[11/12, 7:39 PM] UMMU SULTAN❣: WRITTEN BY UMMU SULTAN!!
Gaisuwa me tarin yawa zuwa ga masoya da abokan Arziki ! Ummu sultan loves u much .......!Wannan shafin nakine my Sweet Mom ! Ina rokon Allah ya kara miki lapiya da Nisan kwana !! Ameeen ya Rabbil izzati.
DA SUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI ......!
MANZON ALLAH ( S.A.W ).YACE" DUK WANDA YA HADDACE AYOYI GOMA NA FARKON SURATUL KHAHFI ZA'A KARESHI DAGA SHERRIN DUJAL....YAN UWA SE MUYI KOKARI MU HADDACE SU ......AllAH YAYI MANA JAGORA AMEEN.
NABILA 5-6
BAYAN ME NAPEP YA Ajiye BEEHA,Se ya wuce domin sauke ZEEHA ,Dan ita gdn su na gaban na su beeha sedai ba wata tazara sosai tsakanin su !!
Da sallama ta shiga gidan nasu, Umma CE zaune ita da Walida kanwar beeha din ,Suna kokarin yin alwala domin gabatar da sallar magrib .
Buta ta dauka itama domin yin tata alwalar .
Bayan ta gama sallar ne taji umma na kiranta ! Amsawa tayi tare da fadin gani nan zuwa umma .Littafin husnul muslimu ne a hannun ta Tana AZKAR na maraice ,
(Yan uwa yana da kyau mudinga yin azkar na safiya da maraice a koda yaushe domin Neman tsari daga sherrin mutune da aljannu.)
Ajiye littafin tayi bayan ta gama ,fitowa tayi Tana fadin gani umma , shimfida umma ke kokarin azawa inda mahifinsu ke zama domin kuwa da an gama sallar isha'i yake shigowa gida ...
Yawwa beeha ta kije ki duba abinci in yayi seki sauke min Dan ita waccan nasan shirme kawai zatamin Cewar umma.To umma ta fada hadi da bin hanyar kitchen din nasu....
Suna tsaka da cin abinci ne ita da Walida kanwarta ,Wayan ta ne ya shiga ringing ,Ta na dubawa koda batayi saving number din ba amma ta gane na Dr sultan ne Dan kuwa shikadai ne ke damunta da kira a kwanakin nan.
Sake kiran wayar akayi akaro na biyu shima batayi picking ba ,! A karo na uku ne umma taji ringing din wayar yayi yawa ta taso da niyyar ta kira beeha, ita ana ta tunanin ko beeha bata kusa ne ....
Itako beeha se tsaki takeyi Dan bata da niyyar dauka .umma CE ta fito daga daki TURUS Tayi ganin Beeha Zaune a kusa da wayar .
Takaici ne ya ishi umma tafara fada ....
Haba Nabila ke wace irin macece wai ?
Kina gani ana kiran wayar ki amma kikayi biris ,!
Wane irin wulakanci ne wannan?
To kisani mutum ba abun wulakantawa bane .Tana gama fadar hakan ta shige warta daki Dan ranta ya baci sosai.Jikin BEEHA ne yayi sanyi ,ganin ran umma ya baci .Setaji duk ba dadi domin kuwa tasan duk abunda ya saka umma yimata fada ba karamin bata ranta yayi ba.
Ringing din da wayar ta ta sakeyine ya saka umma fitowa daga daki don tasan ba karamin aikin beeha ne ba taki picking .
Ringing din ne ya dawo da Beeha da ga tunanin da takeyi ,Ganin umma ta tsare ta da idanu ne ya saka ta daukar wayar Tare da yin sallama...!
Ajiyar zuciya Dr.Sultan ya sauke wanda har se da BEEHA taji ,Ganin ta dauka ne ya saka shi cewa HELLO!!
Sallama ta karayi masa Dan yana cikin dabi'ar ta yin sallama idan aka kira ta ko ta kira a waya.
Hakan da Tayi ba karamin burge Dr tayi ba ,Amsa sallamar yayi !!
Gaisheshi Beeha ya amsa tare da cewa lapiya qalau my LOVE-
Shiru sukayi su dukan su ,can dai Dr.ya katse musu shirun da fadin "
Kin gane me magana kuwa??
Aa ni ban gane ba ....duk da sultan yasan ta gane hakan be sa yaki gaya mata ba ! OK kenan baki yi saving number na ba Any way dai Am Dr .Sultan by name.
YOU ARE READING
NABEELAH
Historical FictionLabarin Soyayya ,Tausayi ,Sadaukarwa Hadi da So me tsananin.