page 5

3.7K 299 13
                                    

🧊 *RAYUWAR BINTU*

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

*Page 5*

Hakanan tanajin muryar Khadija nayawo cikin kwanyarta

"Yaya Bintu mun rasa Hajje,Hajje ta rasu,tatafi tabarmu munzama marayu,we've no one!".

Karasawa jikin gadon da Hajjen take tayi a firgice sannan tashiga jijiiga ta tana fadin "Hajje kitashi,kitashi don Allah ninasan bazaki mutu kibarmu ba,keda bakin ki kinyimin wannan alkawari please kitashi" abunda tadinga fadi kenan tana kuka mai tsuma rai harsaida karfinta yakare zamewa tayi agurin tazauna akasa tana sheshekar kuka awannan lokacin kam har muryarta yafara dashewa amma dukda haka bata bar maganar ba "kitashi Hajje,Please kitashi"
Nurses ne suka shigo sannan suka dauki gawan akaje akayi mata sutura,atake kuma akayi providing ambulance sannan aka dauke su aka kaisu gida. kan kaceme rasuwar Hajje yabaza unguwarsu nan danan gidan yacika makil da jama'a sabida hali nagari da kowa yasan Hajjen dashi hakanan mutuwartata bakaramin jijjiga mutanen unguwar yayiba. Sanda suka iso gida a tsakar gida aka ajiye gawan nata kafin lokacin jana'iza yayi se akaita gidan ta na gaskiya,daman su Mamman Noor baswanan don yaje dauko su Amir daga makaranta,sanda suka dawo suka riske labarin mutuwar kakartasu bakaramin jijjiga Mamman Noor yayi ba though he couldn't cry because he's in a situation whereby hawayen ma sun kasa zubowa,Hajjen da jiya suke tare infact yau yabarsu  a asibiti fa ashedai ganin karshe yayi mata batareda yasaniba,ashedai itadin tafiya zatayi tabarsu. Ilham karasawa tayi wurin da Hajjen ke kwance tana kokarin yakice lukkafanin tana fadin "meyasa zaku rufe fuskar Hajjena bakusan ana zafi bane ba?".......
Dakyar akazo aka janyeta ana fadin Ilham Hajje Allah yayimata rasuwa addu'a zakiyi mata kinji,kuka tasaki tana ihu ni Hajjena bata mutuba tace sena girma zata dainayimin tatsuniya da dare kuma kunga haryanzu ni yarinyace so bazata mutu tabarmu ba,haka tadinga rigima tana kuka duk wanda ke wajen seda ya zubda ma yaran kwalla barinma wanda sukasan halin ubansu. Haka aka sallaci Hajje aka kaita gidanta na gaskiya kuma ba laifi alhamdulillah  tasamu mutane. Yusrah awurin classmates dinsu taji labarin rasuwar Hajje ranar zama tayi speechless tana mamaki kafin tadubi Aunty tace "Aunty dazunnan fa muka rabu da Bintun tazo nan gida kan zataje tasayama Hajjen magani takai mata asibiti"
Aunty tace "lkon Allahn kenan muna namu Allah yana nashi Allah ubangiji yajikan ta da rahama" "Amin" cewan Yusra din tana hawaye nan Auntyn tace tashirya suje suyi masu ta'aziya tunda dare baiyiba aikuwa haka sukaje gidan. Suna shiga ta rungume Bintu  suna kukan rashin tare alokacin har idanun Bintu sungama kumbura amma hakan baisa tadaina kukan ba se ma abunda yakaru,da dare su Yusra suka tafi tareda alkawarin gobe ma zata dawo,godiya Bintu tayi masu harda Auntyn kafin suka wuce gida. Ranar babu girkin dasukayi tun na safe da Khadija tayi takai musu abinci a hospital,to ma inama suketa girki koma sun waiwayi girkin to me zasu dafa tunda last taliyan daya rage shi Khadijan tadafa yauda safe batun mahaifinsu kuma basumasan yana inaba tunda Mamman ya tabbatar musu baiyi attending funeral din kakarta su ba. Har goman dare Mata nata shigowa suyi musu ta'aziya sutafi adede wannan lokacin ne Mahaifin nasu yadawo duk abuge se tangal tangal yakeyi kamar zai fadi Bintu tsabar kunya da takaici batasan sanda tatashi tayi daki ba tanaji yanata haukansa amma babu wanda yakulashi bata ankara ba tajishi akofar dakin nasu cikin maye yace "Don ubanki Ina maki magana shine zaki shigo daki kibarni awaje?".......
