Sunana Amina,amma an fi kirana da hajiya don sunan kakata naci wadda ta haifi babana,mu goma sha biyu ne ga mahaifina matan aure biyu dakinmu mu biyar dakin dakin umma su bakwai kuma itace uwargida,mu biyar ne mata sauran maza ne.dakin mu nice ta hudu gidan gaba daya kuma nice autar mata.yanne na mata duk sun yi aure mazan ma su ukku suka rage ba aure.gwargwado mun taso cikin kulawa da rufin asiri.mahaifinmu maaikacin gwamnati ne iyayen mu mata kuma sana'o'in cikin gidan su k yi.akwai zaman fahimta gidanmu,muna son juna,dukanmu munyi karatun boko.yanne na mata duk suka aikinsu na gwamnati.sai ni da zan shiga tertiary yanzu.amma harga Allah nafison inyi aure kafin in ci gaba har dai da naga qawayena nata aure.
Ina zaman jiran admission ya fito bukin qawata ya tashi.sai dai ina wasiwasin inje ko kar inje don ba cikin gari bane bukin.garinsu zasu wato zamfara ni kuma sokoto.har gida tazo ta roqi mahaifana su bari inje bukin haka dai na daure naje.mun fara bukin mu kamar yadda aka saba har ranar daurin aure ranar da ta shigo qundin tarihina don ko a ranar na hadu da Wanda ya zama abokin rayuwa ta,kuma abokin gwagwarmaya.soyayya ce ta qullu tsakaninmu da Muhammad kabir.yana cikin manya abokan ango.ga wancan lokaci babu mobile phone,sai land line don haka ita mukayi sharing .daga wannan lokaci kuma duk wani ranke ranke saurayi na na aje shi gefe.ban gani kowa sai kabir.abinda ban sani ba Ashe kabir matansa biyu.duk irin hirar da mukeyi ta mace guda ya k min da diyansa ukku.shima maaikacin gwamnati nan yake zaune zamfara.soyayya mu k yi bil haqqi da gaskiya.ina son kabir sosai kamar yadda shima ya k gwada min so,in ba an fadi ba zaa zaci saurayi ne don yanayin jikinshi kuma baida shekaru da yawa don haka na saki jiki na.nikam naga mijin aure.kabir Nada yawan fara,a nan da nan ya k sabo shiyasa ba wani dauki lokaci ba duk gidanmu aka sanshi,ya zama dan gida weekends ya k zuwa mu yini tare,ganin haka yasa gidanmu fara maganar aure, shima ta gefenshi ya nuna ya buqatar haka.duk iyakar binciken da akayi baa samu kabir da takamaiman laifin da zaa kamashi da shi ba.sai dai angano cewa matansa biyu yara biyar ,kuma hakan yaso ya kawo matsala don iyayena da yanne na sun dauki hakan a matsayin yaudara.k nan ba gaskiya yayinda kabir ya dage wajen nuna min yayi kuskure a masa afuwa .ni kuma ido na sun rufe ga sonsa.kamar anayi kamar baayi cikin hukunci ubangiji mu kayi aure da agreement cewa zan ci gaba da karatu.sannan kuma gidana daban bai hadani da matansa ba duk dai cikin ban haquri boye min gaskiyar da yayi don haka na saki jiki.na kwantar da hankali na mu ka bude sabon shafi na amarci cikin soyayya****To yaya ne???inci gaba da labarin ya samu kar6uwa ko in aje in kwanta bacci??sai na jiku.nagode.
Allah sa mu dace amin.
YOU ARE READING
mace hudu
Non-FictionAssalamu alaikum littafin mace hudu labari ne da ya qunshi fadakarwa nishadantarwa.Allah ya sa mu dace amin