🌕⚜DA'IMAN⚜🌕
Na MAMUH GEEE
201→202
Cikin tashin hankali yake tuqin fannah kuwa tana riqeda yaron sbd jini daya 'dan 6ata masa fuska har ba'a ganin kamanninsa. Suna isa asibiti aka kar6esa da gaggawa aka shiga emergency dashi. Xama sukayi bakin qofar gurin cikeda damuwa dina jiran suga abinda allah xaiyi. Hankalinsu ne ya qara tashi ganin anshare awanni suna zaune dr 'din ko 'daya daga cikin nurses 'din ba wanda ya fito. Kiran umminsane yashigo wayarsa ya 'daga asanyaye kafin tayi magana ya fada mata halinda suke ciki. Hankalinta yadan tashi tace gatanan xuwa asibitin yayi saurin cewa, No umminah kadaki zo zamuyi handling komai fannah is wit me So pls relax ummi dnt take d trouble of comin hia D boy will b okey insha allah. No my boy hankalina yarigada ya tashi tunda kuna cikin matsala dan haka bazan iya xama ba ganinan tafe kawai. Duk yanda yaso lalla6ata yaqi saurararsa ta kashe wayar. Tana fitowa palon alh xaid shima yana fito yace, Haj ina zaki yanxu haka kuma? My boy ne tsautsayi yasa ya ka'de 'dan wani yaro shinefa sunkaisa asibiti amma har yanxu bai farfado ba Shine zani can asibitin dan nasan yana can cikin damuwa ga wadda yake ciki kafin wannan 'din. Da ita da dad 'din driver yakaisu asibitin Koda suka isa har lokacin ba wani bayani. Taruwa sukayi suka zauna jigum jigum har tsawon lokaci. Dr ne yafito nurses na bayansa ya gaida alh xaid tareda haj nurat kafin ya gyara tsayuwa yana kallon tameer svd muguwar kamat yaron dashi saiyayi tunanin shine mahaifin yaron yace, Well alhmdl yaronka babu wata matsalar data samesa sai bugewa da yayi da firgita data sumar dashi, Munyi masa dressin 'din raunikansa dan haka yana 'dakin hutawa ankaisa nurse zata kaiku sai kudin charges da magani da zaku biya. Ajiyar xuciya suka saki su duka sbd jin ba abinda yasamu yaron mutane. Ummice tace, Angode dr kuma yaron ba dansa bane tsautsayine yasa ya kadesa. Cikeda mamakinsa dabai 6oyuba yace, Haj ina nufin yaron da suka kawofa? Qwarai kuwa dr ba 'dansa bane. Ikon allah amma kuwa kamar harta 6aci dan bantaba ganin kama irin wannanba. Tsabar ya qara tabbatarwa da kansa yace suxo yakaisu gurin yaron. Ahankali suka tura qofar 'dakin dayake Yana kwance agado an 'daura masa 'dan bandage kadan akai Nurse na tsaye tana 'daura masa ruwa. Tana gamawa ta matsa gefe fuskar yaron ta bayyana tsaf a idanunsu. Murza ido fannah, Haj nurat 'dan qyafta idanunta tayi alamar su bude da kyau ta tabbatar da abinda suke gani, Dad kuwa gyara xaman glass 'din adanunsa yayi sbd yagani dakyau. Oga sir tameer kuwa quru yayiwa yaron baimasan me xaice ko xaiyi ba. Atare dukkansu suka isa bakin gadon suna qara yiwa yaron kallon tsoro. Haj nurat batasan sanda tace, My son kaine kana qarami. Dr ganin suma sunga muguwar kamar daya gani yace, Alh kaga ikon allah ko? Kasa magana yayi sai kallon ikon allah dasuke. INASON DNA TEST NA NAWA DA YARON NAN DR. shine abunda tameer yafada idanunsa kafe akan yaron xuciyarsa na bugawa da qarfi. A razane dukkansu suka kalli tameer 'din kafin suka maida kallonsu ga waleed dake kwance sai alokacin suka gano me tameer ke nufi Yana nufin yaron qila dansane,waleed 'dinsu su duka. Jikin kowa mutuwa yayi sbd tsoron me result xai bayar Dad ya dafa tameer cikin taushin murya yace, Son meyasa zakayi haka, tunda kasan ana kama a duniya why not kabari muga nazli nasan duk inda take tana tareda 'danka Bazata ta6a sakacin barinsaba sbd shi jininkane and batada abin so kamarsa.
