MUGUN ZALUNCI 67-68

286 14 0
                                    

😡 *MUGUN ZALUNCI* 😡

📝 *Ummu Asma'u Sa'adatu*

*Nah sadaukar da wanan littafin ga duk Matan dake fuskantar matsalar aure Allah ya kawo masu sauk'i*

*Bismillahirahamanirrahim*

*Page* 67⚜68

Duk k'okarin scopion ya samu Hajiya Batula ya kasa samunta yaje gidanta, maigadin yace tana asibiti ta samu hatsari, yaje gidan Abubakar yafi sau biyu bai samu ganin sa ba, da safe Scopion yayi sammako zaije gidan Abubakar tafe yake yana sak'a yanda zai fa'di masa yasan Abubakar ba zai k'yale sa ba, gara duk abun da zai masa yayi, yafi masa saukin wanan bala'in da yake ciki.

Tafiya yake yi yana tunanin, wata bak'ar mota ke ta yi masa hon, gudu sosai driven motar yake yi, scopion duk hon din da mutun keyi baji ba, yayi yayi control din mota ya kasa yana on speed sosai, kwashe Scopion yayi ganin scopion ya fa'di kwance ya gudu abun sa, bai tsaya ba.

Scopion kwance cikin jinin, hanyar ba mutane, cen wasu sunzo wucewa suka gansa kwance, taimaka masa sukayi suka kira yan sanda aka wuce dashi asibiti, ya samu kariya a k'afa, Scopion sai kuka Kaye yi yana tunanin ina zai ga Abubakar ko Ruk'ayyatu, ga wani irin azaba dayake ji a k'afar asibiti sai wulak'ancin suke masa babu maijinyar sa, bayada kudi, kudi ko ya samu kashewa akeyi ta hanyar banza a samu a banza a kashe a banza.

Lokacin da aka fito da su Mumy Mimi kuka take yi kamar ranta zai fita, Mumy duk an yanke kafafu biyu, Daddy ma kuka yakeyi sosai, Hajiya Batula likitocin sun bada shawara akai ta asibitin mahaukata,zasu fi kula da ita sosai.

Mumy sai da aka yini ta farfado, ta motsa k'afafun ta duk taji su a daure, lokacin da ta fahimci abun dake faruwa kuka tayi sosai, Daddy na gefe yana bata magana, Mimi duk yan uwan Mumy wanda ta kira yazo suyi jiniyar Mumy sai yace yanada uziri, Mumy bata hul'da da wanda bayada hali, yan uwanta da dama bata hul'da da su, sai masu kudi, masu kudin basada lokacin jiniyar ta.

Mimi sosai ta shiga damuwa, komai sai anyiwa Mumy, su biyu ne yaran Mumy,ita da Abdul kaninta, Abdul ko yaushe a bige yake ya mayarda k'waya kamar abinci, Mumy tayi yawon Malaimai duk a banza.

Mimi damuwa tayi mata yawa, Abubakar tun da aka fito dasu Mumy ya wuce abun sa, yacewa Mimi baya jin da'di, kwanan duk tsatsaye yake sai yayi ta jin fever, Mimi da yammah ta kira yarinyar dake mata aiki tana tambayar su Nur, tace sun fita da Sunday tun da aka dauko su da makaranta, yace zai kai su Park.

Daddare Mimi ta kira Abubakar yace baya gida, takira num Sunday a kashe, ta sake kiran Merry ko su Nur sun dawo Merry tace basu dawo,gidan Mumy ta kira aka ce basu zo ba, hankalin Mimi ya tashi sosai, ta kira Abubakar yayi ta kira num Sunday a kashe.

Mimi nurse din ta rok'a su kullar mata da Mumy ta wuce gida, Dady ta kira hankalin su yayi mungun tashi, har dare yayi ba labarin Sunday da yaran Mimi, Abubakar duk inda yake tunanin zaa same su basa cen, matar da ta ha'da su da sunday suka je gidanta, ta fa'da masu tafi shekara bata ga Sunday ba, batasan garin su ba.

A Abuja suka hadu, Mimi kuka sosai, Abubakar ma hankalin sa yayi mugun tashi wane hali yaransa suke ciki, sun fa'dawa yan sanda, Abubakar kudi sosai ya basu ko labarin Sunday babu, wani dansanda yacewa Abubakar sunyi kure na amincewa mutunin da basu San shi ma, basu San garin sa ba, Mimi har dare yawo suke yi ba labari, asibiti ta koma gurin Mumy kuka takeyi cike da tashin hankali, cen cikin dare zazzafi mai zafi ya rufe ta, ta fara amai ga gudawa da takeyi.

Bata iya kula da Mumy, Dady yazo da cikin yan aikin su kula da Mumy, Mimi ma gado aka bata, gwaji aka fara yi mata, likitan ya rubuta mata general check up.

Abubakar ranar baiyi bacci ba damuwa tayi masa yawa, ina Sunday ya kai masa yara, kwana yayi yana rok'on Allah ya bayana masa yaransa.

**** *****

Umman su Dr ta kira Baffa, tana rok'on su hada Zuri'a tsakanin su hankalinta ya kwanta da Ruk'ayyatu, Baffa yace bayada matsala in Ruk'ayyatu da Ibrahim din sun amince, Ibrahim mutum ne wanda kowa zai zo ha'da zuri'a da shi, sosai Baffa yaji da'di.

Mahaifiyar Najib Mijin Maimuna sosai hankalinta ya tashi K'anin Najib biyu aka tsada ma Miji duk maganar ta watse, ba wanda ya k'ara zuwa yace yana son su, abun duniya ya taru yayi mata yawa, Najib ma tun da ta sanya ya saki Maimuna baya zuwa sai yaga dama, sosai ta shiga damuwa me ke faruwa haka?.

Ruk'ayyatu lokacin da Baffa ya fa'da mata kiran sa da Umman Dr tayi, Ruk'ayyatu tace bazata iya auren Dr ba, abokin Abubakar ne, Baffa yace bazai mata dole ba duk abun da takeso, Adda Saudi tace bataga aibun auren Dr, in Abubakar din nasonki bazai sake ki ba.

Ruk'ayyatu tashi tayi ta wuce a ranta tace bazata auri Dr Ibrahim ba.

*Ummu Asma'u Sa'adatu*

*08182654508*

MUGUN ZALUNCIWhere stories live. Discover now