Part 1

799 23 1
                                    

*🦅🦅🦅🦅🦅🦅ABUNDA ZUCIYA KE SO*
_(What the hart want)_
🦅🦅🦅🦅🦅🦅

*✍🏻ALQALAM WARITERS ASSOCIATION*

*Game son karantawa 200 KACAL👌🏻kota card katura zuwa 07014197556 ko Acct no: 0422555659 GTbank Fadila Lamido sainai adding dinka agroup din da zan fara posting*

         *Page 1*

_"Mamy wannan guy din yasa min ido, kulum idoshi akaina, zan fara fada dashi"_

   _"Wai dan gidan waye ne Baby?, nifa bana son, nagaji fah"_

   _"Mamy ban sani ba nima, amman nan cikin area nan nake ganin shi"_

   _" 'Dan gidan waye ne?, waye baban shi?_

   _"Ban sani ba Mamy, ni dai ganin sa nake"_

   _"Wanne gidan kike ganin yana shiga?_

    _"A hanya kadai muke haduwa"_

   _"Shiru dattijuwar tayi zuwa can tace"_

   _"Kisa ido kika wane gida yake shiga daga yau"_

    _"Jinjina kai tayi sannan ta nufa bedroom  dinta"_

     _"Wanka kawai tayi sannan ta fara rubuce rubuce kamar yadda ta saba, misalin 12:30am tai shirin zuwa makaranta"_

    _"Kishingide ta samu Mamy, Mamy zan wuce"_

    _"A'a Baby daman kina da lecture ne? gashi kuma na aiki driver yanzun nan"_

   _"Ba komai Mamy barin je kawai kice masa 4 yazo ya dauke ni"_
 
   _OK Baby Allah ya tsare"_

    ********************

    _"Tana fitowa gidan gaban ta taji yana faduwa, jikinta ne ya soma rawa, dan duk sanda ta fito da kafarta saita hadu dashi, ganin babu kowa cikin unguwaar yasa ta sake jikin ta, tako take irin na matashiyar budurwar dakeji da kanta, cikin riga da siket na atamfa tare da d'an gyaleta karami sai purse dake rike ahannunta tare da tarin takarddu"_

     _"Tsakanin su da titi akwai nisa ba laifi, kuma gashi bata iya sauri ba taku take dai-dai kamar bata son taka kasa kanta akasa"_

    _"Mashin ta hango yana tahowa kiran Frajend, dan haka tai saurin dagowa ta kalli gurin, shine, ta fada cikin zuciyarta dan haka ta fara matsawa gefen hanya"_

    _"Guy din tun daga nesa yake sakin murmushi, ta gefen ido take kallon sa, wani irin chain ta hango makale awuyansa yana shining, dan haka ta juyo ta kalkesa ba tare data shirya ba"_

    _"Chain d'i dai tagani  awuyan sa, tana matukar shining, hankalin ta ne yakai kan kafafun sa, nan ma chain di ta sake gani daure a dukkan kafafun biyu, mamaki be gama sakinta ba taji an fincike gyalen ta, sai wucewan shi ta gani"_

   _Juyawa tayi da saurin tana kallon yadda gyalenta ke lilo ahannun sa, kasancewan gyalen baki yabata damar gane fari ne kwala, dan bawani kayan kirki bane ajikin shi, rigar jikinsa bata da hannu hakanan wadon sa daga kadan ya wuce guiwa, gashin kansa ne taga yana neman yafi gyalen baki anan nade uwa irin na turawa"_

     _Kulewa cikin layin yayi ganin bashi da niyar tsayawa yasa zuciya yanzo mata har wuya"_

      _"Daga can ta hango ya saki mayafin yayin da iska ta kasoshi tsakiyar hanya, shiko ko waigenta beyi ba"_

    _"Cikin fushi ta nufi gida, da karfi ta tura Gate din gidan ta shige"_

   _"Mamy na zaune inda ta barta nan ta fara kokarin wuce ta tana haki wani na kokar wani"_

    _"A'a Baby baki wuce ba? ina mayafin ki?"_

     _"Kasa mgn baby tayi dan haka mahaifiyarta ta mike ta karaso gare ta, zama tayi kusa da ita sannan ta kwatar da ita jikinta ta zame dan kwalinta tana shafa kwantancen gashin kanta take fadin..."_

     _"Waya tabamin ke ne haka?, haba baby bar fushi haka, karya kawo miki matsala, bansan ki da fushi haka ba"_

    _"Ba tace komai ba, mamy ma bata sake cewa komai ba tsayon wani lokaci, saida ta tabbatar diyar tata ta nutsu sosai"_ sanan  tace,

     _"Yasmeen! waya bata miki rai?"_

   _"Mamy wannan Guy din da nake gaya miki ne ya finceke min mayafi ya tafi dashi"_

        _"😳 Baby wai dan gidan uban waye ne cikin area nan?"_

    _" Shiru Tayi dan haka itama Mammy tai shiru"_

    _"Misalin 5:13pm taji shigowan mota dan haka ta zabura, har gaban motar ta isa adadai lokacin da wani kyakyawan magidanci ke fitowa"_

   _" Wayoyinsa ta amsa tare da shigewa jikin sa"_

   _" Murmushi yayi yana kara tarota yake fadin ya karatu"_

    _"Abbba na yau banje ba"_

   _"Cikin ido ya kalketa meya hanaki?_

     _"Abbba na wannan Guy din da nake baka lbr yauma mayafi ya fincike min ya tafi dashi"_

     _"Wai waye wannan ne???"_

   _"Wani ne fari sosai, Abba yana da Chain a wuyansa da kafafun sa, baya saka kayan kirki jikin sa"_

    _"Oh🤦🏻‍♂ Yasmeen ban gane wannan kwatancen naki ba namiji kuma da chain a kafa? kinsan sunan sa???_

     _"A'a, amman dai Abba yana da fari sosai"_

    _Shiru yayi zuwa can ya kama hannun ta yana dan matsawa yake fadin"_

     _Toh ko dan gidan *Captain Habib* ne?, shima naga yaransa farare ne, wacce mota yake hawa????_

     _"Abba wannan da kafarsa nake ganin sa, yau daya ne na ganshi da Frajend"_

     _Oh🤦🏻‍♂Yasmeen nan area din babu yaron d'ake hawa frajend, sai dai idan shigowa yake yi, zan so insan dan gidan wanene wannan yaron......._

      
         *Fadeela Lamido*

ABUNDA ZUCIYA KE SOWhere stories live. Discover now