tsatsuba 1d

272 10 0
                                    

TSATSUBA
LITTAFI NA DAYA 1 PART D
POSTING. #SAS
TYPING. A.A MISAU

Labari ya isowa Guyson cewa..
.
Nan take sarauniya larbisa taji nadama tazo mata
bisa fitowar da tayi neman wannan littafi na
tsatsuba tunda gashi tun ma tafiyar
batayi nisa ba zata rasa rayuwarta, gama aiyana
hakan keda wuya sai wani
daga cikin birirrikan ya shammaceta ya gabza
mata
naushi a haba saboda karfin
dukan sai da tayi sama tamkar an janyeta da
majajjawa
koda shugaban dakarun nata sadauki Humairu ya
hango
shugabarsu a can sama
kuma ya tabbatar da cewa idan ta fado kasa cikin
wadannan
birirrika ta zama gawa sai ya
falfala da gudu
izuwa kan birirrikan yana mai kwalla ihu
Ai kuwa sai birirrikan suka raba hankulansu biyu
ya zamana cewa wasunsu sun daga kawunansu
sama suna jiran sarauniya larbisa ta fado cikinsu
su dasa
mata wawa
wasunsu kuma sai suka ruga izuwa kan sadauki
Humaisu
yayinda ya rage saura yan dakiku kadan larbisa ta
fado
kan birirrikan shi kuma humaisu yayi karo dasu sai
kawai humaisu
da larbisa sukaji an suresu
anyi sama dasu cikin tsananin gudu na ban al
ajabi tamkar
za a taba hadari dasu
kawai sai gani sukayi an diresu a tsakiyar
sansaninsu
nan take Aljani subauratu ya baiyana tsulum a
gabansu yana mai kyalkyala dariya
ya risina ga tsoho huzallatul marwas yace
yanzu na cecesu ya shugabana amma kayi sani
cewa
anan ne kawai zan iya taimakonku amma da zararr
mun kara gaba sai dai ku
ceci kanku
kafin larbisa ko tsoho huzallatul marwas dayansu
yace wani
abu tuni Aljani subauratu ya rikide ya zama
guguwa guguwar ta tafi da tsananin gudu
irin na tauraruwa mai wutsiya ta fada cikin
dandazon birirrikan
kawai sai gani akayi kawunan birirrikan suna
guntulewa suna faduwa kasa
gangar jiki na bingirewa sai dai kaga jini na tsiri da
feshi
daga cikin wuyansu
koda birirrikan suka ga suna ta mutuwa kuma sun
rasa
wanda yake yi musu wannan barna sai suka
haukace suka rinka ruri da kururuwa
suna kaiwa iska duka amma duk a banza domin
dada
ragargazarsu ake yi suna zama gawa tabbas wuya
ba dadi kuma idan kaji
ana cewa ga ki gudu to tabbas sa gudu ne baizo
ba
lokacin da wadannan birirrika sukaga sun kasa
kare kansu
daga sharrin guguwar da ta addabesu sai suka
fara juyawa da baya a guje suna kokarin komawa
inda suka fito amma sai guguwar ta rinka kure
musu
gudu tana ci gaba da cire musu kawuna har saida
ya zamana cewa babu sauran daya daga cikinsu
wanda ya
tsira da rayuwarsa
A wannan lokacine dakarun sarauniya larbisa suka
fara firfitowa daga cikin
wuraren da suka buya cikin alamun kunya
suna masu sunkui da kai kas
cikin fushi sadauki Humaisu ya rufesu da fada
yana
kokarin hukuntasu kawai
sai sarauniya ta tari numfashinsa tana mai
kallonsa cikin murmushi tace kada ka hukunta su
domin
banga laifinsu ba bisa guduwar da sukayi suka
buya
kai kanka ai kasa tarar birirrikan kayi sai da kaga
zan hallaka sannan kayi kundunbala
ka rugo domin ka kawo mini dauki hakika kayi
gagarumar gwaninta wacce
ta burgeni don haka idan mun koma gida zan yi
maka wata gagarumar kyauta wacce
ban taba yiwa wani mahaluki ba
koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube
sadauki
Humaisu ya zube kasa bisa
guowoyinsa a gaban larbisa yana godiya nan dai
larbisa ta bayar da umarnin aje
a kwanta
ba tare da wani bata lokaci ba kuwa kowa yaje ya
kwanta cikin kwanciyar hankali ba tare da fargabar
komai ba.
