yar aiki ce 008

614 22 7
                                    

💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕
💕💕💕💕
💕💕💕
💕💕
💕

💝Karasa shigowa sukayi tashiga gaisawa da mutanin wajan,duk inda ka juya 'ya'yan manyane da 'yan uwan juna,masu aikin sweet five ne keta shawagi da parantain abinsha a hall din,ko'ina kuma sai duma ke tashi abin dai ba'a magana,daga can gefe kuwa fatima ce da safiya suke tsaye da alama safiya na bata labari ne,safiya tace ni kuwa fatima ko kin san waccan mutumin ne naga tun daxu yake ta nuna ki suna magana da wani kuma ga dukkannin alamu yasan ki ne saboda yanda naga yana maki wani irin kallo,da sauri fatima ta juya tana kallan inda safiya ke nuna mata mutumin,suna hada ido dashi yayi saurin juyawa ya bar wajan, sannan ta juyo da kallanta ga safiya,ko kin sanshi ne safiya ta tambaye fatima,girgiza mata kai tayi alamun a'ah,daga nan dai suka shara zancan,birthday yayi dadi anci ansha antashi lafiya alhamdulillah.

 💞💞    BAYAN MAKO BIYU💞💞
kwance yake saman katifarsa lumtsantsiya kirar itali,idanunsa a rufe yana bacci hankali kwance,kamar a cikin mafarki yaji ana tashinsa daga bacci,ahankali ya fara bude idanunsa har suka washe ya sauke su akan maifiyarsa murmushi ya sakar mata tareda mike wa zaune,maifiyarsa tace jamal lafiyarka naga kana bacci har wajan karfe tara ko yau bazaka aiki bane,dan mika yayi hadi da yamutsa fuska yana fadin zani yau bani da aiki sosai a office shiyasa,momynsa tace shop din fa bakai bane da duty,aa momy yau khaleel ne yayi maganar ne lokacin dayake mikewa yayi hanyar shiga bandaki,jamal ta kira sunanshi,ahankali ya juyo yana kallanta tace idan ka fito inasan magana da kai,murmushi yayi ba tare da ya ce komai ba,mintina talatin ya dauka kafin ya fito palan cikin shirinsa na kananun kaya masu kara masa kyau da kwarjini sai zabga uban kamshi yakeyi,a palo ya tarad da mahaifiyarsa,ya zauna a kujeran dake fuskartarta yana fadin gani momy meki ke san gaya min,murmushi tayi sannan ta kira lami mai aiki ta kawo masa breakfast,sai data tabbatar ya kammala sannan ta fuskance shi tana fadin jamal a matsayina na maifiyarka mai sanka wacca ta duka ta haifeka,badan halina ba sai dan allah ina san insan abinda ke damunka,saboda naga kwana biyu kana cikin damuwa duk kabi ka rame ,kullum idan na tambayeka sai kace min wai aiki  ne,plzz a yau ina tambayarka ka sanar dani meke damunka,dan baka da wacca tafini ,baka da wacca zaka kai ma kukan ka ya share maka plzz jamal,da sauri jamal ya taso daga inda yake zaune ya isa inda mahaifiyarsa take zaune ya rufe mata baki,sannan ya fara magana kamar haka haba momy kece mahaifiyata meyasa sai kin tsaya rokona,ai kin fi karfin haka a waje na,yana kai nan yayi shiru hadi da sauke wawan ajiyar zuciya sannan ya cigaba da fadin abinda ke damuna bai wuce maganar SAYYADA ba,cike da mamaki mahaifiyarsa ke kallansa,bai tsaya jin abinda zai fito daga bakinta ba ya fara shaida mata komai da kuma zarginsa akan fatima wacca take aiki a matsayin YAR AIKI a shop din su, jinjina kai momy tayi sannan tace jamal naji zantukarka amman kasani cewan babu wani mamacin da zai taba dawowa doran kasa,agabanka aka suturta sayyada aka kaita gidanta na gaskiya saboda haka kamanta da batunta,ka manta da cewan ka taba sanin wata ya mace mai suna sayyada sai dai ka rinka taya ta da addua ita da mahaifanta masu kirki da sanin darajar dan adam,allah dai yasa mu dace,ameen dukkansu suka amsa,toh jamal dai ya yarda akan zai manta da babin sayyada badan yaso ba sai dan shi yafi dacewa a yanxu.

