Har na shiga cikin parlour banji an kar6a min sallamar da nayi ba ,daman ban sa rai ba.don na saba wata rana ta amsa min wata rana kuma tayi shiru,haka zaman ya k.motsi da naji kitchen yasa ba duba tana ciki tana hidimarta ,nidai na wuce daki na cigaba da hidimar gabana.anfara kiraye kirayen sallar maghrib as usual gidanmu ya kauraye da hayaqin turaren wuta gabana bai fasa faduwa ba tsikar jikina duk suka tashi ga fili na ambaci inna lillahi wa'inna ilaihi rajiun na kuma ci gaba da ambaton sunayen Allah.daga qarshe na daga hannaye na sama na fara adduar da na saba."ya Allahu ya Rahmanu ya Rahimu ya Malikul quddus,ya Hayyu ya Qayyum,ya Zuljalali wal ikram,ya badi'ussamawati wal ardi,ya Rabbi ya Rabbi,ga baiwarka Allah,in har wannan turaren na sharri ne Allah ka muna tsari da shi ni da yarana,Allah ka sani ina cutuwa da wannan hayaqi Allah ka kawo min qarshen wannan zaman Allah ka min mafita cikin mafitar ka Ya Allah ka gwada min na komawa rayuwa ta dagani sai yarana cikin ni'imar ka da rahamar ka,da jinqan ka da kariyar ka albarkacin fiyayyen halitta Muhammad masoyinka,masoyina amin .rabbana taqabal dua amin"na shafa sannan na shiga toilet dina dake cikin dakin nayi alwala na fito.bayan na gama sallah ina zaune ina tunanin rayuwa,saiga yara da kulolin abinci sun aje gabana ,da plates da spoon na bude to nan ma dai maganar guda ce kamar an qirga muna spoons nawa zamu ci na girgiza kai kawai duk yaran na kallona,na zuba musu abinci qaramin yace mama bani nama na,shima dai as usual duk qassa na dan bubbuga inji mai dan tsokar inbashi sauran kuma nace suci hakanan,lomar farko Sarah ta 6ata fuska Allah mama ba maggi.na ce dauko Ku murmusa Ku dan sa yaji,Allah ya muna maganin abin da bamu iya yiwa kanmu.
A haka dai aka ci abinci ni daman na saba sai dai in aje 'yan kayan qwalama in abinci bai isa ba su ni k ci don presently matsalar da Mike fuskanta k nan ga amaryar gidan amma ga idon mutane ai na samu sauqi tunda an rabani da wadancan.wani lokaci in zauna inyi ta tunanin shin me yasa mata muka 'yan wahala?in ka auri mai mata tace kin auri mijinta,don haka sai yadda ta k so,in kuma kai aka isko tace dole a canza tsari abi yadda ta k so.wancan lokaci na yadda ni na isko shiyasa wani abin in qyale.to yanzu kuma ni ka isko kuma so akeyi in ci gaba da qyalewa anya hakan na yiwuwa?
Matsalar rashin bamu abinci wadattace ranar girkinta anyi ta case din maigidan bai dauki mataki ba.ga shi yasa dokar in ba k k da girki ba ba ruwanki da kitchen.
To yaya mu ci gaba?labarin ya samu karbuwa?ko
YOU ARE READING
mace hudu
Non-FictionAssalamu alaikum littafin mace hudu labari ne da ya qunshi fadakarwa nishadantarwa.Allah ya sa mu dace amin