Al amin Ahmed Misau guyson sunana kenan daga
zauran labarai page
Kashe gari kuwa da sassafe aka kimtsa bayan an
yi kalaci
sai sarauniya larbisa tsoho huzallatul marwas tace
Ljaninka ya gaya mana cewar tafiyar yini biyu da
rabi zamuyi mu
riski dajin da jaruma shumaira take tabbas yanzu
mun shafe tafiyar yini daya kunga kenan saura ta
yini daya jal a gabanmu shin akwai sauran
wani mugun abune da zamu hadu dashi kafin mu
isa
dajin da jaruma shumaira take?
Koda jin wannan tambaya sai tsoho huzallatul
marwas
da sadauki Humaisu suka dubi juna sukayi
shiru
larbisa ta dubi huzallatul marwas cikin fishi tace ai
kai ne
ya kamata ka bani amsar wannan tambaya
huzallatul marwas yayi ajiyar numfashi sannan
yace ya shugabana aini a ganina
yanzu bai kamata kiyi
shakkar wani abu ba tunda dai gashi mun ga
bayan
wadannan mugayen birrirrika saboda nasan cewa
abu ne mawuyaci mu sake haduwa da wani
mugun abu
wanda ya fisu hadari
koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa ta yi
murmushi tace tabbas
kazo da magana mai ma ana yanzu kawai saimuci
gaba da tafiya
ba tare da bata wani lokaci ba kuwa aka hau kan
dawakai bayan an debe komai aka ci gaba da
tafiya ba sassauci
tsoho huzallatul marwas ne akan gaba yana
jagorantar
rundunar, sarauniya larbisa, da sadauki Humaisu
na biye
da shi sannan sauran dakarun, Kamar yadda
Aljani
subauratu ya fada haka Al amarin ya kasance
wato sai da
suka shafe tafiyar rabin yini guda sannan suka iso
wani katon daji mai yalwar
Bishiyoyi, koramai da fadamomi, kai da ganin
wannan
daji kasan cewar dajine mai ni'ima irin wanda
mafarauta ke
so domin dole ne a samu dabobin daji da
tsuntsaye
masu yawa a cikinsa
da shigarsu sai suka hango wani katon garke na
ragon dawa cike da raguna da tinkiyoyi abin
mamaki shine an kewaye garken ne da siraran
itatuwan bishiya marasa kwari
wadanda dabbobin zasu iya kakkaryasu su watsu
amma kuma dabbobin basu ture
itatuwan ba sun gudu
koda dakarun sarauniya larbisa suka hango
garken wannan dabbobi sai suka cika da farin ciki
suka
ruga izuwa cikin garken suka dasawa dabbobin
wawa
da nufin kowa ya kama iya rabonsa
kwatsam ba zato ba tsammani sai sukaji ana
naushinsu
ta sama suna zubewa kasa
duk wanda akayi wa naushi daya sai dai kaga yayi
sama ya fado kasa a matukar galabaice wanda ke
naushin nasu kuwa a samansu
yake shawagi kamar tsuntsu har sai da ya gama
bazar
dasu kasa sannan ya duro kasa bisa kafafunsa
aka
fara kallon kallo tsakaninsa da sarauniya larbisa
ba wani bane yayi wannan gagarumar jarumtakar
ba face jaruma shumaira kai da ganin irin kallon da
sarauniya larbisa ke yiwa jaruma shumaira kai
kasan cewa
tana cikin tsananin mamaki
ba wani abu bane yasata wannan mamaki ba face
a rayuwarta bata taba zaton cewa zata ga
wata ya mace ba mai kyau kamarta ba amma a
yanzu da tayi arba da
shumaira saita raina kanta kuma ta tabbatar da
cewar babu abinda
zata fi shumaira dashi face mulki da dukiya
cikin tsananin fishi shumaira ta dubi su larbisa tace
dame kukazo wannan daji shin yan fashine ku ko
kuwa
matafiyane wadanda basu san ya kamata ba duk
mai
hankali idan ya dubi wadancan dabbobi ya lura da
yadda aka
kebancesu yasan akwai mai su duk da cewa kuwa
a cikin daji suke kuyi sani cewa wannan daji nawa
ne
don haka komai na cikinsa mallakina ne babu
wanda
yake da ikon yin farauta a cikinsa face ni
A cikin wannan daji kakana na bakwai yayi
rayuwarsa
kuma tun daga zamaninsa kawo i yanzu babu