205→206
NAZLIE A guje su abdul suka shigo gidan suna haki murya na rawa suka tsaya gaban mamarsu dake kicin tana aiki sukace, Mama waleed mota ta ka'desa ya mutu yanata jini kuma turawan sun 'daukesa sun tafi dashi. Sakin kofin hannunta tayi da qarfi cikin tsananin firgici tayi saurin kallonsu xatayi magana amma ganin fitar nazli a guje ko hijab bare 'dan kwali batada ajiki yasa ta fahimci taji abunda su abdull 'din suka fada. Mara mata baya tayi da gudunta itama dan kada ayi biyu dan tasan nazli tsaf indai ta ha'da da abinda ya shafi waleed da ubansa. Gudu take saadah da mijinta na binta tana kaiwa gurin taja ta tsaya sbd ganin jini agurin. Sarewa qafafunta sukayi ta durqushe gaban jinin jinkinta na rawa xuciyarta na wata irin azabar da bata ta6a jiba Tasaka hannunta duka ta shafo jinin a zabure ta miqe kafin suyi wani yunquri ta dafe xuciyarta data buga ta yanke jiki ta fa'di jini na futa ta bakinta. Gigitaccen ihu saadah ta yanka wanda yayi daidai da dawowar me gidansu yana ganin nazli ce a xube qasa a gigice cikin mugun tashin hankali ya fito motar ko kasheta ma beyiba bare rufe qofar yana ganin halinda take ciki cikin ru'du ya tanbayi meya sameta Saadah na kuka ta fada masa sai kawai ya sunkuci nazli 'din yasa mota Saadah tashiga ya fizga suka bar su abdl da babansu tajasu yakoma gida dasu yana namakin yanda duk wani alamarin waleed megidansa hameed ke kula dashi sosai sbd ya hango masifaffen son nazli 'din a tareda hameed 'din. ********* Suna isa asibiti aka kar6eta da gaggawa akayi ciki da ita. Kaida kawo yake cikin tashin hankali. Baisan yanawa yarinyar mugun so hakaba sai yau dayaganta cikin wani hali, Tabbas yana mata mahaukacin so dayakejin zai ita sadaukar da komai akanta, Kuma bayajin ko iyayensa xasu hanasa aurenta dan ta ta6a aure. Kuma yayi alqawarin riqeta da 'danta. Anty saadah kuwa har alokacin sharar hawayen tausayin yanda rayuwa takewa naxli take. Duk yanda sukayi tsammanin abun yawuce nan dan nazli kam babu alamar xata farfado qarshema wani 'daki na musamman aka kaita sbd hameed 'din. Oxygen tub aka 'daura mata sbd taimakawa numfashinta gurin fita. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Bayan kwana uku nazli ba wani motsi ba alamar zata tashi Ga hameed sai hidimar narkar da dukiya yakeyi Duk da anty saadah na cikin tashin hankali bai hanata mamakin hameed 'dinba danko innah dataxo saidata tayi tambaya akansa. ****** Kwana biyu dasukayi a asibitin fadar irin gatan dayake samu bama zai faduba sbd kowa anan yake yini sai dare sosai suke tafiya tameer da fannah ne suka xama dashi. Tuni yasake dasu sbd irin soyayyar dasuke nuna masa sai idan dare yayi yahau yimusu rigimar akaisa gurin antynsa. Sunyi yawo a anguwar dasuka kadesa amma sun rasa gano komai sbd duk sukaje suna cin karo da abu maigadi yaje asibiti dubosu. Haka sukayita yawo ba sa'a tuni tameer ya koma ruwa tsundum dan kuwa damuwa ta dawo masa sabuwa. Xaune yake idanunsa sun ka'da jajir ya tallafe kansa ya qurawa su dad ido dasuka shagala akan waleed sai riritata suke. Nan take idonsa suka tara ruwa sbd nazli 'dinsa takamata ace tana gabansa yana bata wannan gatan. Kamar an mintsilesa ya 'dauki wayarsa 'daya ya nemo number hameed ya danna masa kira. Shigowarsa asibitin kenan kiran tameer yashigo masa ya dauka cikin sanyin murya. Hey friend dan allah kayi hkr ranar kunzo kunsama bananan wlh wife to be 'dinace ba lpia muna asibiti ma haryanxu. Sauke ajiyar zuciya tameer yayi cikin sanyin murya shima yace, Kadaka damu nima ranar ban qarasoba nasamu prblm kuma nima ina asibiti haryanxu. Wane asibiti? Hameed ya tambaya yana rufe mota. NAZMEER SPECIALIST Tameer yafada jiki a sanyaye. Nima muna asibitin yanxu hakama ina parking space shigowata kenan ban isa room dinba. Ok kajira ganinan xuwa. Yana isa gurinsa suka qara jajantawa juna kafin suka 'dunguma zuwa 'dakin da nazli take dan tameer ya duba jikin wife to be 'din aminin nasa..