Tsatsuba 2c

259 7 0
                                    

Naku #SAS
IT'S B Y IBRAHIM

TSATSUBA
Littafi Na Biyu (2)
Part C.
.
YAYINDA SARAUNIYA larbisa taji wannan batu
sai tayi murmushi tace koma menene a ransu ai
zamu gani tunda dai sannu sannu bata hana
zuwa
sai dai a dade ba aje ba, Tsoho Huzallatul
marwas ya
gyada kai yace tabbas zancenki Dutse ne
Larbisa tace wai shin yanzu ina Muka dosa ne?
Huzallatul marwas yayi murmushi yace in banda
abinki
ya zaki tambayi kaza hanyar rafi, ni kaina ina bin
jagorancin jaka ne, duk inda naga ta nuna nan
nake
bi damu
Amma ai idan baki manta ba zamuje neman
jaruma
larifat ne wacce zata yi mana jagora a cikin
daji na biyu wanda shine dajin Ujurul majnun
ki kwantar da hankalinki don nasan cewar ba
zamu dauki wani dogon lokaci ba muna tafiyar
zamu riske ta
bisa taimakon wannan jakar sihiri nawa.
Koda jin haka sai Larbisa tayi shiru bata kara
cewa
komai ba
haka dai aka ci gaba da wannan tafiya ba dare ba
rana
babu abinda yake sawa a tsaya ko a yada zango
face
gajiya ko yunwa da kishirwa, har tsawon kwana
uku
sannan suka iso wani babban birni mai kyau
gaske wanda aka kawatashi da gine gine masu
kyau da kawa
ita kanta sarauniya larbisa sai da wannan birni
ya birgeta ta raina kyawun nata birnin harma
tana
cewa a cikin ranta lallai duniya da fadi hakama
abin cikinta a iya tunanin sarauniya larbisa ba za
a taba samun birnin da
yafi nata girma da kawatuwa ba a duniya da yafi
nata
girma da kawatuwa ba a duniya amma sai gashi
tun
kafin ma tafiya tayi nisa ta fara ganin cewar ba
haka
bane
Tun daga nesa da masu gadin kofar birnin suka
hango
tawagar sarauniya larbisa sukaga alamar cewar
manyan mutane ne masu daraja sai suka bude
musu kofada sauri har daya daga
cikinsu yayi musu jagora izuwa fadar birnin
tun akan hanya kafin a isa fadar sai jaruma
shumaira
ta matso kusa da larbisa ta dubeta tace to wai
shin mu
yanzu menene yashigo damu cikin wannan
gari alhalin mun zo ne neman jaruma larift kuma
ga
yadda aka bayar da labarinta ba zata yi rayuwa
ba
a cikin gari sai dai a daji?
Koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa tayi
murmushi tace ai da dan gari
akanci gari, yanzu idan muka ce zamu tafi
neman jaruma larifat
bamu san a cikin dajin da take ba amma da zarar
mun shiga cikin birnin zamu sami labarin inda
take
wata kilama mu sami karin haske akan yadda
zamu tunkareta ba tare da mun fuskanci
wata matsala ba
koda shumaira taji wannan batu sai tayi ajiyar
zuciya tayi shiru bata kara cewa komai ba...
Fadace kasaitacciya abar kwatance domin
lokacin
da aka shigo dasu sarauniya Larbisa cikin fadar
sai gaba
dayansu suka kama kalle kalle suka zama kamar
yan kauye
saboda ganin irin kyan fadar da kawatuwarta
A wannan lokaci ne larbisa ta dada tabbatar
da cewar gaba da gabanta Aljani ya taka wuta
Ita dai a iya saninta a can nahiyoyin dake
bangarenta
babu wata kasa mai
girma da karfin Arziki kamar kasarta don haka sai
ta
fara tunanin cewa a duniyar ma gaba daya ba a
taba samun kamarta ba amma a yanzu
da ta tsinci kanta a cikin wannan birni da
wannan
bakuwar fada sai ta karyata kanta, wani
kyakkyawan
saurayi ne na kwatance bisa karagar mulkin
wannan fada ya yi babbar shiga ta
alfarma irin wacce attajiran sarakai da suka
gawurta
ne kadai ke iya yinta
domin tufafin dake jikinsa darajarsu takai jarin
wani mashahurin attajirin, hatta takalminsa da
kwagirin dake
hannunsa na lu'u lu'u ne a yatsun hannayensa na
hagu da dama akwai zobuna guda shida kuma
duk na
zinare ne masu tsadar gaske, shi kansa rawanin
dake
kansa da falmaran din dake jikinsa da zaren
zinare
a aka dinkasu
koda jaruma shumaira da sarauniya larbisa
sukayi Arba da wannan sarki sai kyawunsa da
kwarjininsa
ya dimautasu sukaji nan take sun kamu da
tsananin sonsa
Hakika babu wata 'ya mace da zata ga wannan
sarki
bataji ta kamu da tsananin sonsa ba, saboda
baiwar
da allah yayi masa ta kyau da arziki, gashi idan
yayi ado sai kaga tamkar dawisu ne
koda shigowar su sarauniya larbisa cikin fadar
sai sarkin ya dubesu sau daya ya kau da fuska
kuma
babu annuri akan fuskar tasa, Al amarin da ya
dugunzuma
hankalinsu kenan domin a tunaninsu kyawunsu
kadai zai iya sawa sarkin yayi marhaban dasu
bare
kuma ga matsayi na sarautar larbisa, cikin sanyin
jiki suka karasa kusa da karagar mulkin sukayi
cirki
cirko
caraf sai tsoho isham ya zube kasa gaban sarki
ya
kwashi gaisuwa sannan ya gabatar da sarauniya
larbisa da jaruma shumaira ya kara da cewa
yakai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa ba
wani abu bane ya kawomu birninka ba face
neman
jaruma Larifat ma abociyar basira da hangen
nesa
saboda muna son tayi mana rakiya izuwa dajin
ujurul majnun domin biyan
wata muhimmiyar bukata ta sarauniya Larbisa.
Koda jin wannan batu sai sarkin ya mike tsaye
zumbur
daga kan karagarsa ta mulki. Fuskarsa cike da
annuri
ya kama kafadun tsoho Isham ya tashe shi tsaye
ya jashi har kan karagarsa suka Zauna tare, su
sarauniya larbisa ma sai yasa aka
basu kujeru na alfarma suka zauna sannan aka
kawo
musu abinci da abin sha na alfarma suka kama
kimtsa
cikinsu suna masu murna da mamakin yadda
akayi
nan da nan ra'ayin sarkin ya sauya bisa jin
