Ganin nayi motarmu ta gaggara daji taje ta daki wata katuwar bishiyar kanya,bigewa nayi da glass din kofar motar wanda ya haddasa glass din ya fashe tare da jin min ciwo a kai,duk wannan bai daga min hankali ba tunda naga motarmu sai fidda hayaki yake kuma nan bada jimawa ba zai iya kama wuta,juyawa nayi da sauri na kalli ya shetima,sai lokacin na lura ashe akwai gun shot Asaman kirjinsa,ihu na saka ina kuka,lura nayi yana numfashi har yanxu,girgiza shi nayi ina kuka,bude idonsa yayi na kyar tare da yin min murmushi,kuka nake babu kaukautawa,hanunsa dake cikin aljuhunsa ya ciro da kyar ya damka min wani box dan karami kamar nah zobe,kallonsa nayi ina girgiza kai,shahada naji yanayi daga nan ban kara sanin abinda ya faru ba,kawai farkawa nayi na ganni gidan wani mutumi,ashe nayi sati biyu ina sume,wato ina coma,bai kaini asibiti ba don shima likitane,da na farka yayi tayinmin tambayoyi amma naki amsawa har dai ya gaji ya kyale ni,watara ya fita aiki ni kuma na fita daga gidan na gudu tare da wannan box din dai da bansan menene aciki ba,tafiya nake bani da ko kwandala atare dani,abun duniya sun isheni,ganin nake kowa ya juya min baya,mutuwa kawai nake son yi ko zan damu rangwamen abinda ke damu nah,ganin nayi kawai ina flying asama,ashe bige ni mota yayi,motar kuma ya gudu sai mamy nah neh ta tsaya ta taimaka min,gani na tayi mutane sun zagaye ni babu mai kawo min dauki,ita kuma tana cikin adaitaita sahu ta sauka ta taimaka min ta kaini asibiti,daga nan zamana ya koma gidanta,tunda na fara zama da ita ban bude baki nayi magana ba,na dauki alkawarin mantawa da rayuwar danayi abaya,bata san mai ya faru dani ba,na dai gaya mata cewa babana da ammina sun rasu,daga nan babu dadi babu kari,ban gaya mata cewa ana kirana da sayyada ba,cewa nayi sunana fatima,sai sa sunan sayyada ya mutu,yanxu kimanin shekara biyu kenan rabona da magana,tana kai nan ta daga ido ta zuba musu hawaye na diga daga idanuwanta,ajiyar zuciya duk suka yi kafin,jamal yace toh wannan dan box din da ya shetima ya baki fah,uhmmm yana nan,umma tace min wai lokacin da ta tsince ni ina rike dashi gam ahannuna kamar dai yana da mahimmanci arayuwata,har tambayata tayi ko ta dauko min nace mata a'a ta ajiye min,sau dayawa idan ina gyara mata wardrobe dinta ina ganin box din cikin amma ban taba budewa ba balle na san abinda yake ciki,uhmmmmm okay,gaskiya lamarin nan akwai rudarwa cewar hussain,but inaga dole muyi bincike amma ya kamata mu fara da wannan akwatin tukun sannan idan kinje gida ki dauki box din ki duba menene aciki,kila yayi mana amfani,toh tace kafin ta daga kai taga agogon ya nuna karfe biyar da minti biyar,ajiyar zuciya tayi sannan tace oga jamal ya kamata na tafi yanxu,mamy zata damu idan ta gan nayi latti,Okay toh amma kinsan baza mu iya bude akwatin sai tare da ke,murmushi tayi sannan tace nima bansan password din ba sai dai nayi dismantling din akwatin,ajiyar zuciya jamal yayi kafin yace ko ma dai menene ki shigo aiki da wuri gobe don mu fara kokarin bude shi,girgiza kai kawai tayi sannan ta fice tana tunanin ko meye ke ciki oho......
