TSATSUBA
Littafi Na Biyu (2)
Part F.
.
Lokacin da boka Barwas yazo nan a zancensa
sai sarki shardas ya kamu da tsananin farin ciki
bai san sa adda ya rungume boka barwas ba
yana mai
kyalkyala dariya daga can kuma sai ya janye
jikinsa
daga cikin
nasa suka fuskanci juna ya dubeshi yace
tabbas yanzu na sami nutsuwa da kwanciyar
hankali
saboda haka ka zuba idanu kawai kasha kallo
zaka ga abin da zai biyo baya, koda jin haka
sai boka barwas ya kyalkyale da dariyar farin ciki
yayi ta kyakyatawa kamar ba zai daina ba daga
can kuma
saiya hade fuska tamkar an aiko masa da sakon
mutuwa ya dubi sarki shardas cikin alamun
tsananin
damuwa yace ya shugabana yaya batun
alkawarinmu idan bukata ta biya? Koda jin wannan
tambaya sai sarki shardas ya bushe da dariya
yace
ai alkawarina dakai dutse ne babu abinda zai
kankareshi
face rashin biyan bukatata, daga wannan rana
sarki
shardas ya fara aiki da shawarar boka barwas ya
zamana
cewa ya karbi juna biyun shadila hannu biyu
ya rinka riritata da kyautata mata fiye da kowa
Al'amarin da yayi matukar baiwa shadila mamaki
kenan tun tana ganin abin kamar yaudara ce taga
ashe
zahiri ne kuma gaskiya domin babu abinda
fuskarsa
da zuciyarsa ke nunawa face tsananin soyayya da
kulawa
Abu dai kamar wasa a cikin wata uku kacal
sai gashi shadila ta fara sakin jiki da sarki shardas
duk da cewar ta daukeshi babban makiyin da babu
kamarsa a cikin zuciyarta sai gashi ta fara rayawa
a cikin
zuciyarta cewar ya kamata ta danne wannan gaba
a ranta
ta dauki komai a matsayin kaddarar da ta wuce
nan fa zuciyarta taci gaba da raya mata cewar ya
kamata
ta manta da duk rayuwarta ta baya ta fuskanci
sabuwar rayuwar da take ciki yanzu domin samun
rayuwa ta gari ga abinda take dauke dashi a
cikinta
kamar sarki shardas ya san abindake cikin ranta
watarana shadila na zaune ita kadai a cikin
turakarta
bisa wata doguwar kujera ta alfarma irin ta sarakai
a wannan lokaci tana sanye
da wata doguwar riga fara mai shara shara wacce
ke
nuna tsiraicin jikinta koda ta dubi
cikinta taga ya dan fara
girma sai ta shiga shafa cikin tana murmushi
ba komaine ya sa ta wannan murmushi ba face
tunowa da babban masoyinta wato mahaifin abinda
zata haifa nan take ta shiga tunanin irin abubuwan
da suka faru a baya tsakaninta dashi tun farkon
soyayyarsu kawo izuwa sa adda su sarki shardas
suka kawo harin sumame ga sansaninsu lokacin
da yake gaya mata cewar
kada ta kuskura ta fito daga cikin wannan tanti da
take
ciki
koda tazo dai dai inda taga sarki shardas ya
sareshi da
takobi sai ta kwalla uban ihu, ihun ne sarki
shardas ya jiyo
a lokacin da dama ya nufo turakar tata cikin
firgici da razana sarki shardas ya rugo da gudu
izuwa
cikin turakarta yana shigowa sai yayi turus bisa
ganin cewar babu kowa a cikin turakar face
shadila ita kadai
a zaune hawaye na zuba daki daki a kan
kyawawan
kumatunta
cikin sanyin jiki sarki shardas yaje ya zauna akan
kujerar dake fuskantar wacce shadila ke zaune
ya kama hannayanta biyu ya
rike suka kurawa
juna idanu sannan ya budi baki a cikin murya mai
taushi
da sanyi a lokacin da idanunsa suka ciko da
