Yar Aiki Ce 001

1.9K 61 0
                                    

Bismillahir Rahmanir Rahim
Ya Allah yadda ka bani ikon fara rubuta wannan littafin lafiya ka bani ikon karashewa lafiya,ka bani ikon isar da sako mai amfani.
💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐

Wannan littafin mai suna Yar Aiki Ce kagagge ne,saboda haka duk wanda yaga ko ta gani yayi iri daya da rayuwarta akasi aka samu ba gangar bane.

Daga karshe ina mai sadaukar da littafin nan ga masoyana.

🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁💐💐💐💐
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁💐💐💐💐💐
🍁🍁🍁🍁🍁🍁💐💐💐💐💐💐
🍁🍁🍁🍁🍁💐💐💐💐💐💐💐
🍁🍁🍁🍁💐💐💐💐💐💐💐💐
🍁🍁🍁💐💐💐💐💐💐💐💐💐
🍁🍁💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐
🍁💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐

Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jinkai.

Zaune take suna karin kumullo tare da maminta.Koko da kosai suke ci,kallonta mami tayi sannan tace fatima kiyi ki tashi lokacin ya kure ta fada tare da kallon agogon dake manne jikin bango daki,wanda yayi nuni da cewa karfe bakwai da rabi ya gota.Tashi fateema tayi ta shiga daki game da dauko jakarta da mayafi ta fito tana daga ma mami hannu tare da murmushi,mamy tace Allah ya tsare hanya ya dawo dake lafiya.Murmushi tayi mata sannan ta daga mata hannu.Tana isa bakin titi ta tsayar da mai adaidaita ta bude jakarta ta dau littafinta tayi rubutu sannan ta nuna ma mai adaidaitar,kudinta ya gaya mata, murmushi tayi alamon ta gamsu sannan ta shiga suka wuce,suna isa ta biya shi kudinsa sannan tayi ajiyar zuciya tare da wuce cikin coffee shop din,wanda tun daga bakin kofar shiga zaka gane na masu dashi ne,sai dan wane da wacce kaidai suke shiga,wajan ya hadu iya haduwa,babu abin motsa bakin da ba'a siyarwa daga kan meat pie, donut,pizza,shawarma,ice cream,coffee da dai sauransu,fatima na shiga ta zarce wajan aikinta wato kicin,nan ta tarad da yan uwan aikinta,nafisa ridwan,james,samuel,jennifer.Nafisa ce tare ta tare da cewa fatima kin san fa oga bayan san latti gashi ke Allah ya zuba miki son latti,hada hannayenta biyu tayi alamon niman afuwa,Uhmmm naji cewar nafisa amma ki kiyaye. don Allah yaso ki yau oga bai tambayi wanda basu iso ba, da kashinki ya bushe,ido ta zaro tana mamakin cewa yau oga ya shigo da sauri shi da yake shigowa wajansu ten zuwa eleven,Nafisa ta katse mata tunani da cewa kuma yau ransa abace ya shigo ta fada yayin da suka karasa kicin din suka fara aiki,kiara ne ta shigo tana cewa fatima sannu sarkin latti wato yau Allah ya cece ki idan ba haka ba da kin shiga uku don oga da fushi yazo and very early,duk maganar nan da turanci kiara tayi don bata jin hausa sosai,zara ido fatima tayi tana kara jijina kai akan dalilin da ya shigo dashi da wuri yau,uhmmm Allah dai ya tsare gaba ta fadi azuciyar ta.

Baking suka fara ita kuma tana hada coffee don customer sun fara musu yawa,tray take hadawa da order din mutane,kiara kuma ita ke attending ma mutane so sai dai ta shigo ta dau tray din ta karasa ta mika musu,su fadeela da suzan kuma ana zaune reception ana gulmar mutane masu shigowa.Karfe daya suka yi sallah masu sallar kenan sannan suka koma kan aikinsu.

Karfe hudu nayi suka tashi,don shift dinsu ya kare yan dare zasu amsa,yan dare sukan fara daga karfe hudu zuwa goma dai dai.Adaidaita ta hau sannan ta wuce gida,tana isa ta shiga cikin gida babu kowa afalo so sai ta wuce daki tayi wanka tayi sallar la'asar sannan ta fito,mamy ta gani zaune,fadawa jikinta tayi tana murmushi,mamy tayi murmushi sannan tace baby bakya girma ko. Murmushi tayi sannan ta kara shigewa jikin mamy.

Karfe biyar suka tashi suka shiga kicin don girka abinda zasu ci,mamy bata barin fateema tayi girka,sai dai suyi tare ko kuma ta rinka mata fira ita kuma tana girka masu abincin.lokacin da suka gama girka shinkafa jollof wanda ya sha busheshen kifi da kayan lambu aka fara kiraye kirayen sallar magariba,daki suka shiga suka gabatar da sallarsu,har sai da suka yi isha'i sannan suka fito suka zauna cin abinci domin daman mamy ta shirya abinci a carpet a falo,Zaman fateema tayi dab da mamy,murmushi mamy tayi tare da zuba musu abincin suna ci suna kallon tashar arewa24 idan ake shirin Tarkon Kauna.
Bayan sun gama cin abincin neh fatima ta kwashe kwanokar ta kai kicin ta wanke su sannan ta fito tayi ma mamy sai da safe ta shiga daki ta kwanta don ita kallo bai dameta ba.
Tana kwance tana tunanin rayuwarta barci barawo ya sace ta.
Ni kuwa nace asuba ta gari babyn mamy

Vote n comment pls
Lot of love
Ummeeter

'Yar Aiki Ce🍁🍁🍁Where stories live. Discover now