Dining

430 32 0
                                    

GYARA: masu karatu idan Baku mantaba rubutun da nayi abaya Yaya Abubakar yana kara2 A ABU GYARAN SHINE MAHAIFINSHI KANO YAKOMA DA ZAMA INDA YAKE KASUWANCI KUMA KASUWANCIN NASHI YA BAUKASA Hakan yasa zama Babban Dan kasuwa. Dafatan zaku min Afuwa. Muje zuwa.

Cigaba.
Kowa ya hallara a dining din shi kadai ake jira, don haka yana zuwa, kujera yaja ya zauna Wanda ke facing din suhailat, Wanda tun zuwanshi wurin ta kasa sakin jikinta. "Wow Ammina wannan kamshin girkinfa " Yaya yafada lokacin da Ammi ta bude food flask din tana serving din daddy.
Zahra tayi murmushi tana cewa "Anty suhailat da Ammi ne suka shiryamanashi" (sakwara ce da miyar ugu da agushi, sai farfesun  bindi da kafar sa) yaya ya kalleni yace wacece suhailat kuma? Nace "gata" ina nunata , yatsaya kamar mai son tuna Abu nace "yar gidan inna husaina kanwar Ammi" yace "OK lallai girman mace ba wuya,ina su yazid kuwa? "  Anty suhailat tace suna gida" Ammice tace "Bismillah" don lokacin tagama serving dinmu.
   Kowa abincin shi yakeci including khairat da nadia. Wanda tunda Yaya yadawo suka nutsu.  bakajin karan komai sai plate da cokula , yayin da Yaya idanunshi nakan suhailat, ita kuma takasa cin abincin sai wasa takeyi da cokalin acikin abincin. Ammice ta dago kanta takalli suhailat Wanda Loma biyu kacal tayi tun fara cin abincin. Sai taga kallon kallo da akeyi, murmushi tayi ta cigaba da cin abincin ta.
Ta kasan table Ammi ta tabo kafar daddy tadago suka hada ido dayake suna facing din juna, tayi mishi signal da ido shima yagansu yayi murmushi ya kada kai ya cigaba da cin abincin shi shima. Muna gamawa muka tafi falo da Yaya dasu mummy muna ta firan yaushe gamo, yayin da suhailat ta tattare dining din takai kayan da akabata kitchen domin wankesu.

******      *****             *******

Abdul rahim ne kwance a rigingine  bisa sofa din dakinshi idanunshi suna kallon ceiling.
Daka kalleshi zakasan ya tsunduma cikin tunani. Tun haduwarshi da Zahra yakasance  baida tunani sainata baida mafarki idan ya kwanta sainata haka yake kasancewa dashi ayanzu. Mata dayawa sunsha nuna suna sonshi , wasuma zuwa suke susameshi suce suna sonshi amma kokadan basa gabanshi, Baya musu kallon masu dankwali kallon masu rawani yake musu. Zahra ce kadai yake gani amatsayin mace saidai yana mata kallon wacce bata koshi da tarbiyyaba. Wata zuciyar tace masa "kamallaketa sai ka gyara mata zama" wata tace mishi "kai aa Hali zanen dutse, ice tun yana danye ake tankwarashi Amma wannan tafi icce tauri da bushewa" tunawa yayi da yanayin yanda bakinta ke motsawa lokacin da take mishi magana cike da gatsali da rashin kunya,ga muryarta mai dadi da take masa gizo a kunne. wata Ajiyar zuciya yayi yana magana under his breath "ohhh... Her mouth will be as sweet as strawberry"gyara kwanciya yayi yana cigaba da tunaninta zuciyarshi takudurta mishi Abdulrahim zaka iya Kaine Wanda kowacce mace take burin ta mallaka don haka mallakar stubborn girl ba abune mai wahala ba. Juyi yasakeyi yana rungumar filo nan da nan cikin abinda baifi  30seconds ba bacci yayi gabadashi cike da mafarkin stubborn girl dinshi (sunan da ya saka ma zahrah kenan).
        Kodaya farka laasar tayi don haka yatashi yadaura alwala domin yin sallah. Kodaya idar wayarshi yadauko domin yin waya da Abokinshi Wanda tunjiya dasukayi waya akan yau zaidawo. Nade daddumar yayi yakoma kan cushion yazauna yana kokarin lalubo numbern, kira yayi bugu biyu aka dauka adayan bangaren.
     ****      ****  ***      ****
Firansu sukeyi cike da nishadi inda Zahra take tambayarta yayan nata " Yaya wai yaushe zaka samamin antyne" dago kan da zaiyi sukayi ido hudu da suhailat  data fito daga kitchen inda yakasa dauke idanunshi akanta" ringing din wayanshi ne yadawo da hankalin shi jikinshi, wayar yadauka yana kokarin tafiya dakinshi while still idanunshi nakan suhailat.  ammi da daddyne suka kalli juna cikin farinciki suna fatan Adduansu tazama gaske. Saurin dauke idonta tayi daga gareshi tana mamakin yanda Yaya Abubakar yake yawan tsareta da idanuwanshi masu fitar daita nutsuwarta.

Waya yake cike da nishadi yana fadin " su Ammi suna lafia yasu mami da Amir?"
  Dagacan bangaren ya Amsa da
      "Lafiansu kalaw yaushe zamu hadune yace gobe inshaAllah naga yanzu garin da hadari sai cida akeyi". Abubakar yace hakane gobe zanzo da sisters Dina mugaisa dasu mamin, Abba yana gari kuwa?"  "Aa yana Cairo meeting zasuyi da the General din soldiers nakasar". OK Allah ya temaka" Abubakar yafada yana cewa anyway saimun hadu goben. Nan suka yi sallama suna daukin ganin juna da zasuyi a goben
Kuyi hakuri da wannan
Kuci gaba da kankaro ma wannan littafin mutunci ta hanyar dangwala yar tauraruwanan.

Nafi karfin aurenshi (girman kansa yayi yawa)Where stories live. Discover now