Shafi Na Daya

1.1K 67 4
                                    


Kwance take akan makeken gadonta,kamar kowane lokaci wayace a hannunta Tana murmushi, domin yau tanaji firar datakeyi dashi tafi ta kullum dadi. Dan a wannan lokacin ne yayi mata albishir din cewa xasu hadu,bayan tsawon lokacin dasuka dauka suna soyayya.

"Ra'eesah!!! Ra'eesah." mummy ce tasake kwala mata kira a karo na uku bayan ta nufi kofar dakin diyar tata, domin taga menene ya dauke mata hankali taketa kiranta bata amsaba. Wayace a hannunta tanata murmushi yayin da mummy ta fisge wayar daga hannunta tace "Ra'eesah, meye yake damunki dahar naketa kiranki tun ina kasa bakijiba."

"Ohh! Sorry mummy wllh ina dan duba wani abune."

"Kina duba wani abu? kokuma kina abinda kika saba. To ni dai ba abinda kikeyi na tambayeki ba ki sauko kije gidan Hajiya Turai kikai mata wannan sakon."

"Ok." Ra'eesah tafada da saurinta domin kuwa dama hanyar fita take nema domin haduwa da kawarta ta bata labarin sabon friend dinta na Twitter.

Cikin sauri ta sauko da shirinta domin ta kagu taje gidan. Driver ne xaune a motor yana jiranta. Cikin nutsuwa Ra'eesah ta fito kamar yadda ta saba "Ina wuni baba." Ta gaishe da dattijon driver.

Cikin fara'a ya amsa "Lafiya lau Yar albarka, kinfito."

Ra'eesah tace "Na fito baba. Ya aikin?"

"Lafiya lau." yace da ita.

Driver ne ya bude mata bayan motar tashiga. Baba maigadi yana daga mata hannu "A dawo lafiya uwar dakina." Murmushi tayi Wanda ya bayyana fararen hakwaranta ya kuma kara bayyanar da kyawunta. Domin Ra'eesah kyakykyawace ta ajin farko acikin kyawawa. Ga uwa uba nutsuwa da girmama nagaba da ita. Shiyasa ma'aikatan gidansu suke jin dadin zama da ita sosai.

Author's Note

Dafatan kunji dadin labarin.
Kar Ku manta Ku fada min ra'ayoyinku game da wannan shafi.

Don't forget to like and comment

RABEELAH
YANDOMA

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Apr 18, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Soyayyar MakahoWhere stories live. Discover now