Cikin kuka tace "kayi hakuri Abba" yar tsaki yayi sannan yace "Ina abinci na?'
Cewa tayi "Babu" aikuwa yahau balbali on top of his voice "babu abinci zakicemin don baki da hankali,wato ni ba mutum bako zanyini awaje sannan indawo gida acemin babu abinci kanku kadai kuka sani,to wallahi baku isaba" daganan yajuya yafita yawuce kitchen jisukayi yanata musu wurgi da kwanuka shi adole yanata dube dube kozai samu abinci sede babu, Bintu kuka kaman ranta zaifita haka Khadija ma gashi Mamman baya cikin gida ganin bayida niyar bari gashi Matan dasukazo musu ta'aziya daga cikin unguwa se kallonshi suke suna kus kus yasa ta karasa gareshi ta rikoshi tana "Abba mushiga ciki ka kwanta don Allah dare yayi" yakice ta yayi yature gefe tafadi sannan yayi hanyar fita daga gidan Allah yataimaketa ba duwatsu agurin so bataji ciwo ba, Khadija ne tazo tadagata tanayi mata sannu haka Matan ma kafin sukayi musu sallama suka tafi..........
Da Mamman yadawo zairufe kofa Bintu tace "Mamman Abba baidawo bafa".....
Rai bace Mamman yace "nina rike kafarsa ne koni nace yatsaya awaje har iwarhaka?" calmly Bintu tace "nacedai kada karufe kofan ko?" rai bace Mamman ya dangwarar da katakon agurin daman dashi suke rufe kofar sesu tura dutsi menauyi ya tare tunda basuda ainahin kofa ajikin mashigar gidan. Har wuraren shabiyu mahaifin nasu baidawo ba hakan bakaramin tada hankalin Bintu yayiba don tasan duk abunda zaiyi to gida yake zuwa yakwana baitaba kwana awaje ba,da Khadija taga tanata safa da marwa tace "Yaya Bintu kizo ki kwanta kidaina damuwa da bawan Allahn dabai damu da Al amuran muba" hararanta Bintu tayi sannan tace "kiyi kwanciyarki Khadija cemiki nayi shi nake jira?".........
Tabe baki Khadija tayi sannan takwanta ta lulluba bawai don tanajin baccin ba a'a kawai dai takwanta dinne sabida tarasa abunyi sannan tunanin rashin dasukayi ma kadai bazai barta tayi baccin ba. Har akayi sadakan uku basu girka komaiba a gidan tunda kosun ce zasuyi kirgin ma basuda abun girkawan donma ana kawo musu sadakan abinci daga cikin unguwa haka Yusra ma kullum inzata zo seta taho musu da abinci daga gidansu. Ayaune ma da Aunty takuma zuwa tadauki 5k tabasu wai na sadakan ukun godiya Bintu tayi tareda yi mata Allah yasaka da alkhairi,ajiye kudin tayi safely tunda already wasu sun kawo irinsu biscuits dadai sauransu shi suka harhada suka kulla aleda suka baiwa jama'a inda sukace sunhada sadakan uku da bakwai da yanma da Yusra zata tafi Bintu tadauko 5k dinnan tamika mata tareda cewa ga kudin ki Kawata nagode sosai Allah yasaka da alkhairi,hararanta Yusra tayi sannan tace "Banaso kirike ahannunki".....
Fuskar tausayi Bintu tayi sannan tace "don Allah kikarba mana" Kai tsaye Yusra tace "Allah kibarshi kawai" sororo Bintu tatsaya tana kallon Yusran da mamaki gyada mata kai Yusran tayi sannan tace "Ranar bayan tafiyarki sega shi anzo nemana wai zanyiwa wata amarya lalle wallahi dana gama masu itada wasu few kawayenta 25k suka bani Bintu inadawowa gida namaidama Aunty kudinta gurbinsu bayan nanne nasamu labarin rasuwar Hajje shine muka taho gidannan kusan maghrib" Bintu cewa tayi "koma minene dai ai bashi nakarba ba kyauta nace kibani ba" dariya Yusra tayi sannan tace "tonikuma nayi niyan bada kyautan se akyaleni" daganan Yusra tayi gaba abunta binta Bintu tayi tana murmushi kafin yace "to tsaya inraka ki mana" Banaso kikoma gida dariya Bintu tayi sannan tayi sauri takamo ta tareda riko hannunta tace "thank you so much Kawata".......
Yusra tace "Babu godiya a tsakanin mu Bintu".....

RAYUWAR BINTUWhere stories live. Discover now