wanda
ya isa ya taba komai a nan sai da izininmu da
yardarmu
ku gaya mini abinda ya shigo daku cikin dajin nan
in ba haka ba kuwa sai dai na yakeku koda
jaruma shumaira tazo nan a zancenta sai larbisa ta
matso
gaba kusa da ita ta sauko daga kan dokinta ta
dubi
shumaira cikin murmushi tace yake shumaira yaga
mafarauci Imshal ki yi sani
cewa nice Sarauniya Larbisa mai mulkin birnin
darul kaizul kuma musamman nazo wannan daji
naki
domin na gana dake bisa wata muhimmiyar bukata
tawa
koda jin wannan batu sai jaruma shumaira ta
gyada kai
cikin alamun fishi da rashin yadda tace mu bama
mu amala da masu mulki kuma baki
da wani abu wanda zaki iya biyana dashi na
taimakeki
saboda haka ina mai
shawartarku daku gaggauta fita daga cikin wannan
daji
nawa idan ba so kuke muyi yaki ba koda gama
fadin hakan
sai jaruma shumaira ta juya da baya ta nufi
wannan
garke na dabbobin ta ta shiga gyara turakan dake
ciki tana daure dabbobin
koda ganin haka sai sarauniya larbisa ta dubi gaba
dayan dakarunta tace duk abinda zai faru
tsakanina da jaruma
shumaira kada ku saka baki ko hannu nan take
larbisa tabi
shumaira izuwa cikin wannan garken dabbobi ta
kama tayata aikin daure dabbobin
Al amarin da ya fusata jaruma shumaira kenan ta
kaiwa
larbisa wawan duka da kafa a wuya, cikin bakin
zafin
nama larbisa ta kaucewa dukan nan fa suka
kaceme da azababben fada suka
wanzu suna masu kaiwa junansu sara da suka
cikin
tsananin zafin nama juriya da bajinta
tun da su jarumi Humaisu suke ganin gumurzu na
fadan
hannu tsakanin jarumai basu taba ganin fada mai
tsananin ban tsoro ba kamar wannan domin
gwanintar ta hadu da gwaninta kuma sadaukantaka
tayi kada da kishiyarta
Sai da wadannan jarumai biyu suka shafe rabin sa
a suna naushi da bugun juna hannu
da kafa ya zamana cewa sun hadawa junansu jini
da majina kuma sun fara galabaita
amma saboda bakar zuciya sunki su daina fadan
amma kuma jaruma shumaira tafi sarauniya larbisa
jure duka domin ita tana iya shanye duka
uku na larbisa amma data naushi larbisa sau daya
sai
kaga ta fadi kasa sai dai tayi hanzari ta mike taci
gaba da fadan
Al amarin da ya dugunzuma hankalin su sadauki
Humaisu kenan domin sun tabbatar da cewa idan
aka ci
gaba da wannan fada a haka har zuwa wani dan
dogon lokaci shumaira zata iya sumar da larbisa
ko
kuma tayi mata wawan rauni Gashi kuma larbisa ta
gargadesu akan kada su
kuskura su shiga cikin wannan fadan
Ana cikin wannan bakin gumurzune shumaira ta
shammaci larbisa
ta daka tsalle sama ta doki fuskarta sau uku da
kafa take larbisa ta dimauce
kuma ta gigice ko da taji zafin dukan saita zare
takobinta ta kaiwa shumaira sara cikin sa a kuwa
ta yanki
shumaira a damtsen hannunta na hagu har wajan
ya dan dare kadan jini ya fito
shumaira tayi tsalle gefe daya tana mai yin yar
kara
bisa jin zafi da zugin da taji koda ta dubi hannun
nata
taga raunin da larbisa tayi mata sai ta fusata ainun Imran_aley
itama
ta zaare rantsatstsiyar takobinta ta ruga izuwa kan
larbisa
itama larbisa saita rugo izuwa kanta
koda ya rage saura baifi taku uku su hadu ba sai
kowacce
ta daka tsalle sama suna masu kai mugun sara
Takubbansu na haduwa saita larbisa ta rabe gida
biyu, A saman shumaira ta doki kirjin larbisa ta
fado
kasa a dimauce kafin larbisa ta mike tsaye
shumaira ta
duro kanta da nufin ta soka mata takobinta a gefen
jikinta......

Tsatsuba 1&2Where stories live. Discover now