🙆🙆 HABIBULLAH🙆🙆

3.3K 112 4
                                    

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers_)


    🙆🏻‍♂🙆🏻‍♂ *HABIBULLAH* 🙆🏻‍♂🙆🏻‍♂

  Writing
              And
                    Story

*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
® *FAUZAH*


*Wattpad👉🏻* *realfauzahtasiu*

🅿2⃣0⃣


Saida aka kira sallar asuba sannan ta iya miqewa da qyar tana tunanin abinda ya kamata ta taimaki Abbannata dashi fita tayi parlourn da niyyar dauko ruwa da cup ja da baya ta somayi tana karanta “innanillahi wa'innah ilaihirraji'un” da sauri ta juya dakin jikinta na tsuma ga mamakinta yanda taga parlourn haka taga dakin resting chair din da dressing mirror da komai dake dakin an hadesu guri guda cikinta ne ya qara cizonta saboda tashin hankali addu'o'i takeyi iyakar qarfinta kafin taji wata muguwar iska tana nata yawo a kanta miqewa tayi a razane tana qara karanto wasu zafafan addu'o'in ji tayi idonta ya rufe kuma har yanzu bata dainajin gunjin kukan iskar ba gefe guda ga Abbanta da yaketa kakarin mutuwa qoqarin bude idonta takeyi amma ta kasa can bayan wani dan gajeran lkc taji wani tiririn zafi ya tunkarota lalube ta farayi a duhu tanason komawa gurin da Abbanta yake amma ta kasa ji tayi kamar an naushi cikinta a wata gigitacciyar qara ta saki tare da yanke jiki ta fadi.

Bata sake sanin meke faruwa ba sai can yamma wajen la'asar a hankali ta rinqa jiyo sautin muryoyin mutane sama² a kusa da inda take motsa hanunta tayi a wahalce ta fara bude idonta tare da tsinkayo wata sabuwar azaba a cikinta batasan sanda ta cije lebanta ba tare da fadin “wash Allah cikina...” da sauri Habibullah ya qaraso gabanta ya ruqo hanunta ya matse da qarfi cikin wata irin murya taji yana cewa.

“Sas.. sannu Babe baki mutu ba ko? Don Allah ki taimakeni kada ki mutu kinji...” shiru taji yayi yanajan ajiyar zuciya bude idonta tayi tar akansa ta qura masa ido a hankali abubuwan da suka faru suka rinqa dawo mata a wahalce ta bude bakinta cikin muryar da bata fita sosai tace “kananan Abba baka mutu ba ko? Na kasance cikin tashin hankali a wannan daren Abba meye ya sameka?"

Kwantar da kansa yayi a saman cikinta kawai ya saki kuka me sauti kamar qaramin yaro batayi qoqarin hanashi ba saboda bata da wani qarfi a jikinta daga kanta tayi ta kalli qarfen dake jikin gadon da take sai yanzu ma ta fahimci ashe a asibiti take harma da robar jini a jikinta a dan rude ta kalli mummyn ta dake shigowa da Daddyn ta da sauri taga Daddyn nata yazo ya daga mijin nata daga jikinta ya rungumeshi ga mamakinta shima sai taga yana share hawaye, rarraba idanu ta rinqayi tsakanin iyayen nata da mijinta jansa Daddy yayi ya zaunar dashi yace “kayi hqr Habibullah insha Allahu bada dadewa ba Allah zai mayar muku da wanda yafi wannan alkhairi yanzu naje gdan naga abinda ya faru na tambayi yan aikin gdan gskyr abinda ya faru sunce sudai wayar gari kawai sukayi sukaga wani part na gdan ya rushe sun shiga domin su sanar daku suka tarar da komai na parlourn a hargitse komai na gdan daya shafi glasses a fashe daqyar aka samu wanda yayi jarumtar shiga dakin baccinku aka tarar daku kowa cikin doguwar Suma ita kuma Heemah cikin Jini hakanne yasa suka kirani suka sanar dani mukazo muka daukeku zuwa asibiti Habibullah yanzu likita yake tabbatar min cikin dake jikin Heemah ya zube.....”

Aiba Habibullah ba hatta Heemah saida ta zabura zata miqe Mummy ta riqeta Shikuwa zabura yayi ya miqe ya kama kafadar surukin nasa cikin rashin hayyaci yace “ yaya..ya zube...cikina ya zube kace Daddy da gaske koda wasa don Allah kace ba haka bane da wasane ko Daddy nasan ma da wasa suke maka kaje ka sake tambayosu babu abinda yasamu cikina yananan nanda wata shidda babe zata haifamin baby Dady ko?” janyeshi yayi daga jikinsa ya sake dubansa yace “kayi cooling mind dinka Habibullah da wuri zaku samu wani insha Allahu muma godewa Allah da abin ya tsaya iyakar cikin jikinta bai shafeta ba”

🙆🙆HABIBULLAH 🙆🙆Where stories live. Discover now