakkanni cike da natsuwa yace " Madina" " naam ta amsa yanda tai zuru zuru yasa Abba yaji dariya Yazo mai ahankali yace" banason neman tsokana I think I bought the game pad for you maisa kika taba nashi?" raurau tai da ido tace "Abba screen din nawa yay scratch ne"  murmushi Abba yay yace "ok remind me gobe zansa adamu Yazo ya karba yakai a gyara miki karki kara tabama Khalifa abinshi batare daya baki izini ba" ahankali tace "to Abba"  "and you Khalifa" ya kalli, Abba yace "duk randa labari ya sameni kace zaka daki yayar ka saina mugun sabama dan ban yarda da raina na gaba dakai ba, kaji ko?"  ahankali yace "to Abba"  Abba yay murmushi "OK less eat" ahankali Madina tai tapping shoulder Khalifa juyowa yay ya kalleta langabar dakai tayi tace "am sorry leefa kaji"  hannu ya dunkule ya mika mata yace "chock-noko"  itama dunkule hannu nata tai ta kaimai suka buga suna dariya shikenan an shirya.  Iyayen suma suka kalli juna sukai murmushi kafin a natsu aka faracin abinci. 
Maman Abd Shakur

[8/10, 21:42] Aishat Muhammad: *MADINAH*
2...

Wajajen 6:30 na safe ta tashi da addu'a tashi daga bacci a bakin ta ahankali ta yaye bargon data lulluba dashi ta sauko da dogayen kafafun ta kasa tadade a zaune tana sossosa idanun bacci kafin ta mike tsaye dan gutun rigar baccin dake jikinta ta cire tadau towel ta daura bathroom ta shiga saida tai brush sanan tai wanka tafito shirya kanta tai tsaf ganin bata salla  tadau dogon bakin riga kawai tasa gaban mirror taje ta dau comb sanan ta juyo tafito daga dakin jin magana a falo yasa ta sakko kasa Mom tagani da yar aikin su Mama mairo suna magana chan gefe kuma Khalifa fa ne yana assignment din da aka basu dan gobe school gobe Monday ahankali ta karaso wajen kusa da Mum ta zauna tana turo baki tace "Mumy ina kwana" kallon ta Mum tayi ta juya ta cigaba da magana da mama Mairo juyowa tai ta kalli Mama Mairo tace "ina kwana Mama"  washe hakora Mama Mairo tayi tace "yar gidana antashi lpy, Mai aka miki kike kumbure kumbure"  kallon Mumy tayi tace "nakasa taje gashin nan ne" da sauri mama Mairo tace "Zona taje miki kinji"  tsaki Mum tayi tace "barta Mama Mairo katuwa da ita kullum Sai antaje mata kai"  murmushi mama Mairo tayi tace "ayi haka hajiya bari nataje mata gobe  nasa amata kitso, zo kinji diyar kirki"  tashi tayi taje gaban Maman Mairo ta zauna tana kallon Mum data dauke kai ta cigaba da kurban tea dake hanunta".  Ahankali Mama Mairo ke taje mata gashin har tagama ta mata parking kan da sauri ta tashi taje kusa da Khalifa tace "Leefa wat are you doing?" daidai lokacin ya rufe book din ya kalleta yace "Assignment din Biology"  kwalalo ido tayi tace "Leefa zaka bani na kwafa?"  wani matsiyacin kallo yamata yace "lallai ma kina can kina baccin ki kinki zuwa muyi nagama abuna saina baki ki kwafa?" matso wa kusa dashi tayi ta daura hanunta a shoulder dinshi tace "plz mana Leefa zan dafama indomie dinan mai dadi" dariya Khalifa yay yace "oya jeki dafamin make it quick"  da sauri ta tafi kitchen. Hararan ta Mum tayi dukar dakai tayi ta tafi kitchen sumi sumi koda Khalifa yaci yaci indomie yay Nak saida yaja aji sanan yabata ta kwafa. 

Da sassafe Mum ta tashe su Saboda su shirya da wuri su tafi school karsuyi latti wanka sukeyi suka shirya Khalifa yafara sakkowa dinning rike da school necktie dinshi a hannu ya mika mum dake zaune akan kujera yace Mumy samin karba tayi yarage tsawo ta samai tace "ina Madina?"  da sauri yace "Mumy tana gaban mirror tana kwalliya" murmushi kadan mum tayi dan tasan shairin Khalifa ne tace "oya jeka ce tafito kuci abinci Adamu na jiran ku a mota"  da sauri yay sama ko minti biyu baiyi ba suka sakko tare tana sanye da black cover shoe tasa white sock Sai green sket daya tsaya daidai guiwarta da long-sleeved shirt mai gida gida datai tokin dashi Sai pink karamin hijab daya bayyana gashin kanta baki sidik tagaba fuskar ta bakomi ta rike wani katon black shoolbag tana saukowa zama tai a dinning Mum da kanta tahada musu tea da fried plantain da Irish tea kawai suka shanye suka tsitsikari plantain din sanan suka mike karaso wa garin mum sukayi ko wanensu ya dugo sukai pecking chick nata Madina tace "love you Mumy"  Khalifa yace "love you Mum"  murmushi tayi tace "love you too make sure you guys study hard concentrate banda wasa"  da sauri suka juya zasu fita Mom tai ijiyan zuciya tace "Madina" da sauri ta juyo tana kokarin goya jaka tace "Naam Mumy"  Mum tace "behave, karki nemi fadan Khalifa Kuma"  murmushi tayi tace "love you Mumy bye"  da sauri tabi bayan Khalifa daya dade da fita daga dakin bayan motor kiran Lexus ta bude ta shiga ta zauna Driver yasa suka fita daga anguwar tasu GRA zaria, daidai Hallmark International school driver yay parking hakan yasa suka fito suna mai bye kafin su juya su shiga school. Upstairs suka tafi atare suke tafiya wani aji suka shiga wanda agaban shi akasa SS2-B gata ga Khalifa yan ajin Sai kallon su suke. 
Maman Abd Shakur

MADINAHWhere stories live. Discover now