abindake
tafe dasu
sai da kowa ya gama kimtsawa ya sami natsuwa
sosai
sannan kyakkyawan sarkin ya dubi tsoho isham
yace yakai wannan dattijo kayi sani cewa yau
shekara
bakwai kenan ina fama da tsananin so da begen
wannan jaruma larifat amma ko sau daya bata
taba
kallona ba tayi mini murmushi bare ta karbi tayin
soyayyata sai dana kwanta rashin lafiya sau
bakwai
sakamakon ciwon sonta da ya kayar dani amma
bata
taba zuwa ta dubani ba ni da ita bata taba yi
mini magana
ba kuma bata taba amsa gaiyatata ba izuwa
wannan gidan sarauta
Lokacin da na dameta da aika manzanni da
kyaututtuka
iri iri na duniya sai ta tattaro duk abinda nake
bata na tsawon shekaru bakwan ta dawo mini
dasu
gami da wasika
A cikin wasikar ne ta shaida mini cewa na daina
bata lokaci
na da tunanina a kanta
domin ta daukarwa kanta alkawari cewar ba zata
taba yin aure ba ko soyayya
har sai tayi gagarumin abin gwanintar da wani
bai taba yi ba a duniya
lokacin da naji wannan batu sai na kamu da
tsananin
bakin ciki kuma na fashe da kuka na takaici
domin banga ranar da larifat zata cika wannan
buri
ba
daga wannan rana ne nima na yi alkawarin na
daina cin abinci mai dadi na daina kwanciya a
wuri
mai kyau kuma na daina murmushi da sukuni
har izuwa karshen rayuwata face a ranar da naji
cewar ta sami damar da zata cika burinta
A tsawon shekaru bakwai da suka gabata
wannan dama bata
samu ba sai yanzu naji kunzo mini da wannan
batun
na zuwa kogon Kitabul sihir inda littafin tsatsuba
yake sai naji
a jikina cewar lokacin samun yardar larifat yayi a
gareni
domin a yanzu ne zata iya yin jarumtakar da har
abada
ba za a mance da ita ba a duniya, ko shakka
babu na san cewa
larifat zata karbi wannan
tayi naku domin bata tsoro ko shakkar wani abu
mai rai akan biyan bukatarta, babu wani abu
wanda
zaku iya biyanta da shi domin ta wuce daku ta
cikin
dajin ujurul majnun face kwadayin cika na ta
burin
ba wani abu da yake burge jaruma larifat a cikin
wannan duniya, saboda ta rasa iyayanta yan
uwanta da dukkan danginta
bisa wannan daliline ta kebe kanta daga cikin
mutane
ta koma cikin daji da zama inda ta zabi ta karasa
sauran
rayuwarta gaba daya
yanzu dai a gajiye kuke, don haka zan sa a kaiku
masauki ku huta washe gari da safe ni da kaina
zanyi muku jagora izuwa dajin Da jaruma larifat
take domin ku gana da ita, ku sanar da ita
bukatar dakuka zo da ita a gareta.
Amma ina neman wata alfarma guda daya a
wajanku?
Alfarmar kuwa itace ina son nima nayi muku
rakiya a cikin wannan tafiya domin idan kuka tafi
kuka barni fargaba tunani da begen halin da
larifatke ciki zai iya jefani cikin wani mugun hali
koda sarki AYUBUL HASNU yazo nan a zancensa
sai kowa
ya cika da mamaki musamman sarauniya larbisa
da shumaira
Kai ni kAina saida na cika da mamakin
wannan sarki
sarauniya larbisa ta dubi sarki Ayubul hasnu cikin
mamaki tace yakai wannan sarki mai daraja kayi
duba izuwa wannan daula da kake ciki ka dubi
girman kasarka da tarin arzikin dake cikinta ka
sani cewa
akwai mata da yawa masu kyau a sassan duniya
wadanda zaka iya mallakarsu da karfin dukiyarka
da mulkinka saboda me yanzu zaka siyar da
rayuwarka don baiwarka?
Lokacin da sarki ayubul hasnu yaji wannan
tambaya daga
bakin sarauniya larbisa sai ya bushe da dariya
kamar ba zai daina ba daga bisani kuma sai ya
hade fuska tamkar an aiko masa da sakon
mutuwa
nan fa fadar tayi tsit kamar babu mai rai a
cikinta
kawai sai aka ga idanun sarki ayubul hasnu sun
ciko
da kwallah har hawaye ya zubo masa, sarki
ayubul hasnu
ya dubi sarauniya larbisa cikin nutsuwa yace
yake sarauniya larbisa kiyi sani cewa a duniya
babu
wani abu wanda yafi soyayya karfi da hadari
masoya da yawa sun rasa rayuwarsu akan
tafarkin mallakar masoyansu
ba komai ne ya janyo hakan ba face duk rayuwar
da babu masoyi dai dai take da zama a cikin
kurkukun
daurin rai da rai kisan sani cewa ke da jaruma
shumaira duk kun kasance kyawawan matan da
babu kamarsu a duk cikin fadin kasata da
nahiyarmu amma kuma baku kama farcen kafar
jaruma larifat ba a fagen kyau kunga kenan
a yanzu babu wata ya mace da zata iya maye
gurbin
larifat a wajena banda fagen kyau a bangaren
jarumta
kuwa ina mai tabbatar muku da cewa in daku
biyun
nan zaku hada karfinku ku yaketa ba zaku taba
samun galaba a kanta ba
koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa da
jaruma shumaira suka bushe da dariya domin su Imran_aley
a
ganinsu ma tatsuniya ce abinda sarki Ayubul
hasnu yake fadi
shumaira ta dubeshi tace aiko yarima RUHAISU
dan sarki ZAIYANU na birnin kufa wanda masana
da masu
bincike suka tabbatar da cewar babu mai karfin
damtsensa da sa arsa idan muka hada karfi nida
larbisa sai mun gama dashi bare wata jaruma
larifat wacce ta
kasance 'ya mace kamarmu
yayinda sarki Ayubul hasnu yaji wannan batu sai
yayi murmushi yace ai
shi kenan inda babu kasa nan ake gardama
Kokowa, ni dai shawarata guda daya ce a gareku
duk abinda zakuyi kyi shi da cikakkiyar hujja
domin banson ku yi irin kuskuren da SADAUKI
HULKAS MAI HULAR LAMSARA YAYI.
Koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa da
jaruma shumaira suka
dubi junansuCi gaban PART C BOOK 2