kwalla
wannan shine karo na farko da shadila taga kwalla
a cikin
idanun sarki shardas tun da aka kawo ta gidan
sarautar
sarki shardas yace ya ke matata na sani cewar a
duniya babu wani mutum wanda kika tsana kuma
kika
daukeshi babban makiyinki sama dani saboda na
kashe miki miji a ranar farko na amarcinku sannan
na rabaki da duk zuri'arki na kawoki kasata da
karfin tsiya inda nayi miki fyade kuma na maishe
dake
matata ta dole
har abada babu abinda zan yi na goge wannan
tabo
nawa akan idanunki ko kuma na burgeki bare
harna
sami gafararki
ki sani cewa ni masoyinki ne na har abada duk
da nasan bakya kaunata dai dai da tsawon dakika
daya
ba zan taba so naga rayuwarki da ta abinda zaki
haifa ta kasance a cikin farin ciki, alfarma daya
nake
so na nema a wajanki ina son ki boye laifin da na
yiwa
mahaifin abin dake cikinki a tsakanina dashi har
izuwa kamar tsawon shekaru bakwai nan gaba a
sannan zaki iya sanar dashi komai idan yana
ganin zai iya daukar
fansa a kaina sai ya dauka , kin san cewar ni ba
zan taba
haihuwa ba face na mallaki Hular lamsara kamar
yadda
na fada miki a baya burina kawai shine na reni dan
mijinki
hailur a matsayin dan cikina, wannan zai kawai
mini da bakin cikin rashin samun da kuma nayi
miki
alkawarin cewar daga nan har izuwa tawon
shekaru
bakwan ba zan taba cutar dashi ba amma fa ki
sani
cewar a ranar da ya cika shekara bakwai zanyi
shiri na bar kasar
nan don tafiya neman hular lamsara
bokana ya tabbatar mini da cewa shima wannan
da naki idan
ya zama saurayi zai tafi neman hular lamsara to a
sannan ne nake
son ki sanar dashi gaskiyar asalinsa da mahaifinsa
domin daga wannan rana mun zama ABOKAN
GABA na sani cewa a wannan lokaci
bana gida don boka barwas ya tabbatar mini da
cewar
sai mun shafe shekara goma sha daya kafin mu
gano inda hular
Lamsara take, kinga a wannan lokaci ban san
kamannin danki ba shima bai san nawa ba don
haka
ko da zamu hadu a wani wurin daban ba zamu
shaida
juna ba zamu iya abokai kuma ko kuma abokan
gaba
idan kuwa na rigashi mallakar hular lamsara tofa
duk inda muka hadu saina gane cewa shine dan
hailur kuma nan take zan kasheshi
Sai kiyi tunani bisa wannan alfarma dana nema a
wajanki
kuma ki tuna cewar
kin taba neman alfarma a wajena kuma nayi miki
tun da kinsa na 'yanta matan zuri arku daga
matsayin
bayi sun koma kuyanginki idan har kikayi mini
wannan alfarma guda daya dana nema a wajanki
babu mamaki ungulu ta Koma gidan ta na tsamiya.
A lokacin da Nikuma Zankoma Inda nafi Wayau
wato Neman na Aure,,,
..
Anan ne Littafin TSATSUBA NA BIYU YAZO
KARSHE
marubucin Littafin yace.
.
SHIN SHADILA ZATA IYA YIWA SARKI
SHARDAS ALFARMAR DA YA NEMA A
WAJANTA?
.
SHIN SU SARAUNIYA LARBISA ZASU SAMI
NASARAR SAMUN ABOKAN TAFIYARSU?
.
WANE IRIN MASIFU DA TASHIN HANKALI
ZASU FUSKANTA KAFIN SU ISA KOGON
KITABUL SIHIR? SHIN SARAUNIYA LARBISA
ZATA CIKA BURINTA NA MALLAKAR LITTAFIN
TSATSUBA
.
DAGA KARSHE SHIN AUWZAB ZAN SAMU
DAMAR GAMA RUBUTO MUKU WANNAN
LITTAFI DUKA ???
.
marubucin yace mu hadu a Littafin TSATSUBA na
Uku (3) Don jin cigaban wannan labari