🙆🙆 HABIBULLAH 🙆🙆

11.9K 250 6
                                    

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers_)


    🙆🏻‍♂🙆🏻‍♂ *HABIBULLAH* 🙆🏻‍♂🙆🏻‍♂

  Writing
              And
                    Story

*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
® *FAUZAH*

*BISMILLAHIR RAHAMANIIR RAHIIM*

*GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI DAYA DAWO DANI ONLINE BAYAN HUTUN DOGON LKC DANA TAFI*

*TABBAS RAYUWAR DUNIYA CIKE TAKE DA ABUBUWAN MAMAKI HAQIQA NAYI MAMAKIN IRIN TARIN MASOYAN DANA SAMU TA SANADIN RUBUTUN NOVELS BANSAN IRIN GODIYAR DA ZANYI MUKU BA,  MASU KIRANA A WAYA BASA SAMUNA DAMA WADANDA SUKE CIGIYATA INA GODIYA DA KULAWARKU GARENI KUMA NASAN NAYI KEWANKU FIYE DA SOSAI*

*KUMA MUNA TARE FOR EVER INSHA ALLAH NA GODE! NA GODE!! NA GODE!!! ALLAH YA BAR KAUNA.*


*GODIYA DA JINJINA TA BAZATA DAI NA WANZUWA GAREKU BA HAZIQAI KUMA JARUMAN MARUBUTA MASUYI  DOMIN ALLAH KUMA DOMIN KAWO GYARA DA KUMA SANYA AL'UMMAH CIKIN NISHADI ,MARUBUTAN BRILLIANT WRITE ASSO.*
*ALLAH YA QARA HADE KANMU DA BAMU ZAMAN LAFIYA ME DOREWA HADI DA QARUWAR FAHIMTAR JUNA*.🙏🏻🙏🏻



🅿1


             Katafaran gidane wanda da gani babu tambaya kasan naira ta samu mazauni  a gdan tabbas a tashin farko zuciyarka zata raya maka cewa samun kwanciyar hankali yafi komai sauki a cikin wannan aljannar duniya da idanunka yake hange.

    Nima abinda kukeji a ranku shi naji a raina saboda haka tsegumi na ya bani qarfin gwiwar kutsawa cikin gdan ta wata madaidaiciyar qofa da naga wani mutum ya bude ya fito alamunsa kadai sun isa su sanar dakai bazai wucce matsayin megadi  ba yanayin firgicin da yake cikine yasa bai iya dakatar dani daga shiga gdanba.

   Da sauri na shiga tare da nufar hanyar da nake tunanin itace zata sadani da cikin gdan ilai kuwa ita dince saboda ihu da na rinqa jiyowa sama2 sauri na qara domin isa inda nakejin muryar tana magana cikin kuka tana cewa.

“Innanillahi wa'innah ilaihirraji'un jama'a mun shiga uku yauma abinda ya dade yana faruwa a gdan HABIBULLAH ya sake faruwa amaryar da aka kawo kwanaki ashirin da bakwai ta rasu wayyoh mukan munga takanmu....." Ban taya ida jin abinda mai kwarmaton take furtawa ba na kutsa kai cikin wata qofar alfarma wadda iyakar tunanina ya bani dutsan diamond ne da nakeji ana fada a hikayoyi.

   Parlourn cike yake da mutane maza da mata wadanda da ganin fuskokinsu kasan suna cikin matsanancin tashin hankalin da baki bazashi iya furtawa ba, ban tsaya anan ba saida na isa inda nake hangen wani matashin magidanci kyakkyawa wankan tarwada zaune rungume da wata mace yanata gursheqen kuka kamar ransa zai fita yana fadin.

“Innanillahi wa'innah ilaihirraji'un  Allahumma ajirni fih musibati wa'akalifni kairan minha!, Bilkisu karkimin haka kada ki mutu ki barni don Allah ki tashi inasonki wlh inasonki Bilkisu ki tausayamin kar kibi sahun sauran kema na rokeki ki tashi ki tashi ki fadamin me nayi muku kuke mutuwa ku barni wannan wacce irin qaddara ce Allah me nayi maka haka kake jarabta ta da wannan qaddarar wayyoh Allah na wannan wacce irin rayuwace!! Allah na tuba ka sassauta min wlh Azeem bani nake kashesu ba niba matsafi bane bansan komai game da mutuwarsu ba!!!.

   Janye gawar akayi daga jikinsa ya yunqura da nufin mikewa Amma sai jiri ya debeshi ya yanke jiki ya fadi sumamme da sauri akayo kansa cikin tashin hankali Wani da naji an kira Alh Khalid ya nufoshi ya kamoshi naya jijjigashi tare da yayyafa masa ruwa amma ina ko motsi baiyi ba wani matashin saurayi ne yazo suka kamashi suka fice dashi tare da wani dattijo suka sanyashi a mota suka fita dashi zuwa asibiti don gudun yin gawa biyu.

   A cikin gdan kuwa sutura akayima marigayiya Bilkisu aka dauketa zuwa gdanta na gsky zuciyar kowa cike da zullumi da tunanin meye yake kashe matan HABIBULLAH ne.  Suna dawowa daga kai gawar kowa ya kama gabansa wannan abu yayi matuqar taba zuciyar ahlin Habibullah musamman Hajiyansa da taketa gursheqen kuka Wata matashiyar mata ce naji tana rarrashin da cewa.

   “Kiyi hqr Hajiya wannan itace kaddarar Habibullah damu ma gaba daya....” “dakata Habiba babu wata qaddara Habibullah shine yake kashe matansa da kansa wlh ban yafeba ba kuma zan yafe ba jinin yata Allah ya isar miki Bilkisu  dama kinqi aurannan ubanki ya nace yanzu ga abinda nacinsa ya haifar mana mun rasaki har abada  Habibullah ya cucemu ya cuceki Bilkisu Hajiya Maimuna duk kece kikaja min wannan masifar Allah ya isa tsakanina dake wlh dagake har yayan naki da ya dauki yata ya aurawa matsafin danki da yafi qarfinki kike gudun laifinsa saboda yayi kudi da jinin yayan mutane....”

    Hannu Habiba ta daga mata tace “dakata Hajiya kada ki gayama mahaifiyarmu maganar banz....” da sauri Hajiya Maimuna ta rufewa yartata baki tana girgiza mata kai cikin fitar hayyaci da fizgar numfashi tace “ kada kice komai Habiba nada kaina dana haifi Habibullah lamarinsa yana bani tsoro tabbas shidin abin bincika na bansan meye gaskiyar lamarinsa ba Habiba ina tunanin zancan mutane gsky ne Habibullah yana qungiyar asiri tsafi yakeyi da matans....”

   Sauri rufe mata baki Habiba tayi cikin kuka tace “na roqeki da girman Allah ki daina fadar wadannan munanan kalaman akan Habibullah wlh Habibullah ba matsafi bane  kiyi masa addu'ar yayewar musifarsa” tana kaiwa nan ta mike tabi bayan Hajiya Rabi mahaifiyar Bilkisu da suka fita daga parlourn da nufin barin gdan ta nufi motarta ta shiga ta figeta da sauri daidai lkcn da Kiran da tayi ya shiga aka daga tace“Khalil kuna wanne asibitin ne?”..


~KU FARA DA WANAN~



*UMMUH HAIRAN CE* ...✍🏻

🙆🙆HABIBULLAH 🙆🙆Where stories live. Discover now