6-8

3.4K 144 2
                                    

[8/16, 20:49] Maman Abd Shakur: *MADINAH*
HWA

6...

Da Khalifa sukaci karo a kitchen saboda tsabegen sauri ta wuce shi, da kallo ya bita ganin yanda ta birkice hakan yasa ya bude kofa yashiga garden din Kalle Kalle yay saidai baiga abinda yabata tsoro haka ba hasalima ice cream yagani Yana mishi welcome tsugunna wa yay ya dauka dariyar mugun ta yay yakoma kan swinging chair ya zauna Yana chan ice cream din, tass ya shanye ice cream din Yana lallashe baki ya jefar da robar a bin din wajen. ahankali ta bude kofar kitchen din, balcony din next compound din ta kalla ganin babu kowa awajen yanzu yasa tafito da sauri tana waige waige dan bataga ice cream dinta ba ganin Khalifa zaune yana wani shillo abinshi yasa taje gabanshi ta rike kugu tace "Khalifa where is my ice cream?" wani matsiyacin kallo yamata hakan yasa tadan matsa baya kadan yace  "namiki kama da barawo ne?"  kaman ance ta kalli gabage bin dake wurin ta hango roban ice cream dinta kafa ta bubbuga akasa idanunta cike da hawaye tace "wlh saika biyani abuna, jiya fa I slept off bansha nawaba Kai kasha almost 3 rubbers yanzu last one dinan shine zaka shanyemin wlh saika biyani" tafashe da kuka agaban shi tana bubbuga kafa, dariya Khalifa yay harda tafa hannu ya kalleta yace "kema ai haka kikemin, Kuma wlh ko kitashin min daga gaba kona miki shegen duka kinda ga su Mumy na sitting room"  ihu takara rafkawa ta tsugunna a wajen tana mai kuka sosai, hannu rigan shi yahau gyarawa ya ciji lebe yace "ok lemme show you" yawani sakko hakan yasa ta mike da sauri ta juya da gudu ta kwalla ihu tace "Mumy kingan shiko" kaman ance ta daga ido, nan suka kara hada ido da Guy din da sauri ta dukar dakai, kofar kitchen ta  bude ta shiga da gudu tana kuka tana kiran Mumy shiko Khalifa mai zaiyi inba dariya ba harda rike kai,  hakanan shima guy din yaji dariyar yazo mai, tabe baki yay tadau phone dinshi kirar iPhone 7 daya bari akan table ya bude kofa ya koma dakin shi.  Lekowa Muhibba tayi ta window tace "zonan Khalifa" hanun rigar shi ya warware ya bude kitchen door din shima yay cikin gida Mum na zaune tana duba Meelmoh magazine Madina dake gefen Muhibba tana kuka tace "Anty gashinan yazo" hararan ta Muhibba tayi cike da takaici kafin ta kalli Khalifa tace "waya ce ka shanye mata ice cream?"  kwantar da murya yay yace "Anty itama fa haka tamin rannannan shine narama"  cikin kuka Madina tace "toba nabiya ka ba"  tsaki Mum tayi ta rufe jaridar hanunta tace "for Godsake kuncikamin kunne, Khalifa!" adaburce yace "naam Mumy"  cike da bacin rai tace "get lost, Idan nasake ganinka a downstairs make sure masallaci zaka inba hakaba saina bata maka rai"  da sauri yajuya Yana dariya Mum tace "And you too Madina get lost" cike da takaici ta tashi tabar wajen itama tana kuka sosai, murmushi kawai Muhibba tayi tace "ni Mumy bantaba ganin inda ya ke tsoron kani bafa" tabe baki Mum tai tai flipping d next page tace "gashi nan Allah yabaki kin gani" ta cigaba da karatun jaridar ta. Daki ta bude ta kwanta akan gado tahau rusa uban kuka dan abun yay mata ciwo ahaka bacci yay awan gaba da ita. Koda Muhibba ta shigo ganin tai bacci yasa tadau Ihsan suka fita daga dakin koda magariba ba da ciwon Kai ta tashi wanka ta shiga bayi tayi tadauro alwala tazo tai salla AL qur'ani ta karanta har lokacin Isha ta tashi ta kabbarta sallan tana idar wa tahada da shafa'i da wuturi tai kwanciyar akan gado, tanaji Anty Muhibba na kiranta tazo ai dinner tai shiru kaman tana bacci.  Wuraren tara da rabi Mum ta turo kofar dakin binta tai da kallo a natse tace "nasan kinaji na kizo dakina ina neman ki" juyawa tai ta bar dakin ahankali ta mike ta zira bathroom silifas tai hanyar dakin Mum karo sukaci da Khalifa dake fitowa daga dakin dauke Kai tayi tai shigewar ta dakin Mum da sallam ahankali ta zauna akan carpet tana wasa ya warwaron hanunta Mum datagama amsa Wayan Abba ta ijiye phone din ta kalleta tace "dakika ki zuwa kici abinci kinxaci rokonki za'ayi?" shiru tayi kanta akasa, mai Mumy ta dauka daga kan mirror ta bude ta tsiyaya kadan ahannu ahankali tace "jeki dibo abinci kizo nan" ahankali ta mike ta sauka kasa spaghetti ta diba kadan tasa fish sauce data gani a sama tadau folk da one bottle of Eva water ta koma dakin Mumy zama tai tafara ci, da sauri ta bude ruwa tasha kawar dakai Mum tayi daga kallon ta, da kyar taci rabi tadau abincin ta koma kitchen ta ijiye ta dawo ta zauna ahankali Mum tace "gobe Muhibba zata tafi" da sauri ta kalli Mum murya chan kasa tace "gobe Mumy?" gyada mata Kai Mumy tayi tace "uhm ki shirya Zaki rakata airport Karfe 9,jekiyi bacci saboda kitashi dawuri" ji tayi duk bataji dadi ba Dan tana mugun son Anty Muhibba.
Ahankali ta bude kofar dakin ta ta shiga ganin Khalifa a zaune kan gadon ta yasa ta daure fuska tace "zoka fita kona hadaka da Mumy" murmushi yay harda kanne mata ido yay kasa da murya yace "haba Midi baby, yakuri to am sorry, Idan Abba yadawo zance yasai mana wasu ice cream din kinji big sis"  turo baki tai tabi ta gefenshi tai kwanciyar ta akan gado ahankali yace "na face am sorry kinji, plz na" yaja hanunta murmushi tamai dake karama fuskar ta kyau tace "tona hakura" yauwa kokefa kashewa sukayi sanan yamata good night yatafi dakin. 

MADINAHWhere stories live. Discover now