MUGUN ZALUNCI 21-22

329 18 0
                                    

😡 *MUGUN ZALUNCI* 😡

📝 *Ummu Asma'u (Sa'adatu*)

*Nah sadaukar da wanan littafin ga duk Matan dake fuskantar matsalar aure Allah ya kawo masu sauk'i*

*Bismillahirahamanirrahim*

*Page* 21⚜22

Dr Ibrahim har suka isa Abuja tunanin yake yi yanda zai taimaki Ruk'ayyatu, karshe ya yanke shawaran zai rik'a yi mata aike ta hannun Faruk.

Bayan an k'are sadakar ukku su Inna suka koma Dukku, Gwaggon su Lami'do ta rok'i Baffa ya bar Ruk'ayyatu wajen su har ta k'are wanka, ganin su zai rage mata damuwar da take ciki.

A nan Bajoga suka bar Ruk'ayyatu da Zara, Zara sai wasanta takeyi batasan mi ke faruwa ba, Faruk sosai yake kula da su Ruk'ayyatu da Zara sai da akayi bakwai su Faruk din suka wuce Gombe, lokacin cikin Zainab ya girma.

Ruk'ayyatu ta rame ta Kode sosai, damuwa sosai tashi ga, Gwaggo tayi fa'da har ta gaji, wani lokacin in tanawa Ruk'ayyatu fa'da, in Ruk'ayyatu ta fara kuka sai Gwaggo ta fara kuka, Inna Rabi tayi ta yiwa Gwaggo fa'da.

Ranar da Faruk ya turo kayan su Ruk'ayyatu dake Gombe, Ruk'ayyatu kuka tayi sosai, Gwaggo da Inna Rabi ma kuka sukeyi, Zara tazo kan jikin Ruk'ayyatu ta kwana tana kuka, Ruk'ayyatu ranar da zazafi ta kwana

**** ****

A Dukku Innar su Ruk'ayyatu ta shiga damuwa, ga Adda Saudi gaban su da yara biyar , ba wani cikin dangin Mahaifin su dake basu taimako, cen lokacin da mijin Saudin nada rai shine mai rufin asiri a zuri'ar su, dan gadon da ya bari ba wani abun azo a gani ne ba.

Mahaifiyarsa nada rai da aka raba gadon aka ba Saudi da yaranta nata, Inna tace Saudin ta fara sani'a, ta fara kawo atamfofi, sai a dauka bashi wasu kudin su fito wasu su lak'e, haka suke ta fama, Alhaji Jibbo da Baffa ke gadi gidan gonar sa, abun yayi sanyi sosai, ga ciwon sugar ta shige sa.

Inna kanta ta rame kullun cikin tunani take, Baffa boye damuwarsa yake yi kar Inna ta gane, shima abun nadamun sa a zuciyar sa.

Maimuna ta k'are Jarrabawar SSCE cike da nasara, Inna sai murna takeyi, tasha fa'dawa Maimuna ta maida hankali sosai tayi karatu, duk da karatun tana jijina yanda zata kasance ga lalori sunyi yawa sosai.

Bayan wattani hudu, Ruk'ayyatu ta kammalla takabar ta, an raba gado tsakanin Gwaggo Zara da Ruk'ayyatu da Zainab, Zainab ta shigo cikin gado kasancewar Lami'do bayada yaro Namiji.

Motar sace sai kayansa na sawa dawasu tarkace, gidan Mahaifin su, shine su Inna suke ciki, kudin da aka saida motar ne su Ruk'ayyatu suka dan samu, Faruk yazo zasu maida Ruk'ayyatu Dukku, ranar Ruk'ayyatu tayi kuka sosai, ta tuna ranar da aka kawota Bajoga, ashe zaman bamai jimawa ne ba.

Koda suka isa Dukku duk fuskar ta ta kumbura, Inna hankalinta ya k'ara tashi ganin yanda Ruk'ayyatu ta rame, farinta ya k'ara fitowa sosai sai dogon hanci take saki.

Su Faruk basu Jima suka wuce, ko ka'dan baya son ganin Ruk'ayyatu cikin wanan hali Faruk din ma sai da ya zubar da hawaye, a nan dakin da Saudi take Ruk'ayyatu ta ajiye kayanta, dakin ya yi masu karanta.

Bayan sallar isha'e Baffa ya kira Ruk'ayyatu nasiha sosai yayi mata, yace Lami'do baya buk'atar komai a yanzu sai addu'ar ta, damuwar ta bazata maida shi ba, Inna shiru tayi batason abun da zai k'ara damuwar Ruk'ayyatu, in son samune tafi son Ruk'ayyatu ta koma makaranta.

Ruk'ayyatu kudin da aka bata tabawa Baffa, da zaayi rabon gadon Gwaggo ta kira sa yazo, yace a raba, ba komai basai yazo ba, Baffa yace taba Inna ta ajiye zai diba yanda zaa yi, Baffa kansa ga lokacin ya yarda Ruk'ayyatu ta koma makaranta, sai dai abunda ya Fahimta Ruk'ayyatu bata son karatun, ko bazata iya karatun ne ba.

Ruk'ayyatu boyar Allah ko yaushe cikin sallar dare take tana rok'awa Lami'do gaffar ubangiji, tayi sallah tayi Azumi, su Inna tun suna fa'dan damuwar da tasawa kanta har sun gaji sun zuba mata Ido.

