*_BURI DAYA_*
_Mamuhgee_Bismillahir-rahmanir Raheem.
I Dedicated the whl of this novel to you herphsatuh (jirwaye).
Sauri yake faman zubawa Amma yanda saurin nasa yake tamkar Yana gudune sbd yanda ko gani bayayi sosai ga babbar rigarsa sai cika takeyi da iska tana qarawa,
Da safe kafin yafita jin zuciyarsa yakeyi fes sbd tunanin yau ranar sa'arsace tunda zasuje maula gidan mai arzikin da yafi kowane mai kudin jahar kudi harma dana wasu jahohin saigashi masifar datafi ha'darin mashin bala'i ta afko masa Dan gwara yasan sama mashin yayi dashi ya zubar akan abinda rashin hakurinsa yaja masa ayau din,
Yana shanyo kwanar layin gidansa wani mugun zufa ya yanko masa ya tattaro kuzari da qarfin hali yacigaba da tafiya Yana kallon tarin kalolin 'yan ta'addar dake cike da qofar gidansa sun baje sunashan iskar makeken bishiyar durumin dake qofar gidan kusan su goma Sha biyar kowanne da kalar mugun makamin dake soke cikin qugunsa ko wani sashe na jikinsa Wanda duk qaddara takaisa shiga huruminsu yanxune zasu yiwa rayuwarsa illa Kuma ba Wanda ya isa ya tanka sbd hukumar ma da ikonta suke aiki sbd zakinsu shine amintaccen yaron DIKKO DILLA.
Wasu daga cikinsu fuskokinsu cike sukeda zanen Sara ko Suka haka jikinsu kusanma Babu Wanda fuskarsa bazata saka mai qaramin qarfin jini zawoba sbd Sam babu alamar wasa atareda fuskokinsu ga wani irin warin daga da wiwi dake tashi tun daga farkon layin unguwar shiyasa yawanci duk Wanda yake Dan asalin gari yasan anguwar ba wurin ganganci bace anguwar sarki ZAKI NEYO ce Sam ba'a mata garaje.
Da gudu gudu sauri sauri yaqarasa shigowa gidan tsohuwar babbar rigarsa kalar ruwan madara data koma kalar brown tana sake dibar iska sbd sauri dayake diba kamar zai tashi sama musamman yanzu daya qara ganin bataliyar 'yan daban dake qofar gidansa kamar qofar gidan wani qaura.
Yana shiga tsakar gidan sbd tsantsar rudewar dayake ciki ya kwashi wani mugun tuntunbe saura qiris ya kife cikin garinda iya talatu ta shanya na kayan mata datake siyarwa duk da duk rabi garin kukane take zubawa sbd yayi mata afkin siyarwa.
Zaune take tana lissafin jarkar tsimin data Saida wadda duk rabi jollyjus ne ta zuba aciki shima sbd afki.
Kallonsa tayi amatuqar sheqe cikin takaicin yanda ya tashi goga mata asara ta hanyar barar mata da gari a 'dan hasale tace"
Wai meye hakane kaketa muzurai kana rawar jiki kamar 6arawon daya ha'diyi kunama?,
Yanzu wannan garin dakake Shirin bararmin kasan hasarar nawane zaka jazamin Wanda nasan ko shekara zakayi kana sana'ar taka ta mutuwar zuciya bazaka Tara kudin biyana ba inyi magana jarabben sarkin gidannan yace bayason hayaniya kokuma yakamamin dabbobi yasa ayanke masa inaji Ina gani qatti suci banza.To wlh banshirya hasaraba kusa Dan haka kafita idona inrufe.
Takalmin hannunsa ya fitar daga cikin babbar rigarsa data gama jiqewa da zufa,
zufa na qara tsatsafo masa Yana zare qananun idanuwansa dasukafi kama Dana Chinese din hauren qasa yace"Qaddara takaini daukar aron takalmin ZAKI NEYO wainda kikaji dahiru yace dubu biyar suke nafita dasu wlh sun katse fata fata duka qafar biyu gurin gudun mahaukatan Karnukan da alhaji dikko dillah yasa aka sakarmasa ga yan maula da mabaratan dasuka tarar masa qofar gidansa duk da tarin yan sandan dake gadin gidan.
Wani irin sabon qululun baqin ciki da takaicine ya quleta tana watsa masa wani mugun kallon takaici baqin ciki yahanata ce masa qala sbd duk iya quluwa da baci ranta yayi sbd sanin masifar da hakan zai jawo
ta miqe ta tahau tattara kan akuyoyinta da kajinta dake walwalarsu filin tsakiyar gidan Dan tasan yau akwai saukar aradu a gidan Dan yau ko butar gidan saita ci uwarta idanba Allah ya tsareba baresu
Akuyoyinta da kajinta kuwa tasan tsaf zai take mata kawunansu su mace abanza,
Tana zaman zamanta rukayya taje Lagos ko wata shegiyar qasar ta hado jini da kafirai kokuma qila wata qabilar anxo anhaife mata masifar daba ita kadai ta addababa har yan gari da anguwa Dan kuwa neyo ba ubanda baya tsoro da shakkarsa ga wani irin kwarjini dayake qarawa mutane tsoronsa.Wani Dan dakin kaji ta gargadasu gabaki daya ta rufe da kwado ta zare mukullin ta dawo tafara tattara garinta tana kwashewa cikin takaici da baqin cikin dake tafasa zuciyarta ta bude murya tace"
NADIA uwar uban me kikeyi a bakin murhun haryanzu dabazaki taso kitayani tattara duk wani tattalin arzikina dake tsakiyar gidan nanba kinaji mara danganar ubanki ya ballo Mana balain dayafi 1990 masifa.