Lokacin da ta isa gida samun mamy tayi tsaye atsakar gida tana jiranta,fada ta fara mata akan kin daga wayarta da batayi ba,lokacin neh ta tuna cewa ta mantar da wayarta a office da kai tayi sannan ta fito da note pad dinta,rubutu tayi sannan ta mika ma umma,karantawa tayi sannan ta daga kai ta harareta,kafin tace banace miki duk idan zaki shiga ki daina ajiye wayarki anyhow ba,girgiza kai fatima tayi tare da langabar da kai tayi tare da hada hannu alamon bada hakuri,murmushi mamy tayi sannan ta ja hannunta suka shige cikin gida.........
jamal maye kake tunani akan wannan labarin da aka bamu cewar hussain,uhmmmm ni ganina akwai makarkashiya yanxu baza mu iya cewa wanda suke solving case dinsa bane mutanen ke bibiyarsu ko dan uwan mahaifinta,don alabarin akwai idan ta sha gaya mana,sain sa dake shiga tsakaninsu duk da bai zai kai kan kissa ba amma dole ta zamana daya daga cikin suspect dinmu.....
Yes i agree with you cewar khalil but ya kamata mu bi ahankali don akwai hadari,duk wanda suka yi wannan aika aikar,is either suna kallon moves dinta ko kuma sun dauka ta mutu,so kar mu bari asan we hold any relationship da ita,sannan she need to be also observate
Ka fadi dai dai Khalil don ni ban ma san ta idan zamu fara ba cewar hassan.
Yauwa kafin na manta ya kamata muje mu gaida daddyn aryan...gaskiya neh tunda suka dawo sau daya muka Je cewar hussain, yanxu idan mun fita sai mu karasa gidan Koh, amsawa suka dukkansu da eh kafin suka Mike don su tafi.........Daddy ya jikin, Alhmdllh ya aiki, mun gode Allah suka amsa dukkansu, madallah, daddy ya fada tana murmushi, uhmm hummm daddy yayi gyaran murya sannan yace dazun na gama yin ma aryan fada, duk dago kai suka yi suka kalli daddy sannan suka mayar da kan aryan wanda fuskarsa babu yabo babu fallasa, dukkanku kunfi shekara talatin amma sai yawo kuke atiti babu iyali, kallon juna suka yi, irin kallon sanin nan, wato sun San za'a rina kenan, cigabawa daddy yayi da cewar wato ku kuna Jin dadin zamanku ahaka neh ko mene,so kuke sai kun kai tuzuru kafin kuyi aure, dariyar da daddy yayi neh ya saka yayi shiru game da kallon kofar da sai sada ka da kitchen, ganin little yayi tana dariya, kallon ta su Jamal ma suke, sai dariya take kamar wata zararriya, sai da tayi maishi sannan ta dago ta kallesu wanda duk ido suka zuba mata, kunya taji ta sunkuyar da kai, daddy neh yace kin gama, girgiza kai tayi alamar eh, daga nan kuma ta karaso, Zama tayi kusa da daddy sannan tace daddy ai idan suka Zama tazurai babu wacca zata aure su sai tsohuwa, ta fada tana murmushi, murmushi daddy yayi Shima kawai,kallon su tayi sannan tace ya Jamal zaku tsaya dinner koh don nace ayi daku,ya think fuskar Khalil yayi, murmushi little tayi sannan tace, uhmmm ya Khalil dole sai ka tsaya fa don Naga ka fara yatsine fuska, gaskiyar daddy neh idan baka son girkin house help kayi aure mana, hararanta yayi sannan yace toh ba cewar nayi ki aure ni ba ki ka ki, zare ido tayi sannan ta tashi da gudu ta such idan ta foto, dariya daddy yayi don idan da sabo ya saba da shirmen Khalil da little.......
Am super duper sorry, kwana biyu kunjini shiru koh, kuyi hakuri pls dan Allah,zaku ce wannan ta fiye bada Amma ayi min uzuri Matsala aka samu.........
Kuyi managing wannan insha Allah zan rinka posting one day off one day on.
Pls vote comment n share
Love
Ummeeter n ameerah
YOU ARE READING
'Yar Aiki Ce🍁🍁🍁
Short Story######## Labari Daga=> Aisha Zakari(Ameerah) Rubutawa => Ummi Amina (Ummeeter) 💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐 Labari neh akan wata yarinya mai suna Sayyada da ta mayar da kanta bebiyaa,saboda wa su mugayen mutane d...