Ruk'ayyatu tayi kuka har saman idanunta ya fara bak'i, ko yaushe cikin mafalkin Lami'do take, zaman ta da Lami'do ya nuna mata gata sosai, Lami'do bawan Allah ne, akwai tauhidi sosai a zuciyarsa, komai zaiyi yana koyi da Sunnah Manzo Allah (SAW).

Ruk'ayyatu na zaune dakin su, Inna ta shigo cikin dakin, Inna zama tayi suna tafa fira da Ruk'ayyatu, cen cikin fira Inna tacewa Ruk'ayyatu da zaki koma makaranta Ruk'ayyatu kamar zaifi zaman nan dakike yi, zakiji sauk'in damuwa da rashin Lami'do, Ruk'ayyatu tayi shiru batace komai ba.

Inna fita dakin tayi damuwa sosai a ranta, da yammah Inna ta shirya, tacewa Baffa zataje unguwa, gidan Malama Balkisu ta tafi, Malama Balkisu makarantar su Ruk'ayyatu take koyarwa, zaman su Unguwa daya suke hul'da da Inna, wani lokacin Inna na bata sako ta kaiwa su Ruk'ayyatu.

Malama Balkisu ta tarbi Inna suka gaisa da tambayar Ruk'ayyatu lokacin da Lami'do ya rasu har Bajoga taje masu gaisuwa, bayan sun gaisa Inna tace tazo ne tana son tayiwa Ruk'ayyatu magana da nuna mata muhimmaci karatun ko zata yarda ta koma Makaranta.

Malama Balkisu tayi shiru tana sauraren Inna, bayan Inna takai aya, Malama Balkisu tayiwa Inna bayanin kowane mutun duniya da irin yanda Allah yayi sa, Ruk'ayyatu nadaga cikin mutanen basa gane karatu gaskiya kodon batada ra'ayin karatun ne? ko kok'arin yin karatun ne batada, Ruk'ayyatu bazata iya karatu ba, tayi zama Malamar ajin su tasan abun da Ruk'ayyatu zata iya a Makaranta.

Shawara da zata basu su bari ta koma Islamiya tanada illimin addinin, sai ta k'ara, ta nemi wata sani'a ta rik'a yi, zaifi, Inna tayi shiru Lami'do ta tuno, maganar karshe da sukayi kan karatun Ruk'ayyatu cewa yayi Inna ta bar maganar karatun, zata samu kasuwanci da zatayi.

Ko shima ya fahimci Ruk'ayyatu bazata iya yin karatun ne ba? Inna tayiwa Malama Balkisu godiya ta koma gida, Zuciyar cike da tunanin iri-iri sosai take tausayin Ruk'ayyatu.

**** ******

Abubukar yaje Maiduguri gidan su Munnawara, Mahaifin ta ya amince Abubakar ya turo magabatansa, bayan ya koma Abuja da kwana biyu, yayansa da k'ananen Mahaifin su, sukaje tambayar aure an basu su, sunkai dukiyar aure ansa biki sati biyu masu zuwa.

Duk hidimar da akeyi Mimi bata sani ba har aka kai lefe,sai saura sati daya biki Abubakar ya fa'da mata, kuka tasa tace yaci amanar ta, a dare ta tattara kayanta da yaranta tayi gidan Mummy.

Mummy sosai hankalin ta ya tashi tasha alwashi sai bayan ranta zaayi auren, Dadyn su Mimi ma yaji haushi yanda Abubakar yak'i fa'dawa Mimi har sai saura sati daya biki, Mummy da Mimi da wata k'awar Mumy tun da safe sukayi sammakon zuwa Bargu cen cikin Niger state wajen wani hatsabibin Boka sukaje.

Kudi sosai suka zuba yayi masu aiki, ya basu wasu layu da rubutun yace su zuba a kogi haka maganar auren zata bi ruwa, ya buga masu k'asa hoton Munnawara ya fito ya kira sunenta sau ukku yace suje zasu ji labarin haukar ta.

Abubukar yace su jira zaizo jiki na rawa ya maida Mimi, sai dai yaga wani bak'in Abu mai girma ya rufe Abubakar nan gaba ya kasa gane ko miye shi, Mumy tace a dai kashe wannan gaban zasu dawo.

Sai dare suka shiga Abuja, a k'ofar gida suka samu Abubakar yana jiran su, yana ganin Mimi ya zube k'asa yana rok'on ta yafe masa tazo suje gida, Mimi ko kallon sa batayi ba ta wuce ciki, wajen Mumy yaje yana rok'onta, wulak'ance taje yaje gobe ya dawo.

Abubakar godiya sosai yayi ya wuce, yana hanya Umman su Munnawara ta kira sa tana fa'da masa Munnawara ba lafiya kashe wayar yayi gaba daya ko sunan Munnawara baya son ji.

Abunda ya faru ga Munnawara tana bacci taji ana kiran sunenta falkawar da zatayi taga wani bak'in Abu kamar dabba kamar mutun kuwar da tayi shine haukar ta, hauka sosai sai da aka daure ta.

Muje Zuwa

*Ummu Asma'u Sa'adatu*

*08182654508*

MUGUN ZALUNCIWhere stories live. Discover now