Aje plate din robar dake hannunta tana fifita wutar murhu dashi tayi ta taso gabanta na matuqar faduwa sbd jikinta dayayi sanyi dajin abinda babansu yayi Dan tanajinsa duk abinda yake fadawa iya talatun koba komai tasan idanba Allah ne ya fiddataba akantane zaifi sauke haushinsa tunda itace mara galihu agidan Dan idan yafara kowa shigewa daki yake ranar bamai fitowa saiyagama fushinsa ya sauka ita kuwa dole take fitowa sbd balain iya talatu shiyasa idan tafito yake sauke Rabin haushinsa akanta ga wani irin mugun tsoronsa da shakkarsa da Allah ya halitta a dukkanin zuciyoyin 'yan gidan harma Dana waje saidai zata iya cewa itakam tsoronta yafi nakowa duk da dai duk balai da msifar iya talatu da duk anguwar ake tsoro itama shakkarsa takeyi.
Jikinta na Dan rawa tafara tattarawa iya talatu kayanta..
Da 'yar waqar sani sabulu wata 'yar budurwa tashigo gidan taci ado cikin Riga da skirt na atampar sheraton 'yar dubu uku da dari biyar fuskarta a kimtse tsaf da kwalliyar dataji hoda da foundation datai mata kyau ba laifi da Jan jambaki 24 hours hannunta riqeda Jakarta da 'yar wayarta vivo mai Dan dama dama sai qamshin bokhour takeyi daga gani cikin nishadi tadawo.
Cak ta tsaya tsakiyar gidan tareda kallonsu cikin mamaki da 'yar fargaba ganin sai tattara kayan tsakiyar gidan sukeyi fuskar iya talatu ba alamar rahama ko kadan ta maida kallonta kan babansu dake tsaye gefe sai zufa yakeyi kamar Wanda yaci wuta takalli iya talatu tace,
Iya lafiya kuke kakkamta kaya rana tsaka?
Harara iya talatu tafara watsawa dattiya dake tsaye har lokacin kafin tace,
Rashin hakurinsa yakaisa ga daukar takalmin ZAKI NEYO yasa yaje yawon maula aka hadosu da miyagun karnuka sukaiwa takalmin fatafata.....
Kallon babansu tayi cikeda takaicin Rashin danganarsa da ako yaushe baya jawo musu alkhairi sbd fargaba da tsoron masifar daya jawo musu basujiba basu ganiba ta turo baki tace,
Nikam baba meyasa bakason ko yaushe a zauna lafiya agidannan gashi yanzu mutum saiya kwana biyu bai wani dogon motsiba sbd tashin hankalin yaya neyo
Yanzu wlh ko mai neman aurena yazo qofar gidannan saiya gwammaci karo da mahaukacin matashin kare akan fushin wannan abin daka yi baba.Kallon iya talatu tayi cikin takaici tace,
Ni wlh nakoma gidansu anty saratu sai dare ko gobe zandawo Dan wlh bazan yarda a mari wannan kyakkyawar fuskar tawa abanzaba tunda babu Wanda yake siyamun mai.
Juyawa tayi rai abace cikin haushi da takaici ta fice tabar gidan tana guna guni sbd tasan tsaf da marin neyo gwara mashin yayi sama dakai.
Nadia kuwa cikin sanyin jiki duk takai ma iya kayanta daki tadawo ta gaban baban nasu dake tsaye Yana muzuran ido cikin mirsisi yace,
Ke ungo nan yi musu dubara da allura da zare ki dinkesu kikai dakinsa ki ajiye masa Kuma wlh duk rintsi Kar shegen dayace nine nasakasu.
'dagowa tayi da sauri takallesa da manyan fararen idanuwanta cikin tashin hankali.
Harara ya watsa mata yace,
Bazakiyi bane kike kallona kamar nace ki kashe mutum.
Sunkuyar da kanta tayi tareda girgizawa idanuwanta na cikowa da hawaye ta karba da hannu biyu ta wuce.
baza babbar rigarsa yayi tareda kada mata iska ya fada dakin iya talatu Yana sharce zufan daya kasa daina jiqasa.
Nadia kuwa bakin akurkin dakinta ta zauna bayan tadauko allura da zare tahau yiwa takalman kwaskwarima jikinta na matuqar rawa sbd sanin yau kwanan wahala zatayi idan yadawo yaga wannan dinkin a jikin takalmansa bayan antsinka.
#Mamuhgee.
#vote
#comment
#andfollow
YOU ARE READING
BURI 'DAYA
Actionand where love ends hate begins.......rayuka da ra'ayoyine daban daban tareda banbamcin rayuwa Amma burinsu dayane...na cimma burin daukar fansar abinda kowannensu ke ganin an wargaza masa.