page 23

448 78 3
                                    

🐾🐾 *ZATO...!*🐾🐾

  ©℘ıŋƙყ
Wattpad:-pinkylady222

Page 2⃣3⃣

Ta na fitowa sai taƙi tafiya ta samu bango ta laɓe ta na jiran su fito ta ƙara kallon shi. Hango sun tayi sun fito kuwa, bakin shi na motsi alamun magana yake.

" sholy lafiya?"

Aysar da fitowar ta kenan ta hango sholyn maƙale da bango ta faɗa ta na dafa ta.
a zabure ta jiyo,sai ta saki ajiyar zuciya ganin aysar ce.
 
Hannun ta ta jawo suka koma ba tare da ta lura da su farouq da ke tafe ba.

Gaba ɗayan su suka ɗinguma zuwa asibitin da aka kwantar dashi dan daman zuwan su ne yasa suka tafo gida  harsu nuriyya ɗin dan tarbar su.

Gurin shiga mota ma sholy tai saurin shigewa motar da mousa ya shiga ta daidai ci saitin madubi ta zauna.

***

Ta na zaune umma na kwance mata kai a tsakar gida yusrah kuma na da ga gefe ta na gyaran wake.

Sallamar amirah ta katse ƴar guntuwar firar da suke yi.

"Oyoyo oyoyo"

Yasmeen ta faɗa sa'ilin da ta ke ƙulle kanta da ta zame da ga gurin umma. Umman kuma ta na ansa sallamar.

Da murmushin ta ta ƙaraso har inda suke tayiwa kanta  gurin zama ta re da gaida umman. Sannan ta zunguro yasmeen ta na nuna mata ƙofar gida.

"Me?" Ta tambaya ta ta na miƙe wa, san nan ta ce "shigo"

Tashi ta yi tabi bayan ta zuwa ɗakin, sai da ta shiga tace

"Angon naki ya na jiranki a waje fa"

Duka ta kawo mata ta kayce ta na daria kafin ta ce

"To ƙarya na yi? Har kin fara kyallin amare Allah.."

Guduwa ta ƙarayi ta na cigaba da daria ganin ta na shirin kai mata duka.

"Allah shirye ki amirah"

"Ameen Aunty, ai yanzu sai aunty ko jikin mu yayi tsami"

Ganin in ta biye ma amiran  za ta tsayar dashi yasa kawai ta ɗakko hijab ɗinta ta saka ta bita da harara san nan ta fita.

  Ya na hango ta ya fito daga mota ya na mata maraba da murmushin da ke fallasa farin cikin da ya ke ciki.

Ita ma da murmushin ta isa  in da yake bakin ta ɗauke da sallama.

"Ranki ya daɗe farin cikin rayuwa ta"

Sadda kanta ta yi cike da kunya ta ce

"Ina wuni"

"Lafiya lau,na same ki lafiya?"

"Lafiya lau" ta ansa.

"Gashi kuma na zo a lokacin da ake jira na" ya faɗa ya na kafe ta da ido.

Sai da ta ɗago kai san nan tace

"Yanzu yanzun nan?"

"Eh wallahi a kwai aikin da zanma baba ne yanzu, ina gamawa zan tafo ayi man haƙuri"

Ta na wasa da yatsun hannuwan ta tace

"Kai babu komai Allah,sai ka dawo. A gaida su mama"

"Zasu ji"

Sai da ta shiga gida san nan ya shiga mota ya tafi.

Tunda ta shiga gidan ta ke jiyo dariyar amirah da yusrah. Ta ɗaga labulen ta na faɗin.

"Da alama duniya ta maku daɗi, me a ka samu ne haka?

Da zakwaɗi yusra ta ce

"Tsare-tsaren yadda biki zai kasan ce muke, gaskiya sai kin yaba ma tsarin mu in kika ji. Shigo dai"

ZATO...! Donde viven las historias. Descúbrelo ahora