Page 1

1.8K 197 8
                                    

🐾🐾 *ZATO...!*🐾🐾

©℘ıŋƙყ
Wattpad:pinkylady222

Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai.

A cikin talatainin daren baka jin motsin komai sai kukan k'wari akai-akai. Takowa take ahankali, sai dai duk sa'ilin da ta dauke kafarta tana jin kamar akwai mai maye gurbin sawun nata da nashi takon. k'okarin kauda tunanin hakan ta dingayi sakamakon fitsarin da take jin inta k'ara cikakken minti d'aya bata yi shi ba zai zubone da kanshi.

A haka ta zagayo bayan hostel d'in nasu akusada daji inda su kan yi fitsari ko bayan gida da dare. tsugunnawa tayi ahankali ta fara, sai dai zata rantse ba k'arar fitsarinta bane kawai agurin ahanzarce ta mik'e cikeda tsoro tana mamakin yadda akaima ta tashi fitsari,abinda ba sabonta bane ko a gida.

ya..si meen, yasimeen..! Tashi ki rakani fitsari

muryar ta gilma mata da ta dinga ji sadda tana bacci, ahankali ta bude ido sai dai wayam! Bataga kowaba, k'okarin rufe idon take dan ta koma baccin da dakyar ya dauketa daman, ga mamakinta fitsarin take ji da gaske ya taso mata da bama zata iya rikeshi zuwa asuba ba.
Dam! Gabanta ya fad'i sai yanzu ta tabbatar da tadata din akai kuma bataga kowaba, amma da yake hankalinta ya gushe ta dalilin fitsarin da taji baisa ta ankara da hakan ba har sai yanxu data fito harma tagama fitsarin.

Sauri sauri ta dingayi ta isa ga dakin nasu amma gani take yayi mata nisa.
Da hanzari ta bude kofar dakin tayi saurin rufewa, sai dai kafin ta isa 2nd square taji qarar bude dakin alamun anshigo ankuma bankata da qarfi an rufe!
Gigitacciyar qara tasaki ta fadi a sume agurin.

** ** **

Yauma kamar kullun sheshshekar kukan ya dinga jiyowa acin k'aton ramin ana ambaton sunan shi,
Ahankali yake takowa da igiyarshi dayake son zurawa dan fiddo yarinyar acikin ramin, saida ya iso gab da ramin yafara warware igiyar zai zura...

"Katashi mana haba Farouq sai kace wanda yai kwana goma baiyi bacci ba dillah ka tashi Daddy na jiranka palour"

Wanda aka kira da Farouq kau ƙara jan blanket din tareda juyawa ya yi.
takaici ya ishi fahad juyawa yayi ya bude bedside fridge ya dakko ruwa ya dawo ya kwarara mishi.
"Wayyo! wayyo Allah na mummy na mutu farouq daya miqe afirgice babu shiri ya dinga zunduma ihu"

" kai dallah malam yimana shiru ka ida miqewa" kawai fahad ya fada yafice yana qa farouq dariyar mugunta dan yasan ko kadan baya qaunar ruwan sanyi koda sha zaishi saiya ajje ruwa ya huce san nan yasha.

Farouq ida durowa yayi daga kan makeken gadon nashi yana gungunai, jiyake kamar ya shak'e fahad daya tada shi daga mafarkinshi daya fara sabawa dashi.

ya nufi toilet kusan mintuna talatin ya fito daure da towel dawani guntu towel din yana tsane jikinshi.
Agurguje ya shafa mai ya feshe jikinshi da turaruka masu qamshi san nan ya dakko farar riga armless da wando three quarter blue yasaka san nan ya fito daga dakin.

Daddy ya iske da mummy sai fahad zaune a dining table
"Daddy sannu da gida"

Yawwa son kafito"

"Eh" ya fada tareda jan kujera daya ya zauna ya na kallon mummy ta kasan ido dake banka mishi harara. Daddy ne ya taso dakanshi ya zubawa farouq abinci itako mummy takaicine ya isheta ganin irin sangarta farouq da ya ke ƙarayi koda yaushe aqalla yanzu faruk shekarunshi 29 amma kodan shadaya bayayin sangartar da yakeyi.
Shiko fahad ya dage breakfast dinshi kawai yakeyi dan girkin mummy ba daga baya ba shiyasa ma koda ya fito baici komaiba don yasan zaici girkinta.

Fahad ne ya miqe bayan ya kammala cin abincin.

" mummy na tafi gurin aiki"

"Allah ya tsare sai ka dawo"

"Daga cen gida zanwuce ai"

"To ka gaida gida ina gaida Mami"
" To inshaAlla zataji"

Farouq ne ya taso dan rakashi waje bayan yawa daddy sallama, suna isowa k'ofar dakin yace agaida gida dan har yanxu haushin fahad din yakeji" girgiza kai yayi kawai ya wuce yasan inya biye ta parouq sai ya makara.
**

"Kai yanzu ba za kaima kanka fada ba kafara zuwa aiki hakanan?To ba zan lamunce wan nan iskancin naka ba wlhy "

mummy ke mashi fada bayan fitar daddy, dan shine ke sangartashi kasan cewarshi shi kadai namiji da yake dashi baya k'aunar abunda zae bata ran Farouq ko ya yake.

"Kiyi hak'uri mana mummy zanfara zuwane ai.."

Hararar da take faman antaya mishi kamar idonta zai fado ya sa shi yin shiru yai sama abunshi yana 'yan k'unkunai, shi baya son ayi mashi maganar zuwa aiki koya yake.

ZATO...! Kde žijí příběhy. Začni objevovat