page 29

2.6K 146 5
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SAREENAH*
_(A romantic love story)_

*Written by*
'''phatymasardauna'''
*🎈Mrs Sardauna🎈*

*dedicated to Sameer naseer deen*

*🌈Kainuwa writers association*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

*Whattpad*
'''fatymasardauna'''

*Page 2⃣2⃣2⃣to 2⃣2⃣5⃣*


Gaba Daya jarabawan SAREENAH sunyi kyau Sosai tasamu sakamako Mai kyau Wanda hakan Kuma bakaramin Dadi yayimataba,, babata lokaci Fahad yasaimata admission a Cikin babban University dake cikin garin Kaduna Wanda Anan Rumana take Karatu saidai it's Rumana tana 200 hundred level ne yayinda SAREENAH ke 100 hundred level , Amma kodayaushe suna tare da juna dazaran sun fito a lecture

Karfe Biu daedae suka fito daga English lecture din dasuka shiga tun 7am sai yanzu 2pm Gaba daya Agajiye take ga wani Dan banzan Yunwa dake sasulan cikinta ,,,

Kan wata kujera da akayita da katako ta zauna ,,

Wayarta dake cikin jaka tahau Kara alamar shigowar Kira ,,, Yaya Marwan shine sunan Daya bayyana Akan Screen din wayar Murmushi Tayi hade da peacking call d'in ,,,,

" Fatan Gimbiyata tana lapia " Marwan yafad'a cike da Nishad'i,

Murmushi tayi hade da sunne kanta Akasa kamar yanaganinta ,, sanin dayayi cewa Kunyarta bazata barta tabashi amsar tambayansaba ,,
Yace
" Nanda 1 hour insha Allah Inacikin Garin Kd " saurin Waro idanunta tayi kamar yanaganinta Tace " Dagaske Ya Marwan Amma Maiyasa bakasanardaniba Tuntuni "

" Nakira Wayarki a time din dazan taso switch of ,,, Namatsu Nazo Naganki my angle Dina kinsan yanda nake missing Kyakkyawar fuskarki Kuwa"

Bahaka tasoba Amma yazatayi tunda haryataso Kuma Yama kusa shigowa Kadunan , danhaka Tace Allah yakawoshi lapia,,

Daidainan Rumana takaraso wajen itama daganinta Agajiye take dansuma yau sunsha Lecture ,,
Kasancewar Aiki yamawa Fahad yawa yasanya driver ne yazo daukansu ,,,

" Yanaga duk jikinki yayi sanyine Sis maike faruwa " Rumana tatambayesa SAREENAH ,,
" Wlhy sis yanzun Ya Marwan yakirani Wai Nanda 1hour zaishigo KD "

Dariya Rumana tayi hade dacewa " Kai kice munada Babban bako ,, shine Kuma kikayi sanyi Haka kobakison zuwannasane ?,,

" Bawai banason yazobane kawai dai Gaskia nibanson Yasakemin Maganar Aurene kamar Yanda yayimini wancan zuwan NASA dayayi duk dacewa Nafadamai kaf abunda yafaru Dani Amma yadage Waishi Aurena yakeso ,, Nikuma Gaskia ayanda nafara karatuna banson abun da zaikatsemini shi " SAREENAH tayi maganan cikin Damuwa ,,

d'annisawa Rumana tayi hade dacewa " kinada Gaskia ,, Amma Agaskia kada kibari Marwan yakubucemiki domin bakadanba gayen ya hadu wlhy ga hankali Kuma Yanada hakuri uwa uba Kuma kinsan Yana matukar Sonki , nidai har cikin Zuciyata Nakesonki Dashi,,

Dedenan Suka Iso gida ,,

Babata lokaci SAREENAH tafad'a toilet tayi wanka , Koda tafito Mai tashafa ajikinta hade da Shafa fowder hade da Sanya lipstick light peach kalan labbanta Eye pencil tasanya a cikin idanunta Hadi dasanya Mascara tataje Tarin eyelashes d'inta Wanda yawansu yasanya Wanda baisantaba zaizaci Nakanti Tasanya,,

Wata fitted gown na Atamfa blue tasanya Wanda yayi matukar Amsar white skin d'inta

Dogon gashin kanta tatubkeshi atsakiyar Kannata ,,
Wani Vail blue colour tadauko Hadi da Yafawa ajikinta dayake Vail din nada Dan girma har cinyarta yazomata, Sosai da Sosai tayi kyau

Flat shoue d'inta tazura hade da daukar wayarta tafice zuwa falo ,,

Ummu da Rumana ne Zaune Sai Kuma Fahad ,,
Zama tayi kusa da Ummu hade dayimata barka da Gida ,,

SAREENAHWo Geschichten leben. Entdecke jetzt