Koƙarin kawar da idanuwan ta ke yi daga kallon nasa,sai dai aka yi rashin sa ya kamata tana kare masa kallo.
Murmushi ya sakar mata har hakoran sa suna bayyana,farare tas da su,tare da dan wushiryar sa wanda ya ke dada fito da kyawun sa
Ji tayi ina ma kasa ta bude mata,ko ta samu inda zata shige saboda kunya,da kyar ta daure kafin bakin ta iya furta kalmar
"Ina kwana"
Idanun sa nakan ta ya amsa ta
"Lafiya kalau Mimi ,da fatan kin tashi lafiya"
Kan ta a duke a kunyace ta ce
"Lafiya lau"
Dady ne yayi hanyar dining table domin yin breakfast,yana sauri kar ya ya makara sabida yana da bakin da zai gani a kasuwaMomy ce ta juya inda Nabil ke zaune ta ce su karasa gaba daya,sai shima yayi breakfast din,kamar ko ta san bai karya ba ya fito,sai ya tashi kawai tare da samu waje ya zauna
Mimi ce ta shiga serving din su,zuba mata idanu yayi yana kallon ta a kaikaice bakaramin kyau tamasa ba kaman ya sace ta ya tafi ya ita ya xamana shi kadai xai rinka kallon ta,gashi komai nata na natse,haka nan taji a jikin ta kamar ana kallon ta
Sai ta zama so uncomfortable a wajen amma haka ta daure ta shiga sakama kowa na sa abincin har dashi batare da ta yarda ta sake kallon barayin da yake ba,bayan ta gama itama ta janata abincin ta bayan ta zauna
a kujerar na fuskantar in da Nabil din ke zaune,hakan ko ba karamin daɗi ya masa ba ya samu abinda ya ke soGanin hankalin Momy baya kan su,Dady kuma an kira sa a wayar sa,ya sa shi kara bada ƙaimi wajen kallon ta son ran sa,har sai da ta kasa daurewa ta ɗago kan ta don tabbatar da shi din ne ke ƙure ta da kallo haka ko ko jikin ta ne ke mata karya,sai ta ko samu damar hada idanu da shi,ta dauka da suka haɗa idanu zai daina kallon nata ne sai ta ga bai dauke idanun sa ba,har da sakar mata murmushi tare da ɗaga mata gira,lallai ma wato ya ma san abinda yake yi,da gangan ya kure ta da kallon don ya ga ko hakan zai dame ta ya gashi kuwa yi nasara
Duk sai ta bi ta takure da yanayin kallon da ya ke aika mata da shi,har abincin ta ta kasa cin ko rabi, taji ta koshi,a ran ta tana tambayar kan ta toh kallon ta yake yi na me nene?
Momy ce ta ga kwata kwata ba ma cin abincin take yi ba, ya sa ta cewa"Mimi na ga kamar ba kya cin abincin,gwara ki yi maza ki gama tunda tare zaku fita da Alhaji"
Ɗago wa tayi ta kalli Momyn da ke zaune a ta dan yamutsa kafin ta ce
"Na koshi ne"
Momyn tace
"Kin koshi kuma?Amma naga ko taɓa abincin baki yi ba,haka zaki fita baki ci komai ba"Momy ke ƙara tambayar ta
A hankali ta ce
"Ban da appetite ne Momy,kuma na sha tea "ta karasa fada a shagwaɓe
"Shikenan tunda kin koshi,sai ki tashi ki kai plate din kichin ki rufe Iya ta fitar ta ba almajirai"
Jin haka yasa ta tashi dama abinda take so kenan ta bar wajen don ba zata cigaba jurar irin kallon da yake bin ta da shi ba,domin ita kaɗai ta san yadda take jin kallon a jikin ta,bata re da tace ta shiga hada plate da cup din da tayi using ta bar wajen,har kuma ta isa kichin din tana jin ƙaifin idanun sa a k
jikin ta
