31-40

2.2K 56 2
                                    

[11/10, 21:25] Mariyat Lawal: 💞  *DOCTOR NA'IM (AA)* 💞



®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼


Written by

*Mariyat Lawal Muhammd*
    💞Mummy💞

*DON'T 4GT 2 FOLLOW & VOTE 4US @GaskiyaWritters Asso ON WATTPAD*

Page 3⃣1⃣

Ya k'araso dai dai saitin inda take tsayen, cikin sanyin muryarshi yace
"Neehal meya faru na ganki a nan? "

   Shirun da tayi mishi ya d'an sashi shiga rud'u, ya soma bin gidan da kallo, toh shidai baiga wani Abu da yake zargi ba.

Ya sake dawo da kallon shi gareta "please Neehal talk to me mana, watss going on"
      

Har lokacin bata d'ago ba balle ta bashi amsa. Sai gyara mayafin dake lullub'e a kanta da tayi

Shima ganin bazatayi mishi magana ba, sai kawai ya ruk'o hannunta ya koma b'angaran nata da ita.

A gefan makeken bed d'in ta ya zaunar da ita, ya d'auki ledojin shi ya nufi side d'in shi.  Ya salam, ai dana shiga d'akin Na'im sai naga na Neehal nafula ne, domin kuwa nashi b'angaran ya ninka nata had'uwa ninkin ba ninkin.

Gashi kusan tsarin ginin nasu iri d'aya ne. Banbancin d'aya ne, shi nashi ba kitchen.

Falonshi komai milk colour ne, kamar dai nashi na gida.

Ajiye ledojin yayi a saman drower bed d'in.
    Malum malum d'in ma a gefe ya ajiyeta, don dama shi ta ishe shi don ba yadda zaiyi ne

Towel ya d'auka ya fad'a bathroom d'in shi. Wanka yayi Sannan ya futo d'aure da alwala.

Shafe jikin shi yayi da had'ad'd'un perfumes d'in shi masu matuk'ar k'amshi. Sannan ya zura jallabiyyar shi fara Sol.

B'angaran Neehal ya dawo. Tana zaune inda ya ajiyeta, ta had'a kai da gwiwa.

   Ya zauna a gefanta tare da d'ago kan nata a hankali. Idonta ta runtse Amman duk da haka hawaye bai daina silalowa daga cikin suba.

"Neehal"  ya kira sunanta cikin kwantar da murya, bata amsa mishi ba, kuma bata bud'e idon nata ba.

Yasa tafin hannun shi a hankali yana goge mata hawayen.

   "Please ki dena kukan nan haka kinji?"

Gyad'a mishi kai kawai tayi.

   Yace "toh yanzu ki tashi muje ki d'an watsa ruwa, kiyi sallah saiki kwanta ki huta koh?"

Nan ma bata ce mishi komaiba, sai mik'ewa da tayi, shima mik'ewar yayi, ya duba cikin kayanta ya Samar mata rigar bacci me d'an kauri wadda zata iya sawa da hijab.

A tare suka futo ya kulle k'ofar
   Suka nufi nashi b'angaran. Jikin Neehal ya gama yin sanyi, kuma ta gama saddak'arwa, shiyasa ta soma yak'i da duk wani tsoro dake cikin zuciyarta. Tayiwa kanta alk'awarin duk abinda yaya Na'im zaiyi, ko zai sata bazata tab'a hanashi ko tayi mishi musu ba, a duk iya tsawon zaman da zasuyi dashi kuwa.

(Toh mudai kam munce Allah ya baki ikon cika wannan alk'awari naki Neehal😊😊😊😊😊)

Hanyar bathroom d'in shi ya nuna mata, tare da mik'a mata night gown d'inta. Batayi musu ba ta karb'a ta shige ciki. Sai data jima a tsaye tana y'an tunane tunanenta, kafun tayi wankan ta d'auro alwala. Ta tsaya gaban mirrow tana kallon kanta da yadda rigar baccin ta d'an kama jikinta duk da batayi rasha rasha da yawa ba, gashi kanta babu d'an kwali gashin kanta ma'abocin tsawo da yawa ya sauko har saman kafad'ar ta.

DR NA'IM (A.A)Where stories live. Discover now