🙆🙆 HABIBULLAH🙆🙆

3.5K 142 6
                                    

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers_)


    🙆🏻‍♂🙆🏻‍♂ *HABIBULLAH* 🙆🏻‍♂🙆🏻‍♂

  Writing
              And
                    Story

*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
® *FAUZAH*

*Wattpad*👉🏻 *realfauzahtasiu*

🅿6⃣


Shidai Habeeb baice komai ba saima qara juya bayansa da yayi ya kuma rufar jikinsa da bargo shigowar Khamal ce ta sanya Alh Khalid dagowa ya duba agogo 2:30pm duban Khamal yayi yace “ya ake ciki ne Khamal?” murmushinsa ya fadada yace “alhamdulillah yays mun shaida wannan daurin aure me cike da tarihi a rayuwar zuri'ar Alh Bukar Bulama Bugari nina karbi sadakin Fahimah da hanuna naira dubu dari da hamsin gasu kaima ka sanya musu albarka”

Hanu Khalid ya daga yanayiwa Allah gdy yace“Allah na gde maka daka nunamin wannan rana mai cike da tarihi a rayuwata Allah ka sanya wannan aure ya zama sanadin sanya rayuwar bawanka cikin farin ciki  Allah ka zama gatan bawanka me tsananin biyayya a gareka ka yanke masa wahala da kuncin zuciya ka sanya yarinyar nan ta zama haske a rayuwarsa...” muryarsa ce ta fara rawa dole tasa yayi shiru yana dauke kwallar da take zubo masa a idonsa daidai lkcn Habibullah yaja wani doguwar ajiyar zuciya data sanyasu juyawa gurinsa da sauri Khamal ya janye bargon daya rufa dashi ganin yanda ya jiqe sharkaf da gumi yasashi kai hanunsa qirjinsa dagowa yayi ya dubi Khalid yace “yaya yana buqatar taimakon gaggawa fah bugun zuciyarsa slow yakeyi" shigowar su Alh Bukar ne yasa suka sami damar dagashi suka fita dashi zuwa wani asibitin kudi dake kusa dasu nanfa likitocin sukayi chahhh a kansa daqyar suka samu bugun zuciyarsa ya dawo normal sannan suka fita suka barshi yana bacci.

A bangaren amarya Faheemah kuwa tunda ta fita daga dakin da Abbannata yake taje ta sanar da kakanninta halin da yake ciki tana kuka daqyar suka lallabata ta tafi gurin walimar tasu qawayenta sunata harkokinsu amma banda ita ta koma ta zuba uban tagumi gabanta ne yaketa faduwa tunda ta tashi da safe tunanin halin data baro Abbanta yana damun zuciyarta, wata Hajjah ce ta nufota da sauri har tana tuntube ta miqe a razane tace“meya faru Hajjah?” hariye guntun yawu tayi tace “ Faheemah Khalid yanzu naje gidanku nemanki na kalli mutane sun cika qofar gdan ina shiga naji ana sanar da an daura auranki da wani waishi Habibullah Aliyu Jimaita....” dafe qirjinta tayi tace “nifa kikace Hajjah? Aa bani bace gsky Abbana ne fah Habibullah inajin dai bakiji daidai ba” tana kaiwa nan ta kwasa da gudu tare da wurgi da jakar hanunta.

Turus tayi a qofar gidan ganin mutane cike da gurin kallon kowa takeyi kowa yana kallonta wasu suna mamakin cewa itace matar aminin mahaifinta wasu kuma suna kallonta a matsayin gawa saboda yanayin girman jikinta babu wanda yake ganin tayi qanqanta da aure, can nesa kadan ta hangi kakanta da mahaifin Habeeb ta nufesu da sauri shima ya hangota kuma yasa wautarta don haka ya sulale daga gurin mutanen da suketa yimasa Allah ya sanya alkhairi ya nufeta hanunta ya damqa ya nufi cikin gdan da ita ta dago zatayi masa mgn ya dora hanunsa akan lebansa alamun tayi shiru haka kuwa akayi itama bata kuma cewa komai ba har suka shiga falon ya zaunar da ita saman kujera, sai lkcn ya bata damar yin mgn yace “ me kikeso kice  Faheemah?” cikin rawar murya tace.

“Alh akace wai an dauramin aure da Abbana?” jinjina kansa yayi da alamun tabbatarwa yace “ hakane na daura miki aure yanzun nan da Habibullah Faheemah ina fatan ke bazaki bamu kunya ba?” ya qarasa mgnr da alamun tambaya, kafesa tayi da dara-daran idanunta da suka ciko da qwallah cikin rawar murya tace “ Alh Abbana fah kace ya zaayi ka auramin Abbana  Alh shikenan yanzu nima mutuwa zanyi...?” rufe mata baki yayi da sauri yana girgiza mata kai yace “meyasa kikayimin wannan tmbyr?” kukane ya qwace mata tace “ iyakar tasowata nasan Abbana ya aure mata hudu dukkansu sun mutu kuma kafinsu ance ya auri biyu anan garin yayun baba Hajar maman Yanah qawata Alh hakane?” baiyi yunqurin kin fada mata gsky ba saboda haka ya jinjina kai yace hakane Faheemah bakiyi qarya ba kukanta ta qarawa qarfi tace “to meyasa ni zaku hadani dashi bayan kunsan cewa dukka matansa mutuwa suke wasuma suna cewa shine yake kashe matansa na rokeka Alh ka warware aurena da Abbana yaci gaba da amsa sunansa na ubana bazan iya kallonsa a matsayin mijina ba don Allah Alh plz wlh shima bazai soba”

🙆🙆HABIBULLAH 🙆🙆Where stories live. Discover now