21

5.9K 483 66
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

Page.21

"Wacece ni? Mike faru dani? Wayyo nikam amaidani gurin Yaddiko da Ya Maheer."
Da sauri na mike zan fita, sake jin karan algaitar yasani zuɓewa a gurin sumammiya.
Kaina sukayo tare da jijjigani, ɗagani Dadda yayi ya kwantar dani akan gadon.
Ya fita da sauri yana isa kofar falo Ya Annur yana shigowa da tare da bak'i tawaga guda.
Har lokacin ba'a fasa busar algaita ba.
Shigowa sukayi dukda a ɗimauce yake bai hanashi cewa.
"Barkanku da zuwa, Annur maza kacewa masu busar nan su daina, Yarinyar nan ta suma, ka kira likita babu lokaci."

Da sauri Ya Annur ya isa garesu tare da dakatar dasu, wayarsa ya ciro yakira likitan.
Dawowa yayi cikin gida da sauri ya nufi ɗakin Mamie. Hankalinshi a tashe, sakani mamie tayi a gaba tana kallona. Zama yayi a gaban gadon tare da kai hannunshi zai riko ni.
"Karka taɓa ta."
" Aka ce mishi" daga bakin kofa, juyawa yayi yana kallon. Su Dadda ne da mahaifinshi mai martaba sarki Umar Muh'd Elkanami tare da limamin maiduguri wanda suka zo raɗa sunan yara, ganin halin da Dadda yake cikine yasa Wanshi kuma sarkin barno yake tambayarshi lafiya mike faruwa.
Shine ya faɗa musu, abinda ya faru dani. Shine lima yace bari ya duba ni, suna shigowa ne Ya Annur yakai hannu zai taɓa ni Liman ya dakatar dashi.
"Kuna da zam zam ne? Ku bani."
Mikewa Mamie tayi zata nufi wardrop ta ɗauko goran zam xam, ta mikawa Dadda.
"Bamai ɗauketa mu fito falo."
D'aukana dadda yayi ya kaini falon.
"Fulani ki zauna a ɗaki." Liman yace mata,
Tunda aka fita dani hankalinta yayi masifar tashi, kamanin Hajja Khadi ne ya shiga mata gizo, dafe goshinta tayi cikin sabon damuwa.
........Tunda aka kwantar dani, liman yasa aka kawo mishi kofi ya zuba ruwan zamzam yayi addu'a sannan ya mikawa Dadda ya umarce shi, yasm shafa min.
Yana gama shafa min. Ko minti ɗaya ba'ayi ba na fasa ihu tare da niman mikewa, rikoni Dadda yayi sosai. Addu'a liman ya cigaba da tofa min yayinda, nake tsalla musu ihu.
"Alkawari akayi damu, karmu sake ta su haɗu. Amma Wancan shaiɗanin Ya kawota wannan kasar, an samu mu nisantata da duk wani abinda ya danganci masarauta, mune muka sanyata take kafiya da ramuwa da son cutar da duk wanda ya zalinceta, karku rabamu da jikinta dan muna tare da itane tun da aka fitar da ita daga cik....."
Watsa min ruwan Liman yayi.
"Wayyo kubar kona mu, komi zakuyi bazamu taɓ'a barinta ba, dan akwai masu bibiyar ahalinta dan sune suka turo mu tayi kuskuren rabuwa da Maheer mun tafi amma kusani kowani cuta da maganinshi shine kawai yake iya cin nasara akanta, kuma bazaku taɓa samun inda yake ba."

Atishawa tare da mika, ia hamma.
"Ikon Allah! Bamai a ina kasamo Mai kama da Hajja Khadi?" liman ya jefa mishi tambaya aikuwa take suka zuba min ido, gyara zama Dadda yayi yace.
"Tashi Ummi Aisha! Ki shiga ciki."
Mikewa nayi a dogon kujeran na nufi cikin gurin Mamie.
Ina barin gurin Dadda ya kalli Annur yace.
"Sai ka faɗa musu inda kuka haɗu."
Nan yayi musu bayani, sannan waziri yace.
"Toh nifa ina ganinta kawai naji jikina ya bani Y'armu ce, dan yanda suke kama da Hajja Khadi ya ɓaci."
"Hmm! Bamai wannan Y'arka ce fa, wallahi kamarsu ta ɓaci. Kuma idan baka manta ba, ai na faɗa maka zata dawo gare ku, amma a kwai dabaibayi a alamarinta. Wanda na faɗa maka shekaru goma sha shida baya."
Shigowar dr Brek ne yasaka suka juya, mika musu hannu yayi suka gaisa. Sannan har Annur zai ce mishi ya koma sai kuma ya mike ya kira ni, tare muka fito.
"Dr kaɗe bi jininta da na Uncle ɗina, kayi musu gwajin ND, ka kawo."
Kallona likitan yayi bayan ya ɗibe jinin, kasa hakuri yayi yace.
"Ke ba kanwar Dr Maheer bane.?"
"A'a ni bansan shi ba." nace mishi a takaice na mike, dan har ya gama ɗiban jininmu,
Ina barin falon Waziri yace mishi.
"Kasanta ne?"
"Eh watanin baya tayi fama da laluran mantuwa, kuma Dr Maheer shi ya kawota. Daga naija, toh watan da ya gabata naji yana nimanta wai ta ɓata, toh kafin ɓatarta naga lokacin da Yake koranta daga gurinshi har nayi mishi magana yace baya kaunar ganinta, daga baya kuma yace yana nimanta kamar zai hauka ce, gashi muma asibitin muna bukatarshi sosai sabida mutum ne nagartacce.."

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now