1

4.5K 97 1
                                    

*illar mazan zamani*

*by*

*AYSHA A BAGUDO*

      *maimuna matar abdullahi*

*yar mutan kagara*

*alhamdullahi muna yiwa dibin masoyanmu barka da sallah ,fatan an sha ruwa lfy Allah ya amsa ibadanmu, Allah yasa ibadunmu da mukayi cikin ramadam karbabbu ne allah yasa jannatul Firdaus ce makomarmu*

page 1 to 5

wasu kyawawan yam mata ne su uKu suke cikin wani dan tsukukun daki, wad'anda  dukanninsu yan'uwan junane ,uwa daya uba daya.
hafsat ce babba sai malika ,sai hauwa wace ake kiranta da imtisan .

hafsat da malika sun kasance yan son holewa da yawon zuwa club ne, yayinda imtisan takasance natsatsiya yariya, koda day bazaka tabacewar uwasu daya ubansu daya imtisan  .

cikin sauri sauri hafsata dake tsaye gaban mirrow take shirinta na fita yawon tazurba dinta data saba na yau da kullun, yayinda makali ke zaune agefeta tana dubanta a kaikaice sbd ita yanzu duniya tai mata warbar kunu, itakuwa imtisan wace shekarunta bazasu haura shatakwas ba tana kwance akan gado tana dubansu tare da takaicin kasancewarsu yan'uwanta.

gbdy hira ce  tashiga tsakanin hafsa da malika, wanda mafi akasarin hirar ta batse ce    wata buduwar ce tashigo dakin a matukar gajiye wace itama shekarunta bazasu  wuce  22 ba , ta cilla jakarta saman gadon da imtisan take kwance, aiko jakar ta sauka akan  fuskar emtisan dake kwance, take ta saki  kara me sauti dan taji zafi sosai wanda sai lokacin fauza ta lura daita .

"shit ta furta a galabaice sorry sisto  wlh ban lura dake ba,ta fadi hk tare da soma babbale botiran doguwar rigar abayar dake sanye ajikinta, wasu haddaun matsiyatan kananan kaya dake sanye ajikinta suka bayyana wanda basu da mara da tsirara, dan babu abinda ba'a hangowa ajikinta, ta fada saman gadon ,tana fidda numfashin wahala tare kiran washi Allah nagaji dayawa kana ta meida idanunta akan
hafsat dake  tsaye tana faman pente fuskarta "wai ni meyasa malika takasa sakin jikinta kmr akanta akarafa cikin shege?

"kema kya fada kawata gata nan  fa narasa gane kanta kwata kwata bansan metake nufi da rayuwarta ba.

"nayi mgn da idanu nayi da baki ke intakaice miki babu abinda ban mata mgn dashi ba, amman gatan nan jiya iya yau, "bata ko tausayina balle ta tausayawa wahalar danake akansu domin  rayuwarmu ta inganta.

"gatan lokacin dazata tsunduma kanta cikin harakar nan, babu yadda banyi daita ba domin naga ta tsira da mutuncinta amman hkn ya cutura, naso ace wannan bakar rayuwar ta tsaya akaina ni kadai banda kannena .

"burina a yanzu bai wuce ta saki jikinta ba .

"aikuwa yarinya gara ma ki maze ki dan dinga fita haraka ko babu yawa.

"haba haba fauza ta yaya zan fita haraka da wannan cikin duk da dai bawani fitowa yayi sosai ba amman duk da hk  ai zai kwambsa min bazai barni na shana ba.
"ke dakata wlh babu wani kwabsi , ai ingaya miki mafi yawancin alazawan nan ,sunfi bukatar mata masu  yaron ciki kmr ki, dan hk ki natsu ki san abun yi ta kalli inda hafsat ke tsaye gaban mirrow har lokacin tana gyara fuskarta .

"kina jina kawata ina dan iskan alhajin danace miki zamu hadu dashi yau.

hafsat ta tsaya da abinda take tare da juyowa tana fuskantar fauza "ingaya miki ba muna zaune tare dashi a hotel din daya kamamana ba har fa muna shirin fara harka, sai wani dan iskan yaronsa yakirasa wai ga me ciki yasamo masa ,jikinsa na rawa ya mike akaina" yace maza maza azo masa daita ita yafi bukata, intakaice miki ina zaune akazo da yarinyar dabata wuce sa'ar imti......

a  matukar zabure emtisan, ta mike zaune tare da dagawa fauza hannu a'a aunty fauza "karki sake kikarasa wannan banzar kwantacen naki dani ,maza ki tofar da bakin miyo ki canza akalar zancenki akaina." bazanye  kawai sun girma amman basu san  sun girma ba, tana karasa fadar hk tare da komawa ta kwanta tana  hararsu daya byn daya .

ILLAR MAZAN ZAMANIWhere stories live. Discover now