43

5.9K 428 51
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAK'A WRITER'S ASSO*

Mai_Dambu
   *Watpad:Mai_Dambu*

_Kyauta ga Masoyan Asali_😘💃🏼

     *Allah sarki nakan rasa abin cewa Idan naga sakonku Nagode sosai nida Muwaddatu waRahaman muna muku fatan Alkhairi*

      _Tukwaici gareki Ummin Adnan Allah ya baki lafiya...._

     '''Ina kuma baran Addu'arku Allah yabawa Mijin Auntynmu lafiya👏 Yasa zakkar jikine'''

~Jelata Ubangiji ya kara miki lafiya~
______
  Page.43
D'ago kai yayi cikin tsananin b'acin rai, ya kalli Mamie murmushi bakin ciki yayi mata sannan ya kauda kanshi yace.
"Idan kika kuma taku zuwa inda Mike a bakin aurenki."
Cak ta tsaya jikinta yana kerrrma tace.
      "Abuba...."
         "Kiyi fita min daga gida, idan nazo na same ki a gidan nan toh zan kuwa datse igiyar dake tsakaninmu."
              "Amm..."
    Bai saurareta ba ya dauke no cak zuwa gurin motar da ya kawo Mu, ya kwantar dani cikin sauri ya koma cikin gidan ya d'auko katinshi da wayarshi.
Muka nufi asibiti,
                Tunda muka isa suka karb'a ni Dadda ya fito sai sintiri yake hankalinshi tashe layin BABAN Buhaina yayi yace.
"Ina son kasako shi a jirgi Yau d'in nan, bana son yaja lokaci."
            Yana gama fad'ar haka ya katse kiran jikinshi ba dad'i. Fitowar likitan da ya karb'e ni yasa shi kallonsa cikin sauri yace.
    "Dr Da fatan sai lafiya? Ya jikin nata."
          Gyara zaman glass dinshi yayi sannan yace.
          "Mun samu numfashinta ya daidaita, matsalar shine cikin jikinta yana niman fitane, shine muke kokarin tsayi da shi."
               "Toh me ya haifar da haka Dr." Dadda ya wurga mishi tambayar.
     "Sir babu lokaci amma yanda jininta ya haura tare da b'acin rai yasa cikin ya samu matsala yanzun zan kokarta naga na dakatar da faruwa haka."

Jinjina kai dadda yayi cike da damuwa. Amma a kasan ranshi yana shryawa Mamie abinda zai mata dan dole ta amshi hukuncin laifin da ta aikata.
              ****
   A Sudan kuwa BABAN buhaina da kanshi yaje ya amso Ya Maheer, ya kaishi gidanshi likita ya kira Ya Maheer yace baya bukata magani ya rubuta aka sayo mishi bayan yayi wanka yasha da sannan yaci abinci kwanciya yayi dan jikinshi ciwo yake mishi. Gefe guda mamakin kiyayyar da Mamie take mishi yake tunani. Ai duk wanda sai so jininka kamar kai yaso aiko dan albarkaci zama da tayi dasu zaisa ta kyale su.

     Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace.
     "Zan girmamaki tankar Uwar da ta haife ni sabida ina Auren gudar jininki Mamie, ga rabon da ya shiga tsakaninmu da wani ne yayi min haka toh da duniya tasan da abinda yayi min."
      Haka yayi ta tunani har barci yayi gaba da shi,
          .....Washi gari da safe ya tashi garau, nan Baban Buhaina ke sanar mishi da sakon Dadda yana jin haka yasan ba lafiya.
        Cikin gaggawa ya gama shiryawa ya nufi airport.
                 ****
A yau gidan yaddiko suka tashi da jimamin mutuwar hajiya Sadika, mutuwar da tayi shi a wulakance kamar mara galihu, dakyar Mamah tasa Sailuba da Fauzan. Tare da hafsat suka mata wanka ita mamah ce ta jagoranci wankar.
        Bayan sun gama mata suka kira yaddiko tayi mata addu'a sai a lokacin ta samu damar fashewa da kuka, babu wanda ya hanata.
                         Haka maza suka zo aka fitar da gawarta dan a sallaceta.
                 Kuka sosai sailuba take tare da cin alwashin ko zatayi yawo tsirara bazata taɓa barina zama da Ya Maheer ba boka ba malam sai tayi sanadin da muka rabu.
                 Babu abinda ke da kuma ɗ'aga mata hankali kamar tafiyar Ya Maheer babu aike babu waya dukda su Abba suna tsaye akantasu amma ai ya dace ya nimeta. Dan haka ta kulle shi a ranta dole ta kwaci kanta kafin lokaci ya kure mata.
              Ana addu'ar uku mutane suka watse. Yan kananun kanenta suka dawo gaban yaddiko da zama tunda dama can gidan mamarsu ce a ciki.
               ****
    Dadda da kanshi ya a airport bai kaishi ko ina ba sai asibiti ina kwance zama yayi a gabana tare da riko hannuna.
    "Me yasa kike karaya da rayuwa da zaran kin rasa abu sai cire tsamani da cigaba, bana son mace me yawan karaya, so samu ki zama jaruma kamar Mamie yanda zaki ji daɗin sarafani yanda ranki yake so amma ba wai ki kwanta kina rai kwai kwai mutu kwai kwai.
           A hankali na bud'e idanuna, gira ya d'aga min.
    "Yes! Kina nan kwance ai bai dace ba, da wani abu yasami cikina kice min nayi haƙuri ko? Toh gwara ki tashi dan har yanzun da sauranki kamar ke ciwon zuciya na shirin kasara ki, da zaran kika na kasa wani auren zan kuma yawa."
        Bansan lokacin da na zaro pillown da nake kai ba na wurga mishi, shigowar Dadda kenan ya maheer ya kwace pillow ta kwali masa, murmushi yayi cikin dattako ya juya bai ce mana kome ba,
    Kallona ya Maheer yayi cikin jin kunya yace.
    "Nima Insha Allah haka zan zama adalin Uba ga duk yarana na ɗauk.."
           "Ji min yara nawa zaka haifa ne kake zaƙewa haka."
        Taɓe bakinshi yayi sannan ya d'aga min kafaɗ'ar shi, yatsina fuska yayi sannan yace.
   "Like 12!"
      "Kutt amma ba dai niba ko? Sai dai matar ka ta zazzaga maka goma ni na rakata da biyu sha biyu sai kace Uwar garke." na faɗa mishi tare da murguɗa mishi bakina.
              Wani kauda kai yayi yana taɓe bakinshi tare da ɓata fuskarshi yace.
  "Hummm, duk sha biyun nake son ki dire min su."
       Cike da jin haushi nace.
"Allah bazan iya ba, biyu sun wadatar idan basu maka ba toh ka san yanda zakayi dani."
         "Oo babu yanda zanyi dake aurene dai babu wacce zata hanani yinshi, komen kishinta kuwa. Dan sai na kar."

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now