Ko daya isa office aiyuka ne suka yi masa yawa sosai bashi ya baro office din ba sai karfe shida na yamma,yana akan hanyarsa ta dawowa gida aka kira sallar magrib, parker motarsa yayi a bakin wani masallaci dan gabatar da sallar sa,bai bar masallacin ba har sai da aka sallaci sallar isha,karfe takwas saura ya kamo hanyar dawowa gida,yana tafiya a cikin motarsa baiyi auni ba yaji ya banke mutum babu shiri yaja burki  💝💖💖        ya tsaya ji kake kiiiiiiiiiiiiiiiii,da sauri ya fito ya isa inda ya banke mutumin,subahanallahi, allahumma ajirni fi musibati waaklifni kairan minha,sune addu'ar da ke fitowa daga bakin jamal,agigice cikin tashin hankali yake kokarin sun gumar bawan allahn dan sa shi a motarsa dan kaishi aaibiti,da sauri ya dakatar da jamal daga abinda yake niyar yi,numfashinsa na fita sama sama da alamu dai magana yake sanyi amman hakan yaki yuyuwa,da sauri jamal ya nufi motarsa ya dauko roban faro ya balle mufin ya kara masa dai dai bakinsa,sai daya sha rabin ruwan sannan,ya fara magana muryarsa sama sama yana fadin,lokaci na ya riga da yayi ko ,daman wannan ranar nake ta jira na gani ,ranar da idanuna zasu hadu da kai,akwai wata muhimmiyar magana da nake san gaya maka wanda nake ta adanama zuciyata kadai,yau kuma lokaci yayi da zan sanar da kai,dan kuwa na dade ina san ganawa dakai amman hakan ya faskara,nan ya fara tari sama sama,cikin tashin hankali jamal yake furta sannu,murmushin karfin hali mutumin yayi sannan ya cigaba da fadin ,ina san na sanar da kai cewan sayyada ba ,be karasa fadin abin da yake san fadi ba suka ji karan bindiga tassss sai a kirjinshi nan take ya fadi ya mutu cikin kidimewa jamal ya mike a kuje dan bin bayan wadanda suka aikata wannan mummunar abin amman cikin rashin sa'a sun bille masa ,hankalinsa a tashe ya dawo wajan gawan wannan bawan allahn ,nan take ya kira yan sanda ba'a fi mintina shabiyar ba suka iso nan,babu shiri karnuka suka fara shawagi a wajan suna haushi,amma babu abinda aka gani ,motan yan mutuware suka dauki gawan zuwa gobe dan bincikar iyalansa ko yan uwansa,har ofishin yan sanda aka kai jamal dan yin bincike da statement,duk abinda ya faru a tsakaninsu da bawan allahn nan babu abinda jamal ya rage ko kadan ,sai dai ma ya kara da fadin da alamu akwai abinda yake san ya sanar dani ,amman kafin yace wani abu an bindigeshi, captain ya girgiza kansa tare da yin wasu yan rubuce rubuce sannan ya amshi lambar wayarsa tare da yi masa godiya,💓💓💓💓💓💓

Karfe goma da rabi jamal ya iso gida duk agajiye tare da tarin dinbin damuwa da fargaban me bawan allahn nan yake san sanar dashi,meyasa suke farautar ransa,wadannan tambayoyin ne suke ta yawo akwanyar kansa,kuma ya rasa wanda zai bashi wadannan amsar,a hankali yake taka matakalar benan da zai sadashi da part dinsa,a hankali yaji an dafashi ,afirgice ya juyo dan ganin waye ne momy ce ya gani ,cikin tashin hankali momy take bin danta da kallo dan ganin kayan jikinsa ya bace da jini,arude take tambayarsa abinda ya faru,amman ko umfan yakasa cewa da ita hakan ne yasa taja hannunsa zuwa palo ta zaunar dashi dan jin ba'asin abinda ya faru,amman har a lokacin jamal ya kasa cewa komai,kuka momy ta sake hakan ne ya janyo hankalin manyan yan gidan saboda dare ya fara ratsawa ko'ina tsit kakeji dady ne ya fara fitowa daga part dinsa sai amjad da amal wadanda suma basuyi baccin ba,hankalinsu a tashe suke tambayar momy abinda ya faru dan ganin irin kukan da takeyi ga kuma jini daya bata kayan jamal,daker ta iya tsayarda kukanta tana sanar da su cewan bata sani ba,ran dady ya dan bace nan fa ya hau fadin taya za'ayi bata san abinda daya faru ba amman ta tasa shi agaba tana kuka maimakon ta tambayi ba'asin zancan,amjad ya dafa dady yana fadin wannan bazaiyi solving mana case din mu ba,haka suka shiga lallabashi ana bashi baki tare da nasiha da kwantar da hankali ahaka har suka samu ya warware masu abinda ya faru tun daga farko har karshe ba tare da ya rage komai ba,salati palan ya dauka tare da jajanta ma abin,daga bisani suka mike momy da amjad suka kaishi daki,amjad ya shiga toilet dinsa ya hada masa ruwa mai dumi dan ya gasa kijinsa momy kuma ta koma kitchen ta hado masa dinner ,bai jima ba sosai ya fito ya shirya cikin kayan baccin sa,sannan ya dan ci abincin sai da suka tabbatar da ya kwanta sannan suka bar masa dakinsa ,jamal kenan dan gata wajan iyayansa da yan uwansa kowa sansa suke shiyasa shi din na musamman ne a gidansu,nima dai cewa nayi ,asuba ta gare iyalan alhaji abubakar,nima na fece 😄😄😄🙂🙂🙂🙂🙂🙂

vote
comment
Share
Lot of love ummeeter

'Yar Aiki Ce🍁🍁🍁Where stories live. Discover now