chapter 6

598 53 1
                                    

#duk asanadin soyaya#
💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦
💦💦by💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦SAFNAH ALIYU JAWABI 💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦

Cikin nasara raihan yafara zuwa makaranta, yaune ranar sata farko dan haka cikin sauri yake gudanar da shirinsa,saida ya gama tsaf sannan yayiwa Inna sadiya sallama, addu'ar samun nasara tayi masa sannan ya fice.

Yana fita yaci karo da labiba tana labe akofar gidan,murmushi suka sakarwa juna cike da tsansar kauna,kallon sa tayi tace ina kwana ya raihan "

"Lafiya kalau yakike ?

"Lafiya kalau nake ,dama zuwa nayi na ganka kafin katafi.

,"aikuwa kin kyauta .

Salama sukayi kowa ya kama gabansa.raihan yana shiga cikin makarantar sauke ajiyar zuciya yayi yace, "Alhamdullah yaudai ALLAH yacika min burina na farko arayuwa ta.

Gindin bishiya yasamu ya sauna kasancewar lokacin lecture dinsu baiyi ba, yana zaune yaji anyi masa sallama,amsawa yayi da mamaki afuskar sa,murmushi sadiq yayi yace, "sunana sadiq yaune ranata tafarko acikin makarantar nan,koma daga yanayin dana ganka nasan kaima haka?

Murmushi raihan yayi yace," haka ne.

Tun daga ranar abota Mai karfi yashiga tsakanin Raihan da sadiq, tun raihan yana ďan basarwa harya ware,ganin yanda sadiq yake da natsuwa da rikon addini .

Labarin labiba sosai sadiq ke Shanta gun raihan tun yana jin daďin ta harya koma yana jin haushi,daga zarar raihan ya fara tuni sadiq zaisan hanyar da zaibi dan ganin An canza akalar zancan.

Wata rana bayan sun fito daga lecture raihan yace, "gaskiya sadiq bakada kirki kullum Nike zaryan zuwa gidan ku,amma Kai shiru.

Murmushi sadiq yayi yace,"to naji tunda yanzun mun gama sai muji ai.

Murmushin jin daďi raihan yayi sannan suka nufi gidan nasu.

Bayan sun gaisa da iyayan sa suka nufi gidan su labiba, cike da zumuďin ganin hasken idaniyan ta tafito tsaf da ita.

Aikuwa tana fitowa suka haďa ido, kasa ďauke idanuwansa daga kanta Sadiq yayi dan gabaki ďaya ta tafi da duk kannin imanin sa.

Gaishe shi take amma gabaki ďaya baimasan tanayi ba,cike da mamaki raihan yaďan dungure shi yana tambayar sa,murmushi yayi haďe da Sosa Kai yace, "hmm kaidai bari,gaisawa sukayi cikin girmama.

Hira suka shigayi saidai Sam sadiq hankalinsa Baya gurin asalima idan za'atambaye shi abinda suke cewa tofa baisan abinda zaice ba, ganin tunanin ta naneman dagula masa lilsafi yasa yace,"raihan zan tafi gida.

Da murmushi ta kalle shi tace, "haba ya sadiq tun yanzu zaka tafi,komawa yayi ya zauna yace, "yanda kikace kanwata.

Dariya duk kansu sukayi ganin yanda ya koma ya zauna babu musu.

Lokacin da sadiq ya koma gida gabaki ďaya kasa sukuni yayi, duk lokacin daya ratsa idanuwan sa ita kawai yake gani tana mishi wannan murmushin nata Mai narkar da zuciyar da akayi domin ta.

DUK A SANADIN SOYAYAWhere stories live. Discover now