page 31

412 67 6
                                    

🐾🐾 ZATO...! 🐾🐾


  ©℘ıŋƙყ
Wattpad:-pinkylady222

Page 3⃣1⃣

     I dedicate this page to you,~Smart and Jaanah😻 i really appreciate  your comments.

      Tun daga lokacin sai Almu ya ishi musty da rakiyar duk ina baban shi ya aike shi anso sihirce-sihircen shi. Wata rana ya bishi wata ran ya zame yaƙi zuwa.

A fannin karatun shi kuma ga dai jarabawa ta fito tai kyau amma baban shi baya da halin biya mashi zuwa ta gaba. Dan haka sai ya hakura ya ci gaba da ƴan buge-bugen shi cikin gari har Allah ya hore mai. Shine kasuwa,tasha aikin ƙarfi duk dan ya samu kuɗi ya tallafi iyayen shi da shi kanshi.

Bayan lokaci ya ja, ya fara zuwa kano ya na sawo ƙananan atamfofi da kayan kwalliya na mata ya na saidawa,harma inya sara ya kafa ƴar rumfar shi ya saida wani abun zuwa la'asar ya juyo da sauran kayan. Wasu lokuttan Almu kan raka shi dan ya ce shi bazai ɓata lokacin shi ga ƙananun sana'a ba ya jira ya ga kuɗin da zasu zo mashi a dinga bashi girma ana kiranshi da Alhj.

**
*Kano*

  A cikin wani lungu marar ɓulewa a unguwar galadanci. Mutane ne da ɗan yawa a ƙofar wani gida.
Wasu bisa baburan su wasu kuma bisa dogon tebirin da ke aje ƙofar gidan suna fira akai-akai game da abinda ke wakana a ƙasa.
  Akai-akai yaro  kan fito da leda ko plate  a hannu ya miƙawa wani daga ciki.

A cikin gidan kuwa
manyan murahu ne guda biyu ko wanne ɗauke da tukunya dai-dai shi.

Wata mata fara tas mai dan jiki, zaune agaban murhu ɗaya da abin tsame ɗanwake a hannu  ta na tsamewa ta na zubawa cikin wata roba mai ɗauke da ruwa.
Bayan ta gama tsamewar ta dinga zubawa a plate ta na ba yaran da aka aiko suna miƙawa na waje.
Sai zufa take tana sharewa da haɓar zane.

"Karimee! Karimee! Wai ina kika shige iyee? Matar ta faɗa cikin ɗaga murya.
 
Wadda aka kira da karime ta taso ta na dafe kai da alama ciwo ya ke mata.

"kizo ki duba Alkubus ɗin nan na fara jiyo ƙamshi,ga mutane can waje sai jira suke,ai haka babu daɗi"

A hankali ta isa ga tukunyar ta duba."ya yi innar mu" ta faɗa.

"To jiran me kike maza a sallami mutane, su kuma ƴan uwan naki daga aike shiru haryanzu basu dawo ba" innar ta faɗa ta na mai da hankalin ta ga zuzzuba ɗanwaken.

Basu samu kansu ba sai bayan la'asar. Alokacin masu siyan ɗan-wake da Alkubus sun tafi.sai kuma a san nan ƴan mata biyu suka shigo gidan kowacce fuskar ta cike da farinci ki, da alamun acen inda suka je sukaci karo da abin da ya assasa masu shi.

Inna da ta ji sallamar su ta fito dan faɗa sai ta yi shiru ganin su da ƴan ledojin su a hannu sai washe baki suke.
Ita ma saita washe nata bakin dukda bata san dalili ba.
Sai da suka zauna sannan suka baje mata kayan hannun su suna faɗin ta duba. Hannu na rawa ta dinga buɗewa ta na ƙara baza hanci.

"A'a ƙamshin mai nike jiyowa kamar kaza-kaza kamar tsire?"

Dariya babbar ta yi,ta gyara zama.
"Ai innar mu da alama burin ki ya kusa cika, kin kusa hutawa da wahalar hayaƙi ki koma gefe ki na shan A.C"

Farinciki ƙarara ya bayyana a fuskar inna"ke kau yi sauri ki sanar dani. Ta dakata da ga buɗe ledar. Ta kalli karimee da ke shafa saboda wankan da ta yi bayan gama aiki." Matso kusa kekam ana abun arziki kin yi zaune"
Murmushi kawai ta yi tasan dai tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi in dai lamarin ƴaƴƴen ta da innar sune.

"Ina jinki zuwaira"
Ɓata fuska ta yi tace"zuwairat zaki ce innar mu"
"To naji zan gyara, faɗi man"

"Ai innarmu mun shiga kasuwa da sa'a muna isa ga mai cefanen wani ɗan gayu ya zo da mota...in dai taƙai ce maki hauwa'u ya hango, shine silar duk siyayyae nan san nan ya ce azuba mana komai na cefanen. Gobe ma ya ce zaizo"

ZATO...! Where stories live. Discover now