domin banson ku yi irin kuskuren da SADAUKI
HULKAS MAI HULAR LAMSARA YAYI.
Koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa da
jaruma shumaira suka
dubi junansu cikin mamaki larbisa ta juyo ta dubi
sarki
Ayubul hasnu tace wanene kuma sadauki Hulkas
mai hular lamsara?
Koda jin wannan tambaya sai sarki Ayubu
hasnu yayi ajiyar zuciya gami da sauke dogon
numfashi sannan yace labari ne mai tsawon
gaske sai dai nayi
iya kokarina na gani ko zan iya gajarce muku
shi...
SADAUKI HULKAS YANA DAGA CIKIN MANYAN
JARUMAN DUNIYA GUDA UKU
wadanda akayi musu lakabi da MAZAN JIYA
jarumai ne wadanda ba a taba yin kamarsu ba
kuma ba za ayi ba
a yanzu da nan gaba domin sun bar abin tarihin
da ba za a taba mancewa dasu ba
sai dai kash
duk su ukun rayuwarsu ta salwanta ne a
tafarkin soyayya
Yanzu dai saiku saurara da kyau kuji wannan
labari domin
akwai dumbin darasi a cikinsa, nan take sarki
AYUBUL HASNU ya shiga basu labari kamar
haka......
.
Hm yanzu ne zamu shiga cikin labarin gadan
gadan
a yayinda zakuji Labarin sadaukin sadaukai
Hulkas mai hular
lamsara
kuma daya daga cikin jaruman duniya Mazan jiya
saboda haka
sai ku gyara zamanku zuwa anjima zanci gaba
da suburbudomuku lbr.

Tsatsuba 1&2Where